Page 9

2K 173 15
                                    

*KO BAZAN AURESHI BA...*
        _(hattara Yan mata)_

            *XINNEE SMART*
_whatpadd @xinnee_smart1_

*This is for my friends and family,🤝🏻😍 I really appreciate all Ur warm wishes and the love u showed me. I truly feel blessed to have such amazing people in my life. Iove u guy's* ❤😍💋💋😍❤

   _For those that don't see my update especially my watpadians I'm sorry I'm soo busy that's why, but now I'm less busy, thank you for your concern_ 🤝🏻😍🤝🏻

*Page 9.....*

'kwa'kwalwarta ce tashiga caji, na neman mafita, dan dole tasan abunyi kafun,  Yaya"Ali yayimata haure da shisshigi, a cewar ta,

        zagayar d'akin tafara, kafun tasoma zance ita d'aya, Amishty, dan dole kinemawa kanki mafita, to mai zanyi?... mai... zanyi.. dole dai ina bu'katar waya.. to a ina zansamu,? tayiwa kanta tambayar, no way....

         Shiru tayi yayinda ta koma ta kwanta kan katifar ta,

Numfashi take saukewa kamar wacce tayi tsere, kanta tashiga ya mutsawa, kafun ta soma sakin wani irin murmushin Mugunta, a lokaci d'aya kuma tasauke ajiyar zuciya,....

        

      

             *********
Hammad, a ranar haka ya kwana yana tunanin ta, da gaske sonta yake, amma zai jira zuwa lokacin dawowar haidar dan sossai yakeson sanin wani abu a game da ita kafun yaganta, dan haka dole yajira dawowar matar haidar.....

        Wayarsa dake gefensa ne tayi ringing alamun ana kiransa, duban wayar yayi ganin wacce ke Kira ne, yasa yasaki d'an gajeren tsaki kafun yad'auka....

     Hello"yafada a kasalance,

a 'bangaren surayyah kam dad'i ne yakamata ko bakomai taji muryarsa mai Sakata kasala, tunowa da tayi da abunda yasaka ta kiransa yasa, tayi saurin janye smile d'in fuskarta,......

A sanyaye tace, anwuni lfy?

Lfy"ya'

amsa a ta'kaice, shiru tayi cikin rashin jin dad'in yadda ya'amsa mata, saidai hakan baisa tafasa maganar da tayi niyya ba, dan haka a hankali cikin muryarta dake nuna sanyinta tace,...

   Yaya"hammad, dama naji kace zakazo kuma bakazo ba, gashi inason zamuyi magana shiyasa nakira ka,

          d'an dakatawa tayi taji mai zaice, shiru yayi batare da yace komai ba, a tunanin surrayah ko bayajin tane dan haka tasoma fad'in.. Hello... Hello... Hello.... kanajina kuwa?

d'an numfashi yaja a dame... Kinga surayya, ina wani abun ne a yanzun so we will talk later ok?
    Batare da yajira mai zatace ba yakashe wayarsa,

Shiru yayi ya nasake jin 'kaguwa da son ganinta, sossai yamatsu haidar yadawo...... Wayarsa dake ringing ne tadawo dashi daga duniyar tunanin daya Lula,

   Hello"little bro, ykk, to to shikenan zanturo maka ayi karatu lafiya, fuskarsa cike da annashuwa ya sauke wayar hakan nada nasaba da wayar da yayi da d'an uwansa, dan sossai sukeji da junansu,...

****,,,

Tunda yakatse wayar take ri'keda ita a hannunta, cike da damuwa ta rafka uban tagumi, Allah yasani tana Matu'kar kaunar hammad.... So wanda bazai misaltu ba, tun kafun yafara sonta take faman wahalar dakon 'kaunarsa sai gashi a daidai lokacin da tafara murnar yafara sonta da nuna kulawarsa a gareta sai gashi abu na neman lalace mata,yazama dole tasan abun yi, tana cikin tunanin,

            KO BAZAN AURESHI BA......... Where stories live. Discover now