Page 39

1.4K 122 14
                                    

  KO BAZAN AURESHI BA...
   (hattara yan mata)

Wattpad @xinnee_smart1

Page 39

Ayman"sulalewa yayi 'kasa yayinda  'kwa'kwalwarsa tashiga caji, maganganun surayya ke sake dawo masa, yayinda yake ci gaba da tuno yanayin Aysha, take kansa yasoma azababben ciwo babu shiri yashige room d'insa,

           Binshi surayya"tayi da goran ruwa da cup, a gefen gado tasameshi yazauna yana dafe da kansa da alama ciwo yake masa.

   zama tayi itama a gefensa bud'e ruwan tayi ta tsiyaya masa, mi'ka masa tayi,, babu musu yakar'ba, yasoma kwankwad'a saida ya shanye tas! kafun yasauke cup"d'in.

          bari in had'a maka ruwa kayi wanka ko?  girgiza mata Kai yayi cike da damuwa alamun a a baya bu'kata,, kafun yace mata.... yanzun dai kije ina bukatar hutu,, amsawa tayi da to,, mi'kewa tayi tanufi fita saida tarike handle d'in 'kofar tace babu abunda kake bukata inkawo maka?

   bai amsa mata ba saima kwanciya da yayi,, ya runtse idonsa.

ganin hakan yasa ta fita a sanyaye, yayinda'kar'kashin zuciyarta farinciki ne dan tasan ko Aysha ce autar mata yabarta har abada saboda son dayake wa d'an uwansa ba 'karami bane. a ranta ta raya... Idan rabuwarsu ta kasance ai sai nafi Kowwa farinciki,, dan tun asali na tsani yarinyar,, kyanta yayi yawa... ta'karasa fad'a a ranta had'i da fiddo sirrin tsaki,, daidai lokacin da take shiga d'akinta,,

*************
Aysha"rasa mai zatayi tayi tsakanin farinciki da ba'kinciki,, saidai daurewa tayi tasaki murnar yake... 'kawata"wace duniyar kika shige har haka? Ina cike da kewarki fa,, hhhhh tom shikenan zan turo. Miki da address d'in gobe sai kizo,, dan akwai abubuwan danake so mu tattauna,, yawwah sai goben kenan,,

Sauke wayar tayi tana ajiyar zuciya a fili tace,, nagode Allah ga Nierjer"tadawo ko bakomai zansamu 'kawar Shawara, tunda Action munyi nisa,, tagumi ta zabga, tana ci gaba da tunaninkanta,,

A ranar yadda taga rana haka taga dare ko runtse bata runtsa ba,, saboda tsananin fargabar da take ciki.

Wann kenan...

*******
Ayman tunda ya kwanta yashiga tariyo komai sanka sanka tunda ga lokacin da yazo yasamu Hammad"a asibiti zuwa labarin da yabashi na yaudararsa da yarinyar tayi,, har zuwa yau da kalaman surayya,,

      Toh"abu d'aya ne yake d'aure masa kai shin dama idan Macce tana bin maza za"a iya samunta virgin? kansa ne ya 'kulle,, a cikin daren yakira wani abokinsa wanda yake kasar Germany Felix wanda yakasance likitan mata ne,, yayi sa'a kuwa yad'aga,, tambayar sa yashiga yi,, ta yadda ake gane Macce virgin,

       Nan yashiga kora masa bayani,,
Godiya sosai yayi masa bayan yagama yimasa bayanin.
     Sake zurfafa yayi cikin tunaninsa kenan kenan Aysha a cikakkiyar budurwa ya aureta, to meye gaskiyar lamarin dake tsakaninta da d'an uwansa Hammad,,? Lallai yana bukatar sani kafun lwakwalwarsa ta tarwatse.

Kansa sai azababben ciwo yakeyi,, haka ya kwana a Raye.... Babu ko burbushin bacci a idonsa ga kewar lallausan jikin Aysha dake ratsa kowacce gaba a jikinsa,,

                 ***********
Kiran farkon da ake ne yasa ta mike bathroom tashiga ta d'auro alwala,, raka'atanil Fajr tayi,, kafun tami'ke dan gabatar da sallar asuba,, dan anrigada ankira,, tana sallamewa tashiga yin azkar d'inta da zikiroronta,, tana gamawa tad'auko alqur"ani,, tasoma karatun ta kamar Koda yaushe,, tana gamawa tamaida shi ma'ajiyarsa,, mi'kewa tayi ta zare hijab d'in jikinta ta nunke juyawa tayi dan ajiyewa........ Kawai taga mutum kishin gid'e a kan bed d'inta.

     Wani irin fad'uwa gabanta yayi,, take ta ja da baya tamkar taga mugun abu,, Shikuwa dubanta yayi da idanuwansa da suka kad'a sukayi jaa.
Zo nan Aisha!

       ya fad'a da muryarsa data sake jefa ta cikin fargaba da tsoronsa,

Ba cewa nayi kizo ba? Yasake maimaita mata, a darare ta'karasa inda yake dur'kushewa tayi a 'kasa kanta Shima yana kasa.    Aisha..... yakira ta batare da yajira amsawarta ba yace...... Meye gaskiyar tsananinki da Yaya na? Ina nufin Hammad.

Shiru tayi,, sai hawaye dake sintiri akan fuskarta,, da yaga alamun bazata amsa ba yasake jifarta da tambayar datakusa tarwatsa ta,, Aisha... da gske kece kikayi sanadin Yaya na ya rasa ransa sakamakon ganinki da yayi a hotel da wani??

        Wani irin d'agowa tayi, tadubi Ayman yayinda wasu irin hawaye masu zafin Sauka da radadi sukayi mata layi a fuska,, bakinta kuwa sai rawa yakeyi,, tama kasa sanin mai zatace,

Ci gaba yayi da cewa.... Ina jinki,, kibani amsata,

    Still shiru taimasa, Shikuwa hakan tunzurashi yake, dan shikam Lallai yanson sanin takamaimai abunda yafaru tsakaninta da Hammad,, saidai ya fahimci bazaiji hakan ta ruwan sanyi ba,, dan haka yace mata, da alama baki shirya fad'amun gaskiya ba, wannan kuma alama ce ta baki shirya zama dani ba,, dan haka kije gida saina nemeki ko ince duk ranar da kikace shirya fad'amun gskiya to zaki iya dawowa gidanki,,

             Yana zuwa nan a zancensa,, ya tshi yafita daga d'akin,,

Bin bayansa da kallo Aisha tayi,, lokaci d'aya kuma wani irin mahaukacin kukanta yazo mata,, aikuwa tabashi sarari,, yitake tana zantuka,,

    Tamkar wata zararriya,, nemawa kanta mafita tayi ta hanyar mi'kewa tashiga had'a Yar jakar kayanta,, tana gamawa tad'au hijab d'inta ta Sanya,, nufar hanyar fita tayi saiga driver da saurinsa yace... Hajiya Alhaji yace inzo inkaiki,, ko kallon driver d'in batayi ba tayi waje abunta,,

Sosai abun ya tunzura Aymna dake balcony yana kallon abunda yafaru,,

Aysha kam,, kai tsaye gidansu tanufa,, tana zuwa umma ta ganta da jaka, tace.. Lafiya? yayinda gabanta ke fad'uwa,, dariya Aisha tayi ganin yanayin umman take taji tausayin mahaifiyarta,, Umma garki damu fa to, Ayman d'inne yayi tafiya shine yakawoni gida wai bai amince da Zamana a can gidan ni d'aya ba,, kuma gashi banda lafiya kwana biyunn,, ajiyar zuciya umma"tasauke kafun tace... Ai shikenan Jeki d'aki ki ajiye jakar,,

         hamdala tayi a ranta nasamun sassauci anan,,
Abba ma da yadawo bayanin da umma tayimasa kenan shikam dariya yayi yace... yaran zamani kenan yo"idanma yabarta a gidan mai zai Cita? Umma ma dariya tayi tace aikuwa dai Allah dai yadawo dashi lafiya,

     *******
Surayya"sai guraren 10am ta tashi kasancewar tunda tayi sallah takoma ta kwanta,, dubawa tayi dakinsa tasamu bayann,, dan haka tashiga kitchen tasoma had'a breakfast,, tana gamawa tayi wankanta tasha kwalliya dan yau sosai takejinta wasai, a cewarta mayya dole tabarta da mijinta dama bata gama murje amarci ba ai muguwa tadhigo mata gida,,,

     Saidai me?

tana zaune a parlour tana jiran dawowarsa, taji ana kwankwasa kofa,, zuwa tayi dan ta bude,, ganin mai gadi tayi rike da envelope a hannu,, gaisheta yayi daga bisani yamika mata envelope d'in,, kar'ba tayi,, mai gadi yace... Inji Alhaji yace inbaki,,

Toh Ngode"tafada had'i da maida kofar ta ta kulle, juya envelope d'in tashiga yi, cike da mamakin mai yasa Ayman zai aiko mata da envelope? To Kodai ajiye masa zanyi? haka tashiga yiwa kanta tambayoyi,

         Wata zuciyar ce tace ai Kawai bude ki duba,, budewa tayi taga kud'i kimanin 100k

Mamaki ne yakamata, sai kuma taga wata yar paper, budewa tayi tashiga karantawa kamar haka....... Aslm ftn kintashi lfy,, ga kudinn saboda bukatun yau da kullum, wata yar tafiya ce ta taso mun ta gaggawa zuwa Florida zanyi kimanin 1week a can zan kiraki idan nasauka,, byeee take care.

   Wani gumi ne ya ratsa goshinta, tasaka hannu ta sharce shi,, kutt? Lallai ma Ayman wato dan yasamu matsala da banzar matarsa shine abun zai Shafeni? Aikuwa komai zaiyi yayinda ai dai dolensa yadawo, idan laso ka shekara a can ba 1week ba... taja 'kyaccin takaici.

          ***********


Xinnee smart 👌💞💕💋😁


Insha"Allah ina saka ran mukammala a page d'in gaba to idan hakan ya yuwu zaku kwana biyu bakuji niba,, 🤣idan kuma bai samu kammaluwa ba a next page insha'Allah zakuji ni nan kusa 🤗

Ngode masoya nah sonso 😍😘😘🤗

            KO BAZAN AURESHI BA......... Where stories live. Discover now