Page 15

1.6K 143 14
                                    

*KO BAZAN AURESHI BA...*
        _(hattara yan mata)_

           *XINNEE SMART*
  _whatpadd @xinnee_smart1_

      *Har kullum inaji banyi asaraba dan nasa daukar miki da page, maman gid'ad'ona* 😍
*Wannan shafin nakine* , *kiyi yadda kikeso dashi, Allah ya raya miki zuri'a ya albarkace su, yaqara* *danqon qauna keda* *oga*
 
*Love u over*😍❤😍
         

          _Kuna ha'kuri da qarancin_ _page fa_ 😪 _Koda dai naji wasu_ _namun kirari da lazy_ _writer_ 😹 _to Ngode_ ,

*Page... 15*

Shafin rayuwa sabuwa tabud'e a rayuwarta, dan kuwa yanzun ji take ba wacce takaita sa'a a rayuwa,

                Ga kyakyawan masoyi ga kaya na alfarma dayake siya mata, ga waya wacce sai yar wance da wane, ga kud'ad'en Kashi,

          A cikin watan iyayen Hammad, suka nema masa aurenta, take akayi komai, aka tsaida rana yakama saura wata ukku su mallaki juna,

      Wayoo iyayi, take tafara yiwa kanta tanajin irin rayuwar da zata Baza a gidan Hammad,.....

*Wannan kenan*........
**********
Surayya"kam lokacin dataji zancen su biyu Hammad zai aura har Yar 'karamar jinya saida tayi, dan kwanciya tayi a kaita'kara mata ruwa,

       Mahaifiyar ta, kam cewa tayi tafasa auren,

   Take kuma hankalinta yatashi tashiga Bawa ummanta ha'kuri, kan ta amince zata zauna da Hammad Koda da mata ukku ne, saboda irin tsananin sonsa datake bazata iya rayuwa babu shi ba,

            Babu yadda iyayen suka iya dole suka zuba mata ido, suna kuma yimata addu'a,
************

Wayarta dake kan kujerar d'akinta tajanyo, data takunna, tashiga Instagram tayi creating new account, nan tashiga tasoma, following stars daga Indian zuwa turawa mawa'ka da Yan film,

              Nan tafara posting pictures d'inta, a take tafara samun followers,

Saida tagaji, sannan ta koma, Facebook Shima tayi creating account, Shima nan tafara samun friend request,
      Yayinda itama tashiga turawa had'i da accepting wanda yayimata wanda bai mata ba, ta barshi anan,

       Tana zaune a haka har akai,   sallar zuhur,bata saniba bare ta tashi tayi, Umma ce taga bata fito ba, tashigo dan tagani,

     Ganin tana zaune ta baje sai dannar waya takeyi Bama tasan tashigo ba yasa tace, to aljanar waya, tashi kiyi sallah, sai a lokacin tad'ago, ganin umma yasa ta d'anyi murmushi, had'i da fad'in umma bnsan anyi sallah ba ai,

      Yo"dama inafa zaki sani kintasa waya a gaba, kedai Allah agajeki inbaki rasa ido ba, sanadin wannan wayar,

    Saboda Allah mutum yatasa waya a gaba, ba al'qur' ani ba, ba wani littafin addini ba, tsawon a wanni? Wlh kiraba kanki da Saida 'karfi bashi,

          Mi'kewa tayi, tana dariyar umma dan ganinta bata waye bane,

           Da dare bayan ta kwanta haka tashiga, chart d'inta,

Washegari ma haka dan yanzun ko islamiyyar da take zuwa tadaina zuwa a cewar ta, takusa aure, boko kuwa dama ba zuwa take ba,

      Yanzun ko Hammad, baya wani samun fira da ita a waya sossai, dan irin yadda kullum cikin son ganin ganin yadda hot hot guy's a duniyar gizo ke rayuwa,

        

      Yauma, tana shiga IG, taga wani jems Williams, datake following, yayi posting d'in wani, hot guy' wayooo, shine abunda Aisha tafad'a,

        Wlh yahad'u, dama da akwai irin wannan a duniya, amma wannan ko a cikin larabawa turawa da India shi d'in na musamman ne,

       Caption d'in kai taduba, best, cricket player, @AYMAN,

      Hmmmmmmm, taja numfashi, a take tashiga account d'in, nan da nan, tashiga likes d'in post d'insa wanda yawanci na wasannin cricket ne,

            Sai wasu pictures d'insa wanda dayawa yayisu ne a gurin sha'katawa,

     Take tasoma jin sha'awar kallon wasannin cricket, fita tayi a IG bayan ta gama yin saving pictures d'insa da wasu daga cikin videos d'in wasannin,

      Shiga tayi browser, tasoma searchin wasannin cricket, nan aka watso mata su, nan tahau kallo nanda nan abun yashiga burgeta, da 'kayatar da ita,

           Itace bata daina dannar waya ba saida charge yayi  'kasa, Sannan ta aje wayar,

          A kwana biyun sai ya Zamana bata posting komai saina wasannin cricket, daga ance Ayman, yayi posting wani abu to yanzunnan zatayi like tayi comments, sannan tayi reposting,

         A yan kwanakin, ita kanta bazata ce ga abunda ke damunta ba, sossai takejin son mutumin da sunansa kawai tasani, bazatace, Yama San dazaman ta ba, a cikin dubu nan masoyansa ba, tasani sarai ba Lallai yama San tanayi ba,

    A rayuwar Aisha tunda take bata ta'ba jin so akan wani d'a namiji kamar yadda takejin son wannan ba,

        Cikin kwana biyu kacal duk tabi ta rame tazabge,

        Hammad kam sossai, ramarta ke damunsa musamman rashin walwalarta idan yazo gunta, kullum idan yayi 'korafi sai tace, kewar barin gidane kuma ko wace Macce ai idan zatayi aure tana haka,

Kullum abunda take fad'a masa kenan idan yana mata  'korafi,

      Saidai shikam yakasa, yarda da wannan dalilin nata, dan yana zuwa gun surayya, idan Ammi ta matsa masa, amma ita baya ganin ta sauya, dan haka hankalinsa yakasa kwanciya,

               Saidai da yayi tunanin kodan dayake itace auta a gidansu shiyasa, sai kawai yakauda fargaba a ransa yaci gaba da al'amuransa,

       *********
Aisha kam abu sai gaba yake hartakai saida aka Sanya mata ruwa, sossai takejin jiki wanda Kowwa bai fahimci halinda take ciki ba kowa gani yake normal ciwo ne,

Wanda ita kad'ai tasan azabar datake ji a ranta, har kuka takan zauna tayi ita d'aya, tace ashe haka so yake? dama haka ake azabtuwa a so? Kodai nice yazomin a haka,?


   

    *Nidai nace Aisha Amishty Allah yakawo mafita, 🤪kufa fan's mai kuka ce🙁*







_Xinnee smart_ 👌🏻

            KO BAZAN AURESHI BA......... Where stories live. Discover now