Page31

1.3K 126 4
                                    

*KO BAZAN AURESHI BA*
         _(hattara yan mata)_

    *Whatpadd @xinnee_smart1*

  *Shiffaki"llah habibty,* *SURAYYAHMS* *Allah yasa* *kaffara ne* 🙏🏻😰

*Page 31*

Rana bata 'karya,, yau Ayman da amaryarsa surayya"suka Sauka a filin jirgi na malam Aminu kano,, sanye yake cikin suite da yayi matu'kar kar'barshi,,  idanuwan sa manne da ba'kin tabarau na kanfanin Gucci.
             Yayinda surayya ta kasance cikin shigar doguwar riga Yar Dubai, pink color, sosai rigar takar'beta saboda yanayin fatarta da kyan jikin ta,

  Sa'kale take a gefensa hannunsa a cikin nata, yayinda d'aya hannun nasa ke ri'ke da trolley d'in kayansu na kamfanin hello king.

           driver ne ya hango shi take ya'karaso gunsa cike da girmamawa yace, barka da zuwa yalla'bai  yawwa malam sani ya gida ya iyali, Ayman ya amsa cike da kulawa, lfy lau Alhmdllh ranka yadad'e...

     To Masha'Allah,, Ayman ya fad'a yana yin gaba da matarsa bayan ta gaida malam sani, malam sani ya kwashi sauran kayan su yasaka a mota,

   Asalin gidanda da zasu zauna da Hammad anan suka Sauka kasancewar dama nan akasa kayan ta sai daddy yace abarsu anan basai amaida a gidan Ayman d'in ba wanda ke kallon gidan Hammad d'in, kasancewar yasan 'kudurin Ayman d'in na auren za'binsa.

Fess! suka samu gidan ba'kura kasancewar daga gidansu surayya anturo masu aiki sun gyara musu, dan haka suna zuwa Kowwa room d'insa yanufa dan refreshing,

    Surayya nashiga room d'inta, wayanta yayi ringing sunan mommah tagani yana yawo akan screen d'in wayar da sauri tad'auka had'i da fad'in hello"mommah.... daga d'ayan bangaren aka amsa da kun iso kenan.... dama nace bari ingwada kiranki da line d'inki na  Nigeria,, gashi kuma nayi sa'a. dariya surayya"tayi had'i da fad'in wlh kuwa,, to Masha'Allah tunda kun iso lafiya yanzun za'a kawo muku abinci, to mommah mungode..... daga nan sukayi sallama tafad'a bathroom.

**************
Aisha ce keta faman shiri dan yau sukayi da Ayman"zaizo kuma ta rigada tasanar da Aunty lauratu dan itakam tuni tafad'a kitchen, a cewar ta dole tayi azama takusan kaiga suruku, Aisha kam dariya tayi tashige d'aki.....

     dafe kumatu tayi cike da nazarin wani kaya yakan tasaka dan duk wanda tad'auko sai taga Sam bai mata ba, wani tunani ne yazo mata,..... Watarana suna video call da Ayman rigar dake Jikinta lokacin irin turkey abayar nan ce red colour,, dubanta yasa keyi yace baby kinyi kyau... dariya tayi cikin jin Kunya wanda bata ta'ba jiba a gun wani da namiji,, tace... Nagode.

   Ci gaba yayi da cewa... gaskiya ina son kalar red a gun Macce bansani ba kodan kalar tana miki kyau ne.......

Zabura tayi jin muryar Action a kanta tana rangad'a gud'a.....  dariya tayi had'i da fad'in... Kai Bea wlh ni harkin razana ni.

    Wai Amishty meye haka inace keda kanki kika cemun yakira ki yace yasauka a birnin kebbi,, to mai kike jira baki shirya ba kinsan dai ba wani tafiya bne ai.......numfashi amishty tasauke... Wlh beb duk kayana ne narasa wanne zan saka,

       Kama ha'ba action tayi had'i da fad'in to!yanzun mishty duk wannan suturar da Allah yahore miki kika cewa bakisan Wadda zaki sawa ba? to nidai waallahi bnsan Wadda zani tayaki za'be ba wallah....... Fashewa da dariya Amishty tayi itama Action dariyar tayi dan dama tayi ne dan Amishtyn ta dara kasancewar taga tadan shiga damuwa,, kuma tasan yadda take dariyar hausar kebbi sosai sai kace itama ba Yar kebbin bace,..........

    Action ce tagaji da dariya tayi shiru had'i da mi'kawa Amishty laidar hannunta wanda sai lokacin ma talura da laidar,, kar'ba tayi had'i da yiwa Action d'in kallon alamar tambaya.

     Alamu tayi mata da ki bud'e kigani.... bud'e ledar tayi had'i da janyo kayan dake ciki..... Wasu matsiyatan Indian dress ne riga da skirt, masu shegen kyau sai mayafinsu sosai kayan sukayi kyau,, kasancewar kalar datafi so ne haka kuma kalar da masoyinta keso wato red.

          Kayan sun burgeta sosai dan haka tana cirowa tace woow Masha'Allah". 'kawata wannan kayan sunyi kyau, dariya Action tayi, bazan tabbatar da kyansu ba sainaga kinsan ya su, kallon bangane ba amishty taiwa Action.

gyad'a mata Kai Action tayi had'i da fad'in nidai kisaka zan shiga kitchen gun Aunty dan na hangota, tana gama fad'a ta tashi zata fita da sauri Amishty tari'ke hannunta had'i da fad'in,,

      Kai Action, ni wlh nama rasa mai zance miki... Am totally speechless..... yar dariya Action tayi tace... basai kince komai ba kawai kimun addu'a Allah ybni miji ngari mai sona Koda rabin yadda Ayman ke sonki ne....... Saidai ina fargabar kozan samu mijin aure a wannan rayuwar dana tsarawa kaina??  ta'karasa fad'a idonta na zubar da hawaye....... Wlh 'kawata ina nadamar abunda na aikata duk da nasan da saka hannun iyayena a lalace wa ta....... Amma nasan da wahala insamu wanda zai aur....... rufe mata baki Aisha tayi tace dan Allah kidaina fad'in haka insha'Allah zaki samu wanda zai aureki,, bu'kata dai kituba wa Allah danshi gafurun Raheem ne, ni bakya ganin abunda nakeyi? amma hakan bai hana nasamu wanda yakesona kuma mutumin kirki...... ai Allah yana yafewa bayinsa matukar sukayi tuba Nagar tacce hka kuma sukayi imani da duk abunda yasamesu cewa daga Allah ne,, dan haka kedai kituba kuma kiyita addu'a domin ita addu'a saiful"mumin ce.

    Amishty ta rarrasheta sosai da kalamai masu tausa zuciya had'i da shawarwari, masu kyau,, saida taga takoma daidai kafun tabarta tafita itakuma tashiga shiri,,

      'karfe 2:25 ya iso Kai tsaye sitting room d'in Baffa Kabir d'an Baffa yaimasa masauki,, ruwa yabu'kata dan gabatar da sallah,
                Bayan ya sallame Action tashiga gunsa suka gaisa ta dire masa abinci da nasha kala kala,,  har takusa fita yace... Aisha"please kice angel tafito haka am eager to see her.

dariya tayi daga bisani ta amsa da yanzun zaka ganta,

    Murmushi yayi had'i da fad'in Ngode.


to yan mata ayi a isa da kuwa gogan naki yace ke zakiyi feeding d'insa..... ta'karasa fad'a da dariya.... itama amishty dariya tayi tace amma da wasa kike ko??     wlh yace ke yake bukatar gani please kije dan da alama zuciyar sa dab take da bugawa idan baisaka angel d'insa a ido ba...... fita Amishty tayi tana fad'in ke kika sani da tsiya...... dariya Action tayi had'i da girgiza kanta tana fad'in lover birds.


    Sallama"Aisha tayi a 'kofar sitting room d'in cike da jin kunya..... amsawa yayi had'i da fad'in shigo mana.... Shiga tayi tasamu guri tazauna, cike da jin nauyi sai wasa take da yan yatsun ta,'kafun halin cewa tayi ina wuni,,

      Da Murmushi akan fuskarsa yace bazan amsa ba tunda kin'ki bari inga fuskarki saifaman sunkuyar da kai kike...... idan kuma fuskar ta saidawa ce to a fad'amun farashinta dan Koda da d'anyan gwalagwalai ne nayi alkawarin fansar ta,......... Murmushi tasaki cikin muryarta mai sanyi da dad'in sauraro tace.... Ai Koda ta saidawa ce to kaikam ka rigada ka siya da abunda yafi d'anyan gwal daraja a idanuna haka kuma nasan zaka adanata had'i da yimata sutura tamkar yadda zaka lalla'ba 'kwai......... Kallonta yasake yi had'i da fad'in gaskiyar ki domin kuwa nayi alkawarin tattalata had'i da tarairayata tamkar jinjiri agun mahaifiyarsa, Aisha bakida matsala dani domin ni naki ne kamar yadda nake zaton ke d'in tawa ce Aisha zansa ki farinciki zan shayar dake madarar 'kaunata mai cike da d'and'ano da gard'i mara gushewa a tunani.

   Nayi al'kawarin mutunta ki daraja ki had'i da baki kulawa gwargwadon iyawata ina ro'kon Allah yasa a duk inda na gaza yataimake ni ya tallafe ni.
   Fatana d'aya Allah ysa ku xauna lafiya da matata........ DAMMM! 'kirjinta yabada wani irin sauti wanda ita Sam tama manta da Ayman d'inta yanada wata mata.. Sam! ta manta... maganarsa ce tadawo da ita daga duniyar tunanin data lula....... Aisha kinyi shiru, idan dan surayya ne garkiji komai batada matsala nasan zaku zauna lafiya kema kuma nasan bakida matsala Fatana kutaru kubani farinciki.........'boyayyar ajiyar zuciya tasauke..... had'i da fad'in insha'Allah bazaka samu matsala dani ba, yanzun dai Kaci abinci..... Murmushi yayi had'i da fad'in Ngode my Angel"murmushi tayi tashiga zuba masa abinci a kunyace........





*************


*Wlh kuna ha'kuri dani fa!* 😥

*ba editing am sowwy 🙏🏻*

            KO BAZAN AURESHI BA......... Where stories live. Discover now