page28

1.2K 124 9
                                    

*KO BAZAN AURESHI BA*
_(hattara yan mata)_

*Whatppad@XINNEE SMART1*

PAGE...28

Tadad'e acikin sujuda tanawa Allah godiya cike da ikhlasi had'i da yin kirari a gareshi, daga bisani tad'ago fuskarta cike da murmushi wanda kallo d'aya mutum zaiyi mata yafahimci halin farincikin datake ciki.

Wayar tasake janyowa tana mai sake duban DM din ..........hi! am Ayman wants talk to u it"s urgent,, call me with this nm anytime u see my Dm.

Abunda sa'kon ya'kunsa kenan,, ta maimaita karantawa a fili da kuma zuci yafi sau a 'kirga,

Zagayar d'aki tashiga yi tamkar mai safa da marwa fuskarta cike da murmushin farin ciki,,

Aunty lauratu, ce tashigo dan dubata sabida tunda tayi ciwo sam batada aiki saina tunani shi yasa take yawan dubata da d'an d'ebe mata kewa.


Mamaki ne yakamata ganin yadda Aishar keta faman zarya a d'aki,, ga kuma fara'a da annurin farinciki dake sauka akan fuskarta,

Sallama"tasake yi a karo na biyu, wanda sai a lokacin Aisha ta lura da ita a gun.

dubanta tayi tace"wa"alaiki....ssa....l...l....am.

Muryarta na rawa...rawar farinciki,

Kujerar dake d'akin Aunty tazauna a kai, kafun tadubi Aisha wacce ke tsaye tana zuba murmushi, aunty ma murmushin tayi daga bisani tace...masha"Allah da alama yau yar tawa tanacikin farinciki ...yar dariya Amishty tayi tarufe fuskarta da hijab alamar kunya.

Aunty taci gaba da cewa...meye sirrin wannan farin cikin naki Aisha? dan rabonda inga kina walwala irin haka tun kafun ki kwanta ciwo ....kai ko a lokacin bana tsammanin kina farinciki irin haka,

Mai yafaru yata?sanar dani.

Shiru Amishty tayi tanaci gaba da murmushinta,, tanbayar duniya Aunty tayi amma sai cewa tyi ba komai ganin bazata fada mata bane yasa tace..ai shikenan idan tayi tsami maji,

Daga haka tafita, da farincikin yau Aisha tana walwala.
ganin Aunty tafita yasa tacigaba da neman laying Action, dan she need someone to talk.

***********
A 'bangaren surayya sossai Ayman ke bata mamaki da irin salon soyayyarsa ga wata irin 'kwallo dayake cillawa a raga,

Itakam ji take tagama morewa da mijin aure, ha'ki'ka tana jin kanta a cikin wad'anda sukayi dace da gwarzan namiji jarumi, wannan yasa ta kwantar da hankalinta tana amsar ko wanne irin sa'ko daga gareshi sai bada kai take bori na hawa,,

Take fatarta tasake fito da asalin kyau mai tattare da alamun hutu da jin dad'i dake ratsata.

A 'bangaran Ayman kuwa shi sam harga Allah bawai son surayya yakeba hasalima kulawar dayake bata yasamo asalin tun ranar da yaje gun wata budurwarsa maergol"wanda bayan yagama she'ke ayarsa bacci yayi awon gaba dashi anan yayi mafarki da Hammad"inda yanuna masa 'bacin ransa akan irin yadda yake treating surayya sam baiji dad'i ba daga 'karshe yahad'a dayimasa nasiha.....tundaga ranar yarage huld'a da mata yake 'ko'karin sauke duk ha'k'kinta dake kansa,

*Wannan kenan!*

Inajinki!cewar Action da jikinta har rawa yake dan taji mai yasa 'kawarta ta taimata kiran gaggawa, hummmmmm! Aisha tasauke numfashi, hannunta tami'ka tajanyo wayarta tami'kawa Action,, kallo action tabita dashi kafun tace mai zanyi cikin rashin fahimta,

Dm din Aisha tabud'e mata tace oyah read it, cike da zallar za'kuwa tashiga karantawa, wani irin ihun farinciki tasaka dan harga Allah taji dadi dan tsakani da Allah takeson Amishty sa'banin Nierjer,

dariya Amishty tayi ta wafce wayarta tace..nidai garki tara mana jama"a,

Wata runguma takaiwa amishty had'i da fadin masha"Allah friend am so much happy for u, we most sealibrit, nan tashiga rawa Aisha nabinta da dariya saida tagaji kafun tazauna tana dariya,

Hummmm,, babe kinsan meye?amishty tafad'a cikin muryar jimami,, dafata action tayi had'i da fadin sai kin fad'a my lucky friend ta'karasa fad'a da murmushi.....narasa tayaya zansoma kiransa barekuma inyimasa magana,,

dariya action tayi,, dan Allah 'kawata kidaina wannan zancen sai kace ba Amishty ba mai wargaza tunanin yan maza no...no please garki badani mana,, wayar Amishtyn tajanyo,,

Numbers d'in tayi copying zuwa phone d'inta.

daga bisani tamaida wayar Amishty had'i dayin dialling,, haka yadinga ringing ba a d'agaba, sossai Amishty tashiga damuwa,

Sai Action ce takoma rarrashinta, da kalaman kwantar da hankali.

Shikuwa a lokacin yana duniyar sama da matarsa .



_Am sorry ba editing so u guys should manage it!_

*Follow/@xinnee smart on whatppad*

            KO BAZAN AURESHI BA......... Where stories live. Discover now