Last Page

2.4K 200 22
                                    

    KO BAZAN AURESHI BA
     (hattara yan mata)

Wattpad@xinnee_smart1
Page43

A bangaren Ayman"tunda yaga Aisha komai nasa ya kwance, ya rigada ya tabbatar wa da kansa son Aisha.
surayya ganin yanayinsa yasauya tamkar ma ya manta da ita ne yasa taji wani irin kishi, take tasoma tari dan da gaske sarkewa tayi wannan karon... da sauri yayi kanta yana mai mata sannu had'i da bata ruwa bayan tasha ne tarin ya lafa bayanta yashiga shafawa,, 'kanwar maman surayya ce tayi sallama had'i da shigowa d'akin, gaisheta Ayman yayi cike da ladabi,,

Nan take cewa naga dare yayi ne shiyasa nace Kuzo ku tafi gida kaida Aisha ni zan kwana da surayyan.
babu yadda ya iya dan haka ya amsa da to iyah,, surayyah kam tamkar tayi kuka haka sukayi sallama, ya fita.
Yana fita yaga Aisha a tsaye jikin d'akin,, saidai ba kuka take ba wannan karon,, jin kamshinsa na rai da rai,, yasa ta fahimci yafito dan haka tad'ago da idonta dan dubansa,, wani yarrrr ko wannensu yaji da ganin d'an uwansa,
Mota yanufa ba tareda yace mata komai ba,, itama motar tanufa da sauri ta bude ta xauna,, baice mata komai ba yaja motar.

Haka ya tsinci kansa da zuwa gidanta, suna shiga yanufa d'akin sa... da sauri Aisha ta karasa gareshi had'i da rungumesa ta baya, wani irin kuka tafashe dashi mai tsananin shiga rai, cikin kukan tashiga rokonsa..... Ya mijina kadubi Allah kadubi girman soyayyar data had'amu ka yafemun wlh lokacin Hammad ne yayi amma ni Sam banida masaniya akan mutuwar sa.
Tabbas! Hammad ya ganni a hotel saidai ba abunda yake zargi ne yskaini ba wlh kawata na raka..... Sake Sanya wani irin kuka mai taba zuciya tayi,, kafun taci gaba da cewa....
AYMAN"kayi mun uzuri wlh inason ka,, bantaba tunanin rayuwa babu kai ba garka hukunta ni abisa laifin da ban aikata ba..... Tunda tasoma magana 'kirjinsa ke bugawa da karfi... idan yace baya son Aisha yayi karya idan yace baya kewar komai a game da ita yayi karya.. dad'in dad'awa baisan mai yasa yakejin ya yarda da itaba baisan mai yasa yakejin kalaman ta gaskiya bane hakann yakejin komai da tafad'a masa gaskiya ne,, shin Asha abar yarda ce kuwa? Zuciyarsa ce mai masa wannan tambayar.

A take kuma tashiga bashi amsa d Lallai ita d'in abar yarda ce dan da rana d'aya bata ta'ba baka labarin karya ba gaskiyrta kasani Ayman"garka cuci kanka tabbas kanason Aisha"dan haka ka kwantar da hankalin ka ka karbi matarka,,

Numfashi yasauke yayinda yake sake jin kukan nata har ransa,, zareta yayi daga jikinsa yana ko'karin shigewa room d'insa, da sauri tasha gabansa idonta shabe shabe da hawaye,, hannayenta duka biyu ta had'a alamar bn ha'kuri.

Tasoma mgana!

garka gujeni dan bnsan dawa zan rayu zuciyata tayi haske ba, garka barni Ayman"nashiga tashin hankali saboda sonka wannan karon Bana tunanin zan tsira matukar kabarni. 'ko'karin dukawa take caraf ya riko ta... Wata irin runguma yayi mta,

Shafar bayan ta yashiga yi,, alamar lallashi itakuwa jinta a faffadan kirjinsa yasa tayi shiru sai sauke ajiyar zuciya take,,janta yayi zuwa kan gado d'ora ta yayi kan kafarsa,, Aisha"nima bazan jurewa rayuwa babu ke ba, saidai abunda nayi ina ganin shine daidai saidai tunda kin fad'amun gaskiya hakan ya wanke dattin dake zuciyata.
Nagode daka fahimce ni mijina!

share mata hawaye yashiga yi,, inda ya'buge da Shafar fuskarta..... daga nan labari ya sauya,, sosai kowannensu yanuna wa d'an uwansa irin kewarsa da yayi,,

Asuba!

Aisha na bacci bayan sallar asuba da tayi taji mugun duka a bayan ta.... A firgice ta farka,, Ayman tagani a kanta fuskar sa babu annuri,, take itama ta bata rai had'i da fad'in malam lafiya?

            KO BAZAN AURESHI BA......... Where stories live. Discover now