Page 24

1.5K 128 7
                                    

*KO BAZAN AURESHI BA*
     _(hattara yan mata)_

    *Whatpadd @xinnee_smart1*

       

*Page... 24*

Tunda aka d'aura aure surayya"takasa samun natsuwar zuciya,,

Tunanin rayuwar ta a tareda Ayman take, wannan d'an uban zafun kan?    'karfe 9na dare aka kaita gidan sa dake had'e dana Hammad"tunda Kowwa yatafi tashiga zullumi,.....

***********
Ayman abunda nakeso dakai, kaji tsoron Allah, kasani surayya amana ce a gunka kuma idan Kaci amana sai Allah yasaka mata,

            Kuma ina jaddada maka tafiyar da zakayi katabbatar da ita kayita dan ba wanda zaka barwa ita, wata'kila ma asamu ragowar shaid'ancin ka,,

    Sunkuyar da kansa yayi dan sossai yaji kunyar kalaman mahaifinsa.

Insha"Allah Abba zaka sameni mai biyayya wa umarninka, wani irin sanyin dad'i ne yaziyarci uban dn yamanta yaushe magana mai dad'i irin wannan ta had'a sa da d'an nasa mafi soyiwa a cikin yayansa,.

           Hakan sai ya tuna masa da Hammad"yaro mai ilimin addini uwa uba sanin ya kamata wanda ke sake janyo masa 'kima a idanun al'umma,

      Wani irin hawaye ne yasirnano masa na tsananin kewar d'ansa,,

         dasauri yasa tissue yagoge,, batare da Ayman yagani ba,.

Tashi kaje Allah yayimaka albarka,

            Amin y Allah Ngode Abba Allah ya'kara girma.

Yana gama fad'a yatafi,

      

******
Shiru shiru har goma ba Ayman ba labari hakan yasa surayya,, cire ran zaizo,, dan haka tashiga band'aki tayi wankanta, tana fitowa tazira doguwar rigar baccinta milk colour,

   Duk da yunwar datake ji hakan baisa tanemi abinci ba Sai ci gaba da dakon yunwar tayi,, dan fargabar garsu had'u,

     Misalin10:30 yashigo gidan,, direct bedroom d'insa yanufa,, wanka yayi yasaka kayan baccin sa,, kalar sky blue da suka sake fiddo da hasken fatar sa wanda sai wani glowing take,,

                   Parlour yakoma ledar da yashigo da ita yad'auko, kitchen yanufa,, plate yasamu yajuye gashashiyar kazar sa da akaiwa gashin ruwa ruwa,, wani plate d'in yad'auko yazuba adadin yadda zai iya cinyewa,,

        Yad'auko cup da fresh milk, d'in da yashigo dashi,

Parlour yakoma,

       Zama yayi yaci ya'koshi yayi nak!

Kitchen yakai kayan wanke hannunsa yayi, har  yanufa hanyar bedroom d'insa,, wata zuciyar tace masa, garka manta kayiwa Abbanka al'kawarin kula da yarinyar!

       Badan yasoba yakoma,, tad'auko sauran kazar da milk d'in,, yashirya a trey, yanufa d'akinta,

      Yadad'e a tsaye yana knocking,, ba'a bud'e ba..... itakuwa cikin bacci tasoma jin knocking, tsoro ne ya kamata,, tana tunanin waye tasake jin sabon bugu, wannan karon kamar wanda ke dukan yasoma hassala,,,

                Shahadar 'kuda tayi, ta bud'e, ganinsa tayi a tsaye ri'ke da tray, saida'kirjinta yabada sautin duuuumm,,

       Bakinta ne yashiga rawa,, gashi takasa matsawa tabashi hanya,,

           Haushinta ne yakamashi, imagine tana ganinsa bazata iya cemasa sannu ba bare takar'ba kayan hannunsa dad'in dad'awa ma gashi ta tare hanya,,

            KO BAZAN AURESHI BA......... Where stories live. Discover now