Page29

1.3K 122 4
                                    

*KO BAZAN AURESHI BA*

      whatppad@xinne-smart1

Page...29

Saida yasamu natsuwa,, bayan yayi wanka yad'au wayar lokacin ne yaga missed call da  number Naija.

      har ya ajiye wayar wata zuciyar tace masa kodai itace, numfashi yaja kafun ya yanke shawarar bikin kiran.lokacin surayya"taje kawo masa cofee,
Sabida yanayin garin akwai sanyi,

Lokacin da kiran yashiga wayar Amishty,, suna tare da Action tayi mata rakiya zuwa parkong lot d'in gidan inda ta ajiye motarta, yayinda suke sake tattaunawa akan Ayman d'in.

        Turus !tayi lokacin dataga kiransa, Action ce tadubeta had'i da fad'in bea bakiranki akeyi ba?  Numfashi tasauke kan tanunawa action wayar....

   Jiki na rawa Action ta warce wayar, 'ko'karin yin received takeyi saidai kan tayi ya katse, haushi taji, tasaki d'an tsaki, dariya Amishty, tayi tace, kai Action ko d'an jan ajinnnan babu?

  Wani jan aji kuma? Kina gani harda jinya muka kwanta saboda shi...ai gwara muyi muyi.....aikuwa bata gama rufe baki ba Aisha takaiwa bakin duka, tana cewa bana son iskanci Allah nidai to.....kai beb wannan shagwa'ba haka ...dan Allah ki adanawa d'an wasa Ayman....ta'karasa fada tana mata gwalon tsokana.

       Sallama sukayi bayan sungama zolayar juna Action tatafi da al'kawarin kira taji ko Ayman yasake kira.

Itadai Aisha dariya kawai tayi tana d'aga mata hannu,

tamkar jira yake tashiga d'aki saiga kiran shi yasake shigowa,   jikinta har rawa yake,  tunani take tad'auka kokuwa?hardai takai gayin shahadar 'kuda tad'auka,

    Shiru ne ya ratsa kunnuwan ko wannensu.dan data d'auka kasa cewa komai tayi, dayaga alamun bazatayi magana bane yasa yayi sallama"hello"salam-alaiki.

     Saida tasauke 'boyayyen numfashi kan ta'amsa da wa"alaikassalam.cikin wata iriyar murya mai rawa rawa, sassanyan murmushi yasauke, kan yace kina lfy?

        Saida tayi shiru, kafun ta'amsa da lfy lau.

Fatan da Aisha nake magana?yasako mata tambayar da batayi tsammani ba,  gyad'a kai tayi tamkar yana ganinta shikuwa jin shiru bata amsa bane yace hello"kina jina?

        A sanyaye tace ina jinka, d'age kafad'a yayi tamkar tana ganinsa, yaci gaba da cewa.....kina magana da Ayman Bashir chanji.

     Shiru tayi tana juya sunan a ranta, itakuwa wata ta'baji da wannan sunan?  bata tuna ba dan haka tashafawa kanta lafiya, tahanyar ci gaba da saurarensa,
                      Aisha" a zahirin gaskiya bansan da yaushe ne ko wani lokaci ne naji nakamu da 'kaunarki ba abunda nasani kawai inasonki so wanda banta'ba yiwa wata ya mace kwatan kwacinsa ba.
                   inaso muyi magana ta gaskiya a tsakanina dake dan na tsani yaudara,  Aisha kinajina?amsawa tayi da inajink, dan itakam mamakinsa yagama kamata yanda yake magana kai tsaye.
             Cigaba yayi dacewa.zanbaki lokaci ko zuwa gobe ne mayi mgana kinga mu anan dare yayi.saida safen ......shiru yayi yanajiran mai zatace, fahimtar hakan datayi ne yasa tace Allah yatashemu lafiya.
cikin muryarta mai dad'in sauraro wanda saida yalumshe ido,,

   yana kashe wayar, tawani yi shiru tanabin wayar da kallo tamkar shine a ciki, hmmmmmmm tasauke wani irin kasalallan murmushi,  mai cike da shau'ki had'i da kaiwa hannunta cizo, dan tasake gazgatawa dagaske wai ita d'in ne?aikuwa rad'ad'in dataji ne yatabbatar mata cewa a farke take dan kuwa ba mafarki take ba.

        Wani irin tsalle tadoka had'i da fad'awa kan katifa cike da farinciki.

        ***********
A yan kwanakin sunyi wani irin sabo wanda yawancin lokuta suna ma'kale da waya wataran suyi video call wataran vc call, wataran kuma chart,  amma har yanzun baibari surayya tasan halinda yake ciki ba dan a cewarsa akwai lokacin da yadace tasani,

    Yanzunma kwance yake a kan bed, yayinda surayya ke dining tana 'ko'karin had'a jera musu lunch .

Chart yake da abar sonsa, cike da shau'ki mai tafiya da ruhi, typing yashiga yi kamar haka.....baby...tell me what color ur eyes are.

    Aisha"dake kwance kan katifa tasakeyin wani juyi cike dajin dad'in firar dasuke, ganin sa'kon yashigo yasa tasaki murmushi har dimples, d'inta yalo'ba, 

   Typing tashiga yi...dark brown almost black.

Murmushi yasaki, kafun yatura mata, you're beautiful.

   Wani murmushin tasaki had'i da maida masa, hmmm har nakai ka?

     Shima murmushi yayi, ai maza basu da kyau,

Amishty: hmmm!yadda kace ba amma ni nasan kanada kyau, 

Ayman:hmmm!to ya nake?

Amishty:uhmmm....nidai kanada kyau....if i said kyau i mean kyau..😃 a kyanma mai sanyiiiiii.........🙈🏃🏻‍♀

Ayman: dawo ina zakije, bangama dake ba

Amishty:dariya 😝

Ayman:my..... princess.....

Amishty: I'm not a princess.

Ayman :good.

Ayman:because I'm not a prince

Amishty :hhh nidai ba ce ba.....

Ayman :baki ce me ba?

Yatura yayinda fuskarsa ke cike da murmushi mai had'e da dariya,, daidai lokacin ne surayyah ta turo 'kofar d'akin nasa,,

Zama tayi a kusa dashi bayan tayi sallama ya amsa.

dubanta yayi,, murmushi tasauke kan tace Yaya abinci na jiranka,,  amsawa yayi da yawwa ina zuwa...... had'i da maida fuskarsa kan waya,

    Tashi surayyah tayi zuciyarta cike da tunani dan talura dashi a yan kwanakinnan Sam hankalinsa nakan waya tasha kamashi yana waya wanda daga yaganta zaice ina zuwa zankira anjima, itakam dai tafara zargin Anya ba watace keson 'koce mata miji ba a daidai lokacin da zuciyarta tafad'a kogin son sa ba??

    Har takai'kofa tajuya had'i da fad'in Yaya"ina jiranka, fa, please kace tajiraka anjima kwa, karasa.

    A d'an firgice yadubeta, saidai bai bari hakan yayi tasiri ba, yace banganeba, ita wa?

Dariyar ya'ke tayi kan tace... Ita 'kanwata nidai inajiranka, taja masa'kofa ta wuce.

Shiru yayi, cike da tunanin a ina tasan yana magana da wata mace, Kai mata dai sai abarsu waton duk abunda yakeyi tana saka mai ido,,

   Sallama yayiwa Aisha da zummar sayi waya anjima,,

        Tashi yayi daga shi sai boxer yafita yana sa'ka abunda zai ce mata...............











Kuna ha'kuri da rashin editing ga kuma rashin post akai akai ga gajeren chappy 🤦🏻‍♀ Kai nifa abubuwan nawa da yawa,, kuta haquri dani kunsan abu ga mai iyali 😟😹

_Follow /@xinnee_smart1_

            KO BAZAN AURESHI BA......... Where stories live. Discover now