Page 22

1.6K 113 3
                                    

*_KO BAZAN AURESHI BA...*
       _(hattara yan mata)_

           *XINNEE SMART*
    _whatpadd @xinnee_smart

_Am sorry please, nayi mantuwa a last post d'ina bansaka number ba hope dai bku rud'e ba(lol) yanzun zamu tashi a page 22 kenan 🥰_

  
     *This page is for you my darling sister flasher 💋I love you so much sweetheart 🥰Stay blessed 😍*

*Page.. 22*
Lokacin data fara zuwa makaranta,, sossai ta maida hankali a kan karatun ta,.

     Zuciyarta ta gaza sabawa da kowwa dayake cikin makarantar. hakan yasa dayawansu suke mata kallon mai ji da kanta, wanda ita Sam baidameta ba, rashin number Nierjer"shine abunda ke damunta gashi bata number ko mutum d'aya daga cikin 'kawayenta bare ta tambayi number Nierjer, a 'bangare d'aya kuma ga damuwar mutuwar Hammad" da ya tsaya mata a rai dan sossai takejin mutuwar ta tsaya mata a rai, Allah yasani bawani so takeyiwa Hammad ba amma mutuwarsa sossai tadameta.......
***************
Ayman! na rigada nagama magana dan na fad'a maka wannan zancen ba gudu baja da baya dan haka inason kasani bazaka koma ba harsai ka amin ce anyi aurenna.

      Daddy"gaskiya...... Ayman kaguji sa'bawa umarnin Abba,, ka dinga jin maganarsa, kakuma dinga bin umarnin sa,,............ Kalaman Hammad ne suka shiga dawo masa, tamkar yanzun yake fad'a masa,.

        Shikenan daddy"na'amince Allah ysa hakan shiyafi alkhairee,,
     Hakan yasamu kansa da furtawa, maimakon abunda yayi niyyar fad'a,

        Masha'Allah"to kokai fa naji dad'i sossai daka fahimce ni, Allah ya tabbatar da alkhairee, kuma Allah yayimka albarka.

     Amin y Allah.

*********
Surayyah dan Allah ki kwantar da hankalinki, dan aurann kisan Sarai babu fashi tunda har mahaifinki ya amince to fa Baza a fasa ba,,
                    Kuma ma ni banga abun damuwa a auran Ayman ba,

    Ummi"bawai Ayman ne banaso ba ummi, kawai dai nasan Ayman yafi 'karfi nane,..... dan Allah yimun shiru! Mahaifiyarta ta dakatar da ita,

   Kintaba ganin inda namiji yafi'karfin mace?

    Inaso kisa a ranki Ayman, namiji ne kamar ko wanne, dan haka idan dai ke bakifi 'karfunsa ba to shi bazai fi qarfinki ba,

   Dan haka kisoma shiri, tana gama fad'in haka ta tashi tawuce,,

       tagumi! Surayya, tarafka,, zuciyar ta cike da fargabar auren Ayman dan tasan Sam! ba tsaran auranta bane dan tanajin labarin sa a gun Na"eema, ( *Na"eema 'kanwar hammad ce wacce aka haifa wasu shekaru)*

  Sam baya son raini gashi da jiji da kai,, uwa uba kyau class da Allah yai masa,, duban kanta tayi a jikin mirror d'in dake gabanta,, gwauron numfashi tasauke,, yayinda take'karewa kanta kallo, irin hallitarta, wanda Sam gani take ko 'kafar Ayman bata kamo ba,,........ duniyar tunani ta Lula.........

*********
Sauri take,, tamkar mai shirin tashi sama saboda makara da tayi gashi yaune rana nafarko da zata soma attending lecture d'in malamin,, daga labarin data Kanji a bakunan d'alibai,, Sam lecturer d'in bashida kirki,,

       Haka kuma, ba'a shiga idan dai ya rigada yashiga,, wannan ne yasa fargabar ta yasake yawa,,
             dab da zata shiga tayi Karo da mutum! d'agowa tayi dan taga waye, sauke idonta tayi kan Aisha Lawal,, wacce ake cewa Action,, Aisha Lawal Yar gidan senator Lawal 'kaya ce yarinyar Sam batada mutunci duk makarantar Kowwa yasanta,, dan haka nema da Amishty taga itace sukai Karo saida gabanta ya fad'i,,

      'ko'karin bata ha'kuri take taji saukar Mari akan fuskarta wanda yasa saida taga taurari,, d'aga idonta tayi dan taga waye wannan?

       'Daya daga cikin yar Koran Action ce,,

            KO BAZAN AURESHI BA......... Where stories live. Discover now