Page 33

1.2K 116 9
                                    

*KO BAZAN AURESHI BA*
       _(hattara yan mata)_

*Whatpadd @xinnee_smart1*

*Page... 33*

Yau saura kwana hud'u Ayman yazama angon Aisha... dan haka ko wani 'bangare shiri ake ba kama hannun yaro,, Ayman dama tun saura sati biki yadira a 'kasar,, duk da rashin shiri da suke da surayya"hakan bai hanashi bata ha'k'kinta bai hanashi yayimata kayan fad'ar kishiya ba, had'i da bata kud'i domin tayi hidimomin bikin sai karba tayi... babu gode bare nagode.

      Shikam Sam hakan baidameshi ba, dan a cewarsa tunda haka taza'ba ai sai taitayi shi da ita aga wanda zai gaji,

tundaga Germany yasiyo wasu kayan lefen... da yazo kano ya'karasa da abunda yakeso, Baffa ne yace masa ba Sai ankawo lefe ba yabarshi a gunsa duk ranar da Allah yakawota ta kar'ba, hakan kuwa akayi yabar lefen a bedroom d'insa.

         *******
Wai saboda Allah Amishty"meye haka? Ya zakice baza ayi komai back sai walima, gaskiya nidai baki kyautanba... Action ce mai wannan zancen wanda kallo d'aya zaka yimata kasan Sam bataji dad'i ba.

dariya Aisha"tayi kan tace Wayoooo tawan ki fahimce ni please, ni kawai event d'in ne yafita kaina dan Allah muyi ha'kuri gar ayi komai, zumburo baki Action tayi had'i da fad'in ai dole in hakura tunda banice Amarya ba, kuma bazan miki dole ba,

       Murmushi amishty tayi.. tace, Kai kawata ai ko cewa kikayi dole ai kin isa dani... ba wani ni ban isa dake ba wace ni? Banza a banza d'an wake a hotel?

Hhhhh"...... Kai kawata wlh kin wuce banza a gareni kawai dai ra'ayi ne banayi.

Ai shikenan Yar bu'kulu kawai.

dariya suka fashe dashi........

**********
Ranar Asabar da 'karfe 12 na rana jama'a suka shaida d'aurin auren Ayman Bashir chanji, da Amaryarsa Aisha Abubakar D'akin gari. Akan sadaki naira100k.a mahaifarta d'akin gari family house d'insu akayi d'aurin auren.

       Yayinda wannan albishir ya riski Aysha, sujudu shukur, tayi hamdala tashiga yi had'i da godiya ga ubangijin talikai.

tadade a cikin sujadar,, daga 'kashe tami'ke ta kabbarta sallah raka'a2 tayi daga dan nuna godiyarta ga Allah nad'auka kin sarki da ya tabbatar da al'kawarin aure a tsakaninta da zabin ranta mosoyinta kuma bugun numfashinta, Ayman.

              A bangaren Ango ma abun ba'a cewa komai dan kuwa only God's know how happy he is yau Aysha tazamo mallakinsa burinshi yacika.

Ana gama d'aurin aure aka shiga shirin Kai Amarya inda ango ya kawo private jet dan yan Kai Amarya, a take aka zabi danginta masu zuwa Kai Amarya,

*********
Tun ranar da ta tabbatar da za'a d'aura auren Ayman zuciyarta ke cikin Kuna da ba'kinciki har yanzun da labarin d'aurawan ya risketa take taji wani sabon 'kuncin wanda har bata iya controlling kanta ba saida tashiga toilet tayi kukanta ma'ishi wanda take zazza'bi yarufeta........

*******
Direct motocin da suka d'aukosu gidan Ayman dake kusa da gidan Hammad inda surayya take ciki aka nufa dasu,,

       Kowwa da yazo gidan Masha'Allah kawai yake fad'i dan sosai su umma da Abba su Baffa da yayyinta sukai mata 'ko'kari dan d'akinta ko yar wani mai mukamin sai haka.

     Abinci aka kawo musu sukaci sukai nat suka yi salloli daga nan a kaita fira, Amarya kam nacan'kunshe a d'aki,, ita da'kawarta Action sai wasu yan mata wanda suke abokan wasa dasu, su ukku ne Rukayya ameena da fiddausi.

    

Bayan sallar isha'i wayarta yashiga ringing dauka tayi ganin wanda ke Kira yasa tasaki Murmushi, dauka tayi had'i da sallama,

     Amsa masa tayi da Tohm. bayan taji mai yace.

duban Action tayi, tace beb Ay me, yace ku shirya wai akwai dinner..... wata irin ihu Action tasauke had'i da fad'in Masha'Allah..... dariya amishty tayi tace Allah ya yaye miki.... Action zatayi magana kenan sukaji sallama, amsawa sukayi yayinda suke duban masu shigowa,

Yan mata ne guda biyu d'aya d'auke da kit d'ayar kuma rike da ledoji,, gaisawa suka kafun d'ayar tace amaryar mu, bro ne yace azo a miki make-up saboda zuwa dinner OK bis'millah.

   Take Halillos mai make-up da aka d'auko daga garin katsina saboda kwarewarta, tashiga aiki, kan kace me tuni Amishty ta sauya tayi wani irin kyau Masha'Allah,, woow beb.... Shine abunda action ke fad'a tana gyad'a Kai.
Itadai Halillos mai kwalliya dariya kawai takeyi dan jin dad'in yadda aketa yaba aikinta.

      Shigar blue tayi na wani dan datsetsen material, wanda akaiwa d'inkin doguwar riga, kasancewarta fara sai shigar tai matukar kar'barta, sosai tayi kyau su action ma casual make-up d'in akai musu, suma da nasu ankon daga ango

     Suma ankonsu blue ne saidai head d'in shine pink, sabanin Amarya da komai nata blue ne.

       Sosai gurin dinner d'in ya had'u ango shigar farin tattausan yadi yayi wanda ya had'a komai fari wa shigar tasa. Sosai yayi matukar kyau da kwarjini.

      Lokacin da suka shiga hall d'in take kida yasauya,,

Dinner tayi kyau da armashi dan kuwa anci ansha anyi pictures da videos masu kyau kuma an cashe, a can nahango yan XINNEE SMART NOVELS na faman kwasar kaji hardai au oo Anga banza 😜lol!

        Sai 1dare aka tashi,, ango da kansa yaja matarsa har gida suna isa yayi parking a parking lot, bude murfin tayi da zummar tafita ya rike mata hannu, dubansa tayi, shi ita d'in yake kallo, kallon juna suka shiga yi na seconds,,
    Ita tafara sauke idonta, wasa tashiga yi da warwaron dake hannunta, hannun yakamo ya sumbata, a cikin kasalalliyar muryarsa yace ina son wannan yanuna lallin hannunta yana sake mata tafiyar tsutsa a hannun, wanda take jin shi har cikin ranta,,   dan shagwa'bewa tayi wanda batasan ma tayi hakan ba, tace...dan Allah zantafi dare na dad'ayi...

       Kwantawa yayi jikin kujerar ya zuba mata idanuwansa masu rud'ar da ita,

Ba tsammani taji muryars..... Aysha... Mai yasa nakejin sonki har haka?... Aysha ina jin wani irin so a kanki wanda bantaba jinsa a Kowwa ba... Uhmm

  daburcewa tayi dan sam! bata tsammaci wadannan kalaman daga gareshi ba.

        rungumota yayi izuwa jikinsa, bai tsaya wata wata ba ya Kai bakinsa a nata yashiga aika mata da zazzafan kisses, wani yarrrr taji tsikan Jikinta yayi jin irin yadda yake kissing d'inta, take tarasa control d'inta,

         Saida taji yafara shafata ta ahamo a inda suke take tajanye daga gareshi,, bata tsaya bata lokaci ba tayi cikin gida abunta, Koda tashiga kowwa ya kwanta dan haka itama tube kayan Jikinta tayi tasaka na bacci ta kwanta.

Saidai da tarufe ido moment d'insu na d'azu ne ke dawo mata, haka tadinga doka Murmushi ita d'aya har bacci ya kwasheta.

    A 'bangarensa Shima da'kyar ya kwashi jiki zuwa gidansa, saidai me? Yana shiga parlour yatarar da wani irin bacin rai.................................






Not edited!

_Xinnee smart_ 💋

            KO BAZAN AURESHI BA......... Where stories live. Discover now