Page 7

2.2K 177 9
                                    

*KO BAZAN AURESHI BA...*

       _(hattara yan mata)_
   
             *XINNEE SMART*

     _whatpadd @xinnee_smart1_

*Page 7.......*

Sallar asubar da aka fara Kira ne, yafarkar da Abba, tashi,yayi zuwa ban d'aki  yayi al'wala, yata Yar da umma, itama tanufa band'aki,

   Raka'atanil, fijir, yayi kafun yanufa masallaci, Umma kam tana fitowa band'aki tayi nafilarta itama, aka Kira sallah, takabbarta, saida ta sallame tana azkar, ta tuno bata tashi Aisha, ba kuma tasan halinta Sarai idan dai ba, tashinta akayi ba, bazata tashi ba,

      mi'kewa tayi tanufi d'akin, wayam bata ganta ba, sai tayi tsammanin ko ta tashi tana band'aki danhaka saita koma d'aki taci gaba da azkar d'inta,

Har gari yayi haske, fitowa umma tayi dan tafara aikace aikacenta,
    Madafi tashiga ta d'ora, ruwan koko bayan ta share madafin tas, kwanukan wanke wanke ta had'a,

Kai tsaye tanufa d'akin Aisha,dan kiranta tazo ta wanke, yadda tagansa d'azu har yanzun yana nan hakanan,

    Shiru tayi tana tunanin mai Aisha takeyi a band'aki har yanzun, tunanin tane yakatse lokacin da taji sallamar Ali,

   Kallonta yayi ganin yayi kamar hankalinta a tashe,

A ladafce yace umma ina kwana? lafiya lau Aliyu, ya aikin, lafiya lau Alhmdllh, Abba yana ciki ne? Eh yana ciki, har ya nufa d'akin Abba yaji fitsari, buta yad'auka yanufa band'akin,,

Umma bama talura ba, shiga yayi yayi fitsarinsa har yana shirin fitowa, idonsa yakai kan turmi da kujera, dummm yayi kafun yad'auko su, fitowa yayi dasu yana cewa umma dake tsaye a inda yabarta.....

Umma mai kuma yakai kujera da turmi band'aki,?
tun kan yakai 'karshe" 'kirjin umma yabuga, turmi kuma Aliyu?

Eh umma gashima nafito dasu, Inna"lillahi wa inna' ilaihim"raji'un, Umma tafad'a tana zama a 'kasa da'bas, yanzun kam ta gazgata zargin ta, Aisha, ba a gidannan ta kwana ba,

     To ina taje, Yaya Ali kam tunkan umma tayi masa bayani ya fahimci, mai ake ciki Aisha ce takai turmi da kujera dan tafita,

Sossai ransa ya'baci, dan har jijiyojin kansa sun mi'ke, ransa zafi yake,

    Abba ne yafito yagansu a haka, kallonsu yayi a tsanake, kafun yace, mai ke faruwa?

Umma, cikin muryar tashin hankalin da ko wace uwa zata iya shiga yayinda a kace yarta mace baliga bata kwana a gida ba, kuma ba wani gurin cikin dangi taje ba,...........

Mallam, Aisha zata kasheni mallam..... Aisha.....

kasa 'karasa maganar tayi saboda muryarta dake shirin fiddo da kukan dake taho mata,

        Sub"hanallah, haba Maryam... haba, garki ce, zakiyiwa yarki kuka domin bashine mafita ba, addu'a itace mafita, kukanki fitana ne a rayuwarta,

     Shiru umma tayi tana sake 'ko'karin danne kukanta dan tasan gaskiya ya fad'amata, kukanta ga Aisha guba ne..

Ali kam yau ya'kudurta tabbas yau sai yayimata lahani a'kafa ta yadda bazata sake Koda mafarkin sake fita bane, musamman yadda yaga raunin mahaifiyarsu da damuwarta duk akan Aisha...........

Hannun umma, Abba yaja zuwa d'aki, Aliyu ma, d'akinsa yakoma ransa nadad'a 'Kuna,

Sossai Abba ke kwantar wa, Umma hankali, yana nunamata addu'a wa d'a shine the best thing, bawai kuka da munanan kalamai b,

           ********

A cikin sand'a da da nasani mara amfani, take sake dosar gidan,  zauren tashiga, ganin takalman Yaya Ali, yasa zuciyarta wani irin bugawa, wani irin yawu mai d'aci ta had'iye,

            KO BAZAN AURESHI BA......... Where stories live. Discover now