Page 42

1.4K 144 4
                                    

            KO BAZAN AURESHI BA...
         (hattara yan mata)

     Wattpad @xinnee_smart1

  This is for you..... Mamn gid'ad'ona,, Aunty jammy yakasai,, fateema Radda,, Mrs Mahmoud,, eashert Mustapha,, mama G,, murja Na"ikke,, Aysha Akash,,
Maikokona,, 'kawata mum teemah,, inner kime, mommy na ummu zinnira,,maman Sulaiman,, ummy yesmeen,, Maryam kolo,, mummy zaheen,, ta Annabi. 🙏❤️😍😘😍Ftn Alkhairee 🤗

Page42
Da'kyar aka samu kan Aysha,, har take gane mutane,, kwananta biyu a asibiti aka sallame ta,, inda aduk tsawon kwanakin nan Abba yayi ta neman layin Ayman"amma amsa d'aya wayar a kashe,,

     Dan haka suna komawa gida Abba yace... Aliyu yakira msa mijin Aisha"wayar Aisha Yaya Ali ya d'auka yanema number Ayman... Sau ukku yana kira bai samu ba dn haka yacewa Abba number tasa bata tafiya,,

                 Koda Abba yaji haka... Cewa yayi Koda ba"asameshi ba gobe zata koma d'akinta dan a cewarsa ko mutuwa ce gwara tad'auketa a d'akinta bare kuma jinya ce....

            Kashe gari da sassafe yasaka ta ta shirya kayan ta,, domin komawa gidanta Aisha babu yadda ta iya dan haka tanaji tana gani Abba yasa Yaya usman ya maida ta gidan Ayman"a karo na biyu!

          Sake 'kurawa sakon nata ido yayi tabbas ko shakka babu fad'a masa takeyi tana d'auke da ciki,, wani irin sanyin dad'i yaji domin kuwa Allah yasani yana matuqar son Yara,, zuciyar sa sa ce tashiga tuno masa da Aisha,, a take yaji ransa na baci,, saidai hakan baisa yaji yafasa yunkurin tafiya gida da zuciyar sa ke hasasa masa ba,, ko shakka babu yazamar masa dole yaje ga uwar dansa ko yarsa dn tabbatar da lafiyar ajiyarsa,,,

            Take yashiga shiri.......

********
Tunda takoma ta ke cike da fargaba da tunani iri... Iri,,

           Yau ma zaune take a parlour sai tunanin take,, taji ana knocking, amsa wa tayi da waye ne!? had'i da isa bakin 'kofar.... Nice Na"eema... aka amsa daidai lokacin da take bude kofar.

          duban juna sukayi had'i da sakarwa wa junansu murmushi,, shigo mana sister.. ya zaki tsaya a waje... Aysha tafad'a tana murmushi,, Na"eema ma amsawa tayi da nagode had'i da karasa wa cikin parlourn

         gaisawa sukayi Aisha takawo mata d'an abun ta'bawa,,   Aunty Aisha...Kar dai surayyah batann gidan? cewar Na"eema, kallon rashin fahimta Aisha taimata, ganin hakan yasa tace.... Surayyah ce mukayi waya kan cewa Zanzo to shine nazo gidanta inata dokawa shiru kuma mai gadi ya tabbatar mun tana nan,, shine nayi tunanin ko nan ta shigo, mai gadin bai lura ba?

Ayyah wlh bata shigo ba,, cewar Aisha.

To Aunty Bari inje insake bugawa babu mamaki ko bacci takeyi,, OK tom bari in d'auko hijab d'ina muje,,

Sunkai minti biyar suna buga kofar shiga parlourn surayyah amma shiru kakeji,, gashi Na"eema sai Kiran wayarta take tana ringing ba a d'auka,,

Aisha ce tayi dubarar d'auko key ta bude kofar da ke iya sada su ta cikin gidan ko wacce akwai kofar cikin ikon Allah kuwa ta bude da sauri Na"eema tashiga saidai basuga surayyar ba,, bed room d'inta tanufa nan ma shiru,, kamar ance ta bude toilet... tana budewa kuwa ta ganta a kwance jini na bin kafarta,,

Wani irin kuwa tayi had'i da kiran sunan surayyar... da gudu Aisha tafad'a toilet din da tajiyo ihun Na"eema,, ganin abunda ke fa ruwa ne yasa tasaki nata kukan,, bbu shiri ta fita driver takira,, suka kinkimi surayyah sai hospital,,



*****

Nishad'i yakeji! Wanda hakan baya rasa nasaba da zuwan da zaiyi gida,,

Ko a jirgi sai murmushi yake dokawa,, duk da shaidaniyar zuciyar sa dake son bata masa rai akan tunanin Aisha,, saidai hakan yakasa yin tasiri a gareshi.

Karfe8pm jirginsu ya Sauka a malam aminu kano international Airport,,

Taxi ya d'auka drove,,


**********
Tabd'i jam! Yemiiii! Kokwazami...... Nierjer ce mai wayann surutan,, bayan taje gidansu Aisha tasamu labarin takoma gidanta bayan takira ta kuma ta tabbatar mata d hakan,, saidai tayi ko'karin bugun cikinta amma babu wani bayani kwakwara da tasamu,, hakan yasake tunzura ta matuka...tana zarya a d'akin saurayinta tana sake tsinewa Aisha... Shegiya mayya,, yauwa bari ma in rarranqwashi kan wannan abun ko zan samu ma Ayman d'in ya d'an'karawa Shegiya saki.. Aikuwa tana gama fad'ar hakan ta janyo mutum Mutumin ta inda ta boye shi.....

Yana isowa gidansu yanufa saidai yasamu mummuman labari cewa surayyah tana asibiti... saboda fad'uwa da tayi bayan ta zame,,  hakan ya haddasawa cikin dake Jikinta d'aya ya fice kasancewar d yan biyu ne likitoci kuma sun samu nasarar farfad'o da ita tareda tsaida jinin.


d'akin da aka fad'a masa yashiga,, samun ta yayi a kwance ita d'aya idonta a lumshe saidai ba bacci take ba,, karasawa yayi gurinta,, hannunta ya rike yashiga shafawa a hankali ta bude idonta,, sai cikin nasa,, murmushi yasakar mata,, aikuwa itama babu jira ta maida masa dn Allah shaida ne tana matuqar son Ayman"fiye da tunani,, Fuskarta ya shafa,, had'i da fad'in,, ya jikin wife? Babyna ne ya wahalar dake ko sorry... d'an zunburo baki tayi... Kafun tace ai babu laifinsa sai naka ba Kai bane katafi kabarmu ba?? tayi wani narai narai da ido kamar zata zubo da hawaye,, yatsansa ya d'ora kan lips d'inta yace no... garkiyi mun asarar hawayenki kinji.... Yanzun ai gani nazo zan kula dake..... Sosai ran surayya yayi dad'i ji take babu maccen da ta kaita sa'a a duniya.

Flaks yajanyo yashiga had'a mata tea,, duk da tafad'a masa ta koshi...... bata yashiga yi....

'karar bude kofar toilet ne yasa dukan su duban kofar,, wani irin fad'uwa gaban Aisha yayi... Tabbas shine... Shine dai Ayman abincin zuciyarta... bugun zuciyarta... Wanda tunaninsa yake hanata sukuni.....ido ta zuba masa.... Yayinda Shima d'in ita yake kallo.... Idan yace bayason Aisha hakika yayinda karya ita d'in zane ce a zuciyarsa wanda baya gogewa,,  saidai tayi masa laifin da bayajin cewa zai yafe,, yazama dole ya kwantar da maitarsa akan Aisha idn dai har d'an uwansa nada kima a idonsa (ta zalunce ni! d'an uwana sonta nake dare da rana ashe ita d'in bata taba qauna ta ba.....) kalaman Ayman ne suka sake zuwar masa,, wani irin bacin rai yashiga mabayyani....


Surayya"kam harga Allah tama manta da Aisha a toilet tun zuwan mijinta sanyin idaniyarta,,

A zahirin gaskiya yau ganin halin da Aisha tashiga sabida ita hakan yakau da kaso cas'in na kiyayyar da take mta Lallai Aisha mai saka alkhairee da sharri ne,, ita d'in kishiya ce abar Fata,, dan haka yanzun ma tana ganinta ta sake mata murmushi,, saidai lura tayi Sam hankalinta baya gunta,, duban sashen Ayman tayi wanda Shima hankalinsa na kan Aisha,,

Take na mata ya motsa,, aikuwa tashiga Tari kamar ta sarke,, da sauri dukan su sukayi kanta yayinda Aisha ta d'auko ruwa a fridge,, Mika masa tayi had'i da fad'in bata ko zata sha,,karba yayi batare da yadubeta ba,,

      Rungumo surayya yayi zuwa kirjinsa,, wanda take Aisha taji kamar ta rungumi transfomer,

Wasu irin hawaye masu zafi ne suka sauko mata,,

Da sauri tabar d'akin,, kirjinta na tsananta bugawa,,

Jingina tayi da bangon asibitin tashiga rera kuka mai cin rai,, a zuciyarta tana mai tabbatar wa kanta saita karkato da hankalin mijinta a kanta dan Rayuwa babu shi ba Rayuwa bace a gareta,, Lallai ne Ayman ya rayu da ita domin shi d'in nata ne,, domin ta akayi shi haka domin shi akayi ta.....






Kuna ha'kuri gobe insha'Allah Allah zamuje qarshe garku qosa da bini

Wlh ina son ku! 💋





Xinnee smart 😘😘💕💅

            KO BAZAN AURESHI BA......... Where stories live. Discover now