Page 14

1.6K 153 5
                                    

*KO BAZAN AURESHI BA...*
      _(hattara yan mata)_


               *XINNEE SMART*
      _whatpadd @xinnee_smart1_

*Page... 14*

Haka Hammad, ya kwana yana tunanin yadda zai sanar da Aisha, wannan zancen danshi harga Allah yaso ya aureta ita d'ayan ta, batare da ya had'a ta da wata ba,

      Saidai kuma bazai iya 'kin bin umarnin mahaifinsa ba,

     

   Washegari"haka yayita tunanin mafita har 'karfe 5.30pm, wanka yayi yashirya cikin farin yadinsa da akaiwa d'inkin zamani, sossai yayi kyau a cikin shigar kasancewarsa chocolate, a gogon Gucci ya d'aurawa hannunsa,

        Feshe jikinsa yayi da designers d'in prhps,

            Wayarsa da car keys d'in sa yad'auka zuwa gidansu Aisha,

      Yana isa yasamu guri yayi parking, fitowa yayi, yasoma kiran layinta,

          Yaya"Ali ne yafito daga gidan, yana ganin, Hammad, ya'karasa inda yake, sallama yaimasa,

         DA murmushi Hammad yami'ka masa hannu sukai musabiha, nan suka sake gaisawa, kafun Yaya"Ali yace... Malam kwana biyu inakan tsinkayar ka, a 'kofar gidann

Dan haka dama nace idan nakoma ganinka a'kofar gidann zanyi maka magana, dan kuwa bansan abunda ke kawoka gun'kanwa ta, ba,

         still fuskarsa da murmushi, yace nayi laifi Babban Yaya, ayi ha'kuri dan Allah, amma a gaskiya ni alkhairee ne yake kawoni gun yar uwarka, dan yauma nazone dan muyi magana ta 'karshe da ita akan turo Maga bata na,

     Numfashi Ali yasauke, shikenan, zanyi magana da Aishar, nagode to Nima Ngode, nan sukayi sallama Ali yatafi,

        Yana barin gurin saiga Aisha tafito, dama tazo fitowa ta hangosu da Yaya Ali, shiyasa ta la'be a zaure,

    Salllama, taimasa, cikin murmushi mai had'e da fargaba, ya amsata, nan suka gaisa, kafun suka shiga fira,  wanda rabi duk itace keyi,

    Lura tayi Sam baya cikin wal'walarsa, dan haka ta d'an dubeshi, my heart yadai,

d'an dubanta yayi, cike da damuwa ya furzar da iskar bakinsa, kafun yace, inada damuwa, ne Aisha, cikin damuwar itama tace mai ke faruwa da harka kasa fad'amun?

                Shiru yayi kafun yace... tunanin yadda zaki fahimci damuwar tawa nakeyi,

A sanyaye tace, kadaina 'boyemun duk halinda kake ciki, just share it with me, my be I can find the way out"

            Cikin rashin tabbas da, nuna bazan rayu babuke ba, ya fad'a mata duk yadda ake ciki, yana gama bayaninsa tadubeshi cike da damuwa, ba tare da tace komai ba,

       Rarrashinta yashiga yi, had'i da mata alkawarin faranta mata sonta, zai auri surrayah ne kawai dan bin Umarnin iyayensa, amma itace za'binsa,

           Cikin damuwa tace, garka damu zanyi shawara,

da haka sukayi sallama, yatafi,





********
Wannan shine ga 'koshi ga kwanan yunwa,  ta'bd'i, kishiya,

       Aisha ce mai wannan zancen ita d'aya a d'aki,

Zagayen d'akin tashiga yi,dan nemawa kanta mafita, Lallai dole tasan abunyi, zuciyarta ce tace Aisha bakida lokaci, bakiji mai yace mahaifinsa yace ba,?

    Tsaki amishty tayi, tsohon banza kawai yayi zamaninsa yayi na wasu, to Sai na auri d'an nasa kuma inmallake shi da dukiyarsa inga ta tsiyar,

      Lallai ke mai shirin yin kishi da Amishty rayuwar ki nacikin garari, tayi dariyar Mugunta kafun takoma cewa, na'amince masoyina Hammad zan aureka Koda da mata ukku ne inkasance ta hud'u,

         Daga haka tasauke ajiyar zuciya da murmushinta na samun mafita,.............

    Yauce ranar da Abba"yabashi na ya fad'a masa mai ya yanke,

         Dan haka Shima rana nayin sanyi yatafi gidansu Amishty, dan jin mai tayanke,

                       


Dubansa tayi, da idanuwanta dake burgeshi, baisani ba kota fahimci hakan ne yasa take rud'asa dasu,

                     Hammad"tafad'i sunansa, cikin wani Salo na shau'kin so, wanda zai dad'a tunzurar da wanda aka furtawa tare da sake tsananta zazzafar 'kauna a gareshi wa ma'anbacin,

    Dubanta yayi batare da ya amsa ba,

        Bata damu da rashin amsawar tasa ba, dan haka taci gaba da magana,

        Inayi maka sonda bana shayin nunawa ko fad'arsa a gaba Kowwa dan haka bazanyi fargabar zama dakai tare da wata daban ba, kawai dai damuwata shine, irin yadda zandinga musayar ka, da wata,

         Tunanin ko zan iya jure rashin ganinka ko na awa d'aya ne bayan munyi aure shi yasa kaga jiya nakasa baka amsa,....

ta'karasa fad'a kamar zatayi kuka, Shikuwa wani irin azababben sunta yakeji yana 'Kara azalzalarsa da wani irin tausayin ta ganin kawai wai dan tunanin rashinsa na awa d'aya ne ma yasa tashiga wannan halin,

     Ganin yadda yashiga lalla'bata da rarrashi yasa ta sake logayewa tana nuna masa ita babu abunda tafiso sama da yabi umarnin iyayensa, sai dad'a 'karfafa masa guiwa take,

        Take tasake samun matsayi a gurinsa,

                             Haka suka sha firarsu, kan sukayi sallama, a take washe gari yasiyo mata waya iPhone8,


Wayooo dad'i, zumud'i farinciki amishty tamkar ta rungumi titi,




*Toh! dagann labari yasoma*🙃








_Xinnee smart_ 👌🏻

            KO BAZAN AURESHI BA......... Where stories live. Discover now