Page18

1.4K 120 2
                                    

*KO BAZAN AURESHI BA...*
     _(hattara Yan mata)_

          *XINNEE SMART*
    _whatpadd @xinnee_smart1_

*Page.... 18*

Zagayar d'aki Nierjer, tashiga yi bayan takoma gida, a ranta tana sa'ka yadda zata raba Amishty da wannan auren,

              Zama tayi a tsakiyar d'akin yayinda zuciyarta ta tuno mata da bayanin teema inda take cewa,

     Ni abunda ma banjiwa Amishty dad'i ba uwar mijin fa Sam batasonta dan da'kyar ta amince ya aureta tareda Yar yayanta,

            Numfashi Nierjer, tasauke, a bayyane tace,.. This is the right time, dole inraba Amishty da aure dole ta rasa budurcin ta, kafun aure, amma ta Yaya?

          dukan kanta tayi kafun tace, ba wannan ba Nierjer, kifara dakatar da wannan auren, murmushi tayi bayan ta tuno da tsiyar data shirya, tace, wawuyar amishty kawai, hhhhhh,

        Harda wani bani labari tad'auka 'kaunarta na keyi batasan idan nabarta tai wannan auren ba bazan yafewa kaina ba,

         Haka ta kwana tana 'kulla mugun nufinta,

     

**********
Amishty tunda Nierjer, ta tafi taji tadan samu nutsuwa dan koba komai tasan za'a samu mafita dan haka yau har baccin data kwana biyu batayiba,.tayi


       ******
Tunda gari yawaye yakama yau asabar, farinciki yakasa gushewa a fuskar Hammad dan ko bakomai yau zai kasance angon Aisha, ga kuma 'kaninsa dayake so fiye da komai, zai zo, yau zasu kasance tare duk da baiji dad'in da bazai samu d'aurin aure ba,

         

        Hajiya saudah, ce a cikin yan uwanta a side d'inta, akace ana sallama da ita,

     Fita parlour tayi ta tambaya maison ganintan wata Yar matashiyar budurwa tagani, kallo d'aya zakaiwa yarinyar kasan batada tarbiyya, wata yar takarda tabata, tareda waya 'kirar tecno mai keypads,

     Kallonta hajiya sauda tayi kafun tamaida kallonta kan takarda da tsohuwar wayarda take mi'ka mata,

                   Da alamun neman 'karin bayani, juyawa kawai yarinyar tayi batare da tace komai ba,

  Hajiya sauda tsabar mamaki da yakamata kasa dakatar da yarinyar tayi, saida tafita taji haushin rashin tsaidata datayi,

     Tana fita takira layin Nierjer, hello" Nierjer, tafad'a cike da za'kuwa taji ya akayi, Done"shi kawai yarinyar tafad'a, kafun tasake cewa hope kudina sunann a kammale?

    Bakida matsala Nierjer, tace kafun suka kashe waya,

******
Hajiya sauda kuwa d'aki tashiga ta rufe takardar tabud'e, ganintayi an rubuta ta kunna wayar hannunta,

        Tana bud'ewa kuwa taga music, playing tayi Jikinta har rawa yakeyi, muryarda batasan ta wacece ba, ce taji tana magana,
abunda yaja hankalinta sunan Hammad d'inta dataji ta ambata,Jikinta har tsuma yakeyi jin bayanan da yarinyar keyi,

Gumi ne yashiga tsatsafo mata, Lallai waton wannan yarinyar da Hammad yamatsa sai ya aura ce, to bai isaba, dole a fasa aure nan shiyasa tun farko ni bataimun ba,

     Da sauri tafita zuwa side d'in Hammad d'in saidai bata sameshi ba,

                    Dan haka tashiga kiran layinsa,...........


*********
Amishty dole kizo muje dan nemawa kai mafita, Nierjer, ina zamuje yanzun cikin taron bikinnan nidai gaskiya na ha'kura,  

          Haba Amishty amma ai kinsan bazan cuceki ba, ko?

Nasani, amma, Kinga wlh ni zantafi kuma duk abunda yabiyo baya tofa garki nemeni, tunda Bakyaji,

        take zuciyarta ta yarda da Nierjer, kan taimakonta takeson yi, dan haka tami'ke hijabinta tazura, sunzo fita wata 'kanwar Abba tagansu, gwaggo murja,

Aisha ina kuma zakuje haka gwaggo wankin gashi zanje kinsan jiya bansamu zuwa ba saboda kaina daketa ciwo shine yanzun zanje,

       To gardai ki dad'e Kinga yanzun 12,an kusa d'aura aure, to gwaggo,

     Sauri sauri, suke tafiya, har suka Sami abun hawa, suna cikin tafiya, a cikin adaidaita, harsun d'an gota wani hotel sai Nierjer, tacewa mai adaidaitar dan Allah malam, d'an tsaya inkar'bo Sa'ko,

     Tsayawa yayi a gefen hanya, cewa yayi gaskiya su sallameshi dan shi bazai iya tsayawa jiransu ba,

   Sallamarsa Nierjer, tayi, Amishty kam ba baki Sai kunni dan ita sam takasa ma tsaida tunaninta gu d'aya bare tayi tunanin nan d'in dasukazo baidace ba,

      Kai tsaye tanufa reseption, key d'in d'aki ta kar'ba,

    Suna shiga Amishty, tad'an kwanta kan gadon dan d'akin mai room d'aya ne, dafe kanta tayi, kafun tace Nierjer, dan Allah kiyi ki gama mutafi, ni nama farajin kawai gwanda mukoma gida in ha'kura da auren tunda dai yanasona,

     Nierjer, dariya tayi a ranta tace kin makaro yarinya, yau Allah ne kawai zai hanani shafa miki ba'kin fentin danayi niyya,

       Lemon exotic dake ajiye a gefe Nierjer, tad'auko ta tsiyaya, tami'ka mata sha wannan ziciyarki tayi sanyi 'kawata,

              Babu musu takarba, tasoma sha saida ta shanye duka ta ajiye a gefe take tasoma buga hamma, nanda nan bacci ya kwashe ta,

dariya Nierjer, tabuga, kafun tad'auko wayar Amishty, text tashiga rubutawa, wanda address d'in hotel d'inne,da number d'akin,,

      Sending tayi a contact d'in Hammad,

************
Lokacin da sa'kon ya riske shi, yana cikin abokansa ji kawai yayi alamun Sa'ko yashigo, dafe Kai yayi bayan yagama karanta text d'in,

      Text d'in adreshin hotel da kuma number Aisha? Kansane ya kulle, take yashiga neman layinta, saidai kuma abu d'aya computer ke fad'a masa wayar tana a kashe,

          Zuciyarsa ce tace yaje yagani Maine ne,,

Take yakar'bi shawarar, motarsa ya fad'a, kai tsaye yad'auki hanyar hotel d'in, yayinda zuciyarsa ke bugawa,................



Xinnee smart 👌

            KO BAZAN AURESHI BA......... Where stories live. Discover now