KO BAZAN AURESHI...

By xinnee_smart1

80.9K 6.5K 492

Labarin budurwa mai rayuwar Kwad'ayi da buri, cike da rashin godiyar Allah,........................ More

Page 1
Page2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9
Ban Ha'kuri.. 🙏
Page 10
Page 11
Page 12
13
Page 14
Page 15
Page16
Page17
Page18
Page 19
Page20
Page 22
Page23
Page 24
Page25
Page 26
page27
page28
Page29
Page30
Page31
Page 32
Page 33
Page 34
Page 35
Page 36
Page 37
Page 38
Page 39
Page40
Page 41
Page 42
Last Page

Page 21

1.5K 123 4
By xinnee_smart1

*KO BAZAN AURESHI BA...*
        _(hattara yan mata)_

        *XINNEE SMART*

*Happy  birthday to you my Amishty*💋

*Page..* Alhaji Bashir canji asalinsa haifaffen kano ne, mutum ne shi mai arziqi, kasancewar harkarsa ta chanji sossai take kawo masa kud'i dan haka bai tsaya iya harkar chanji ba,

     Yanayin wasu kasuwancin nasa,, kasancewar sa mutum mai taimako ne yasa kullum Allah ke dad'a budamasa a harkarsa,, ya auri matarsa hajiya saudah ne dalilin wani abokin sa Alhaji sani waton mahaifin surayyah wanda ya kasance Yaya ne a gun saudah,

        Shekarar su goma da saudah amma ko bari bata ta'ba yiba,, tun abun baya damunsu har yafara damunsu musamman ita saudah dan fargabarta Kar Alhaji yaqara aure,, matar ta haihu duk da batasan waye mai matsala a tsakaninsu ba, dan duk inda sukaje tabbatar musu ake da lafiyarsu lau lokaci ne baiyi ba,,

    A haka kasuwanci yakai Alhaji Bashir 'kasar libia inda acan yahad'u da Maryam,, inda soyayyah tashiga tsakaninsu,, wanda da'kyar iyayenta suka amince akayi aure,, saudah ba'karamun tada hankalinta tayi ba wannan yajanyo mata mummunar tsanar Maryam,,

            Zaman Maryam da saudah zamane na babu dad'i dan sam Maryam batasamun walwala a gidan idan dai ba mijin bane yadawo,, kullum tana cikin Zaman d'aki,,

      A haka tasamu ciki, saudah na gane tanada ciki tabi tashiga ta fita harta samu maganin xubar da ciki tazubawa Maryam a Lemo,

Allah ya nufa Baza a Haifa cikin ba take ya'bare, sossai Alhaji Bashir yashiga damuwa sakamakon barewar cikin, saudah kam tamkar ta taka rawa, a cewarta saita haihu kafun wata mace ta haihu a gidan,.....

Haka akaci gaba da zama a gidan batare da kowwa yasan dalilin 'barin Maryam ba,

    Tun  'barin datayi bata sake samun wani cikin ba, Sossai Alhaji yadamu yayinda itakuwa tamaida al' amuranta a gun Allah dn tasan shine mai badawa,, a haka Allah ybawa saudah ciki, saida cikin yayi wata ukku kafun asan dashi dn ita kanta batasan tanadashi ba,

   Take fi'ili yatashi a gidan yazamana sai abunda takeso za'ayi, Alhaji Bashir tsabar soyayyarsa da son Yaya yasa Sam baya ganin laifinta,

Ba qaramun ha'kuri Maryam "tayi da hajiya saudah ba, musamman a wannan lokacin,

  A haka Allah ya sauketa lafiya, tasamu d'a namiji, kyakyawa dashi, suka d'auki son duniya suka d'ora masa, hatta Maryam ba'a barta a baya ba,

      Itama sossai takeson Muhammad,, wanda itace take kiransa da Hammad,, take mahaifinsa Shima yakama Hammad yazamana Kowwa Hammad yake kiransa, hajiya saudah ganin tasamu d'an da yashiga zuciyar mijin su yasa ta d'an sassautawa Maryam dan a cewar ta aci gaba da sha'ani wai ancuci na 'kauye,,

      Saida Hammad ya shekara ukku a duniya kafun Maryam da yake Kira da Mami tasamu ciki tunda ta fahimci ciki ne da ita taboye a bunta bata fad'awa Kowwa ba, harsaida yafito da kansa,, saudah bataso ba amma haka Allah yaso dn haka ba yadda ta iya,

        Sossai sha'kuwa tashiga tsakanin Hammad da Maryam, dn tafi kula dashi akan ammy, dan haka Shima yafi sakewa da ita akan Kowwa a gidan wannan yasake janyo mata wata soyayyah a gun Alhaji Bashir,,

    Lokacin da Alhaji Bashir yasamu labarin cikin Maryam tamkar yayi Yaya dan dad'i,,

   Haka taita rainon cikin ta har ya'isa haihuwa,, wata rana akayi mata waya kan iyayenta sun rasu sakamakon hatsaniyar da ake a Lebia,,

    A take naquda yataso mata wanda tunkafun a qarasa da ita asibiti,, jini ya'balle mata,,

Sai aiki akayi mata aka fidda babyn da kallo d'aya zaka masa kasancewa ba cikakken bahaushe bane,, dan ko gashin kansa irin na mahaifiyarsa ne,,

      Maryam ko ganin abunda ta Haifa batayiba tace ga garin ku,,

Sossai mutuwar ta daki Alhaji Bashir,, hatta hajiya saudah taji mutuwar a lokacin,,

    Nan rainon *AYMAN*  yadawo hannun hajiya saudah,, inda yake shan madara, Hammad da 'kyar aka samu yadaina kukan maminsa,,

    Nan yadawo da soyayyarsa kan d'an uwansa Ayman,, tunda Ayman yataso yake fuskantar banbance banbance da Ammy ke nunawa a tsakaninsa da Hammad, dan ko laifi sukayi tare to saita Zane Ayman ta'kyale Hammad,,

   A ranar kuwa wuni Hammad zaiyi yana kuka dan har Ayman yayi shiru Shikuwa yanayi,,

       Haka suka taso da 'kaunar junansu,, har Hammad yagama karatun secondary aka samar masa gurbin karatu a Cyprus,,

    Ranar da yatafi dukansu basuyi bacci ba,,

Haka suka ha'kura saidai waya a wuni sayi sau biyar,,

      Lokacin da Hammad ke shekarar'karshe lokacin Ayman yatafi Germany,,

        Inda acan ne komai na lala cewar tarbiyyarsa yafara,, Hammad bai fahimci hakan ba Sai a wata ziYara da yakai masa ta bazata a lokacin sossai hankalinsa yatashi,,

                 Yayi bakin 'ko'karin sa gun ganin d'an uwan nasa ya daidaitu saidai, hakan yagagara, wanda har yabar duniya yana fatan hakan,,

*****************

Numfashi Ayman yasauke yayinda wasu irin hawaye suka sauko masa masu tsananin radadi da kewar d'an uwansa,,

        Sake lumshe ido yayi yayinda zuciyar sa,, ke tuno masa wai d'an uwansa wata mace ce tai sanadiyarsa,, Lallai bazan yafe Miki ba u most pay for it,,......................

************
Aisha tunda taje d'akin gari, kullum zuciyarta cikin wasiwasi take tareda nadama da 'ko'karin nemawa Kai mafita,, dan zuciyarta a Matu'kar cushe take,

          A haka'kanin baffanta wanda shine Allah yafitar a family d'in yasa yayi karatun boko yanzun haka lecturing yakeyi a university of Kalgo,,

     Yazo gidan,, ganinta yasa yanemi takardunta na secondary dan yasan lbarin komai da yafaru,, a

Allah yasa ta taho dasu dan haka tad'auko tabashi,, take yanema mata gurbin karatu a Kalgo dan sossai takardun nata sukayi kyau,,

           English shine course d'in data za'ba cikin ikon Allah suka bata,,

Ba bata lokaci tafara karatu ba kama hannun yaro,,

*MAFARI*........... 💘💋💘






_Xinnee smart_

Continue Reading

You'll Also Like

58.9K 4.5K 78
Najib yaron littafin bai dda buri da aaddu'a sai ta Allah yaya bashi mace ta gari mai ilimi Sumaiyya Yarinya ce yar karya wacce ba abinda ta iya sai...
589K 19.3K 166
Genre: Space, Doting, Farming, Time travel, Healing Alternative: 空间之农家女是团宠 Author: 小糊涂大仙 Synopsis: Xu Linyue from the 21st century crossing over with...
119K 6.6K 51
labarin soyayya da ban tausayi
11.6K 1K 56
Shin abinda nayi zan samu sassaucin allah kuwa bare na iyayena,wanda sun yi alkwarin duk wanda yayi mua'amala dani bashi basu. Taya zan tunkaresu bar...