KO BAZAN AURESHI...

By xinnee_smart1

80.9K 6.5K 492

Labarin budurwa mai rayuwar Kwad'ayi da buri, cike da rashin godiyar Allah,........................ More

Page 1
Page2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 8
Page 9
Ban Ha'kuri.. 🙏
Page 10
Page 11
Page 12
13
Page 14
Page 15
Page16
Page17
Page18
Page 19
Page20
Page 21
Page 22
Page23
Page 24
Page25
Page 26
page27
page28
Page29
Page30
Page31
Page 32
Page 33
Page 34
Page 35
Page 36
Page 37
Page 38
Page 39
Page40
Page 41
Page 42
Last Page

Page 7

2.2K 177 9
By xinnee_smart1

*KO BAZAN AURESHI BA...*

       _(hattara yan mata)_
   
             *XINNEE SMART*

     _whatpadd @xinnee_smart1_

*Page 7.......*

Sallar asubar da aka fara Kira ne, yafarkar da Abba, tashi,yayi zuwa ban d'aki  yayi al'wala, yata Yar da umma, itama tanufa band'aki,

   Raka'atanil, fijir, yayi kafun yanufa masallaci, Umma kam tana fitowa band'aki tayi nafilarta itama, aka Kira sallah, takabbarta, saida ta sallame tana azkar, ta tuno bata tashi Aisha, ba kuma tasan halinta Sarai idan dai ba, tashinta akayi ba, bazata tashi ba,

      mi'kewa tayi tanufi d'akin, wayam bata ganta ba, sai tayi tsammanin ko ta tashi tana band'aki danhaka saita koma d'aki taci gaba da azkar d'inta,

Har gari yayi haske, fitowa umma tayi dan tafara aikace aikacenta,
    Madafi tashiga ta d'ora, ruwan koko bayan ta share madafin tas, kwanukan wanke wanke ta had'a,

Kai tsaye tanufa d'akin Aisha,dan kiranta tazo ta wanke, yadda tagansa d'azu har yanzun yana nan hakanan,

    Shiru tayi tana tunanin mai Aisha takeyi a band'aki har yanzun, tunanin tane yakatse lokacin da taji sallamar Ali,

   Kallonta yayi ganin yayi kamar hankalinta a tashe,

A ladafce yace umma ina kwana? lafiya lau Aliyu, ya aikin, lafiya lau Alhmdllh, Abba yana ciki ne? Eh yana ciki, har ya nufa d'akin Abba yaji fitsari, buta yad'auka yanufa band'akin,,

Umma bama talura ba, shiga yayi yayi fitsarinsa har yana shirin fitowa, idonsa yakai kan turmi da kujera, dummm yayi kafun yad'auko su, fitowa yayi dasu yana cewa umma dake tsaye a inda yabarta.....

Umma mai kuma yakai kujera da turmi band'aki,?
tun kan yakai 'karshe" 'kirjin umma yabuga, turmi kuma Aliyu?

Eh umma gashima nafito dasu, Inna"lillahi wa inna' ilaihim"raji'un, Umma tafad'a tana zama a 'kasa da'bas, yanzun kam ta gazgata zargin ta, Aisha, ba a gidannan ta kwana ba,

     To ina taje, Yaya Ali kam tunkan umma tayi masa bayani ya fahimci, mai ake ciki Aisha ce takai turmi da kujera dan tafita,

Sossai ransa ya'baci, dan har jijiyojin kansa sun mi'ke, ransa zafi yake,

    Abba ne yafito yagansu a haka, kallonsu yayi a tsanake, kafun yace, mai ke faruwa?

Umma, cikin muryar tashin hankalin da ko wace uwa zata iya shiga yayinda a kace yarta mace baliga bata kwana a gida ba, kuma ba wani gurin cikin dangi taje ba,...........

Mallam, Aisha zata kasheni mallam..... Aisha.....

kasa 'karasa maganar tayi saboda muryarta dake shirin fiddo da kukan dake taho mata,

        Sub"hanallah, haba Maryam... haba, garki ce, zakiyiwa yarki kuka domin bashine mafita ba, addu'a itace mafita, kukanki fitana ne a rayuwarta,

     Shiru umma tayi tana sake 'ko'karin danne kukanta dan tasan gaskiya ya fad'amata, kukanta ga Aisha guba ne..

Ali kam yau ya'kudurta tabbas yau sai yayimata lahani a'kafa ta yadda bazata sake Koda mafarkin sake fita bane, musamman yadda yaga raunin mahaifiyarsu da damuwarta duk akan Aisha...........

Hannun umma, Abba yaja zuwa d'aki, Aliyu ma, d'akinsa yakoma ransa nadad'a 'Kuna,

Sossai Abba ke kwantar wa, Umma hankali, yana nunamata addu'a wa d'a shine the best thing, bawai kuka da munanan kalamai b,

           ********

A cikin sand'a da da nasani mara amfani, take sake dosar gidan,  zauren tashiga, ganin takalman Yaya Ali, yasa zuciyarta wani irin bugawa, wani irin yawu mai d'aci ta had'iye,

     Takalminta tacire, ri'kewa tayi a hannu, cikin sand'a, take takawa zuwa cikin gidan, caraf.... taji andan'ki hanunta ganin wanda yari'keta ne, yasa, zuciyarta kusan bugawa,

Ba tareda yace komai ba, yaja hannunta, zuwa cikin d'akin sa maida 'kofa yayi ya kulle,...........



*********************************
Parking yayi a daidai gate d'in gidansu, shiru batada alamar fita, hakan yasashi juyawa, kallonsa take yayinda Shima Itan yake kallo yazamana suna duban juna eyeball to eyeball,

       Surayyah"yakira sunanta cikin muryar sa, mai sanyi.......

Shiru tayi bata amsa ba, saima sunkuyar da kai da tayi, zuciyarta, na rawa rawa, batasan mai yasaba amma sossai ta kejin kishin yan matan datagani a motarsa, musamman mai ji dakan,

        Dad'in dad'awa tanason sanin ala'karsa dasu da har yad'auko su a motarsa, har d'ayar tanaimata kallon raini,

So take duk wa'yannan tambayoyin ya'amsa matasu,

        So take ta tambayesa, saidai kwarjinin sa yasa takasa tambayar sa, takasa, tambayar sa, Koda kalma d'aya, ga wani irin zazzzafan kishi dake cinta a 'kasar zuciya,

    dubanta yasakeyi a Karo na biyu, surrayah dare nayi fa,...

shiru bata amsa Shiba still gashi taki fita, kamar ya karance ta, yace,

     Please surrayah go home, we will talk later, it's late now, OK?

d'an siririn hawayenta tagoge, dan sossai take tsoron rasa shi,

Bud'e motar tayi, had'i da fad'in gud9t,

night take care, yana gama fad'in haka yaja motar suka nufa gida,

         Na"eema, dake baya talafe tamkar bata cikin motar sossai takejin tausayin Yar uwarta kuma aminiyarta na irin soyayyar datakeyiwa yayanta,

        Suna isa gida, yayi parking a parking lot,

A sanyaye Na"eema tafito,

    Cikin gida tashiga a ranta tana 'kudurta dole tasamu Yaya hammad suyi maganar da safe kota samu abunda zata'karfafa guiwar 'kawarta,...................


Part d'insa yanufa, yanashiga yatu'be yashiga wanka, coffee ya had'a yasha, sanan ya kwanta, yayinda Fuskarta tashiga yimasa gizo, tamkar yanzun yake ganinta,

                    Murmushi, yayi a ransa, yace, ita d'in dabance, cike da tunaninta bacci tad'auke shi,


***********
Dur'kusar da ita Yaya"Ali yayi, yasoma wanka mata Mari, take bakinta yafashe, abu ga farin mutum nan dann Fuskarta tayi ja,

      Ham'barar da ita yayi saida ta tuntsura,

Yasa 'kafarsa yasoma'kwallo da ita,

Belt d'insa yad'auko yasoma zuba mata tun tana numfashi, har tadaina saida ya tabbatar ta suma sanan ya'kyaleta,

Yazauna yana maida numfashi, kallonta yake cike da tsana da'kyamatar halinta, danshi sam bayajin nadamar dukan da yayimata, jirama yake ta farfad'o takar'bi sabon duka,

               Abba, tunda yasamu, Umma tadan kwantar da hankalinta, yashiga wanka dan zuwa shago, duk da a ransa bayajin dad'i ko kadan, saidai yana ko'karin dannewa, dan garya karyar wa umma zuciya,

    Dan haka Koda yadingajin kuka sai yadauka makota ne, dan bai zaci dawowar Aisha a lokacin ba,

            Umma, kuwa tanasoma jin kukan, lokacin Abba yana ban d'aki,

d'akin Aliyu, tale'ka hangen ta tayi sai faman zuba mata belt yakeyi, da sauri umma takoma d'aki, ranta na baci da dukan da akeyi wa Aisha, duk da taji tausayinta, amma dole tabari a hukunta ta, ko tayi wa kanta karatun ta natsu,

                  Koda Abba yafito zashi kasuwa, baisan halin da ake ciki ba, dan haka tafiyarsa yayi, Shikuwa Aliyu, yana jin fitar Abba yafito d'akin Abba yashiga ruwan sanyi yad'auko a fridge,

 
Yanazuwa ya she'ka matasu a Kai,

Wata irin ajiyar zuciya tasauke kafun tafashe da kuka saboda irin rada d'in da takeji,

                Kallonta yake cike da jin haushi,

Tsoro tsantsa ne a cikin zuciyarta,

     Jikinta har rawa yake, dan tunda take a duniya, bata ta'ba jin kanta cikin tashin hankali ba, irin yau,

          Idanunsa da sukayi ja, yazuba mata, wayar hannunta yakar'be, yaja hannunta kamar tsumma, ya watsa ta, tsakar gida,

     Fita yayi daga gidan yaje yakira mai gyara yazo ya d'aura mata hannunta dan tayi targad'e inda ya Kwad'a mata 'karfen belt d'in,

          Mari yaje ya siyo, yana zuwa ya d'aura mata, ya rufe kwad'on, cikin d'akinta ya watsar da ita, cikin kaushin murya yace,.....

Idan dai ke, shegiya ce ba yar halak ba, kisake fita, kuma wlh idan dai ciwo yakama uwarmu, to Kisani bazaki bini bashin rantsuwa ba, I will make sure kema kin..........cikin takaici yawuce ba tare da ya'karasa fad'in abunda yake son fad'a ba,


Wani irin azababben kuka Aisha tasaka, wanda tundaga zuciyarta yake fitowa.....

*************
Nierjer, tana tashi taga bataga Amishty ba, dariya tayi,had'i da fad'in shegiya ga tsoro ga rashin ji,

           Saida tayi karin kumallo a gidan kafun tashiga Shiri, ita dayake gidansu uwa ba kwa'ba ne,

        Tana cikin dudduba kayanta ne, taci Karo da pant da bra d'in Amishty, wanda da alamu garin sauri ne, ta manta su,

        Cikin seconds, wani irin shu'umin tunani yazo mata,

Dariyar Mugunta tayi, had'i da fad'in, Aisha Abubakar 'Dakin gari,...... U are in my track........

           

           *Azumi* 😪🙇🏻‍♀



_Xinnee smart_ 👌🏻

Continue Reading

You'll Also Like

53K 1.8K 12
Just walk in and read, I promise u are going to be mesmerize with the emotional love story embedded in this novel.
37.1K 737 10
A girl that was raised by a single Mum, she's a Baker, a henna designer meet the love of her life, but In between their love lies another love, what...
589K 19.3K 166
Genre: Space, Doting, Farming, Time travel, Healing Alternative: 空间之农家女是团宠 Author: 小糊涂大仙 Synopsis: Xu Linyue from the 21st century crossing over with...
28K 1.7K 22
Tayaya ummi da salman zasuyi rayuwar aure wanda da abaya basu son junan su an hada su AUREN HAĎI ku biyoni muji yadda zata kaya