KO BAZAN AURESHI...

Af xinnee_smart1

80.9K 6.5K 492

Labarin budurwa mai rayuwar Kwad'ayi da buri, cike da rashin godiyar Allah,........................ Mere

Page 1
Page2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 7
Page 8
Page 9
Ban Ha'kuri.. 🙏
Page 10
Page 11
Page 12
13
Page 14
Page 15
Page16
Page17
Page18
Page 19
Page20
Page 21
Page 22
Page23
Page 24
Page25
Page 26
page27
page28
Page29
Page30
Page31
Page 32
Page 33
Page 34
Page 35
Page 36
Page 37
Page 38
Page 39
Page40
Page 41
Page 42
Last Page

Page 6

2.1K 165 14
Af xinnee_smart1

*KO BAZAN AURESHI BA...*

      ( _Hattara yan mata_)

          *XINNEE SMART*

_Whatpadd @xinnee_smart1_

*Kuyi ha'kuri dajina shiru yarona ne bashida lafiya,*

*Having a friend like you is a  blessing, I love you so much Dear* *surayyahms* 💋
*Page 6......*

Cike da yanga da iyayi, itama tabada tarihin amarya, tana gamawa tami'kawa Mc Mike, takoma gun Zaman ta, raba idanuwa tashiga yi, dan so take tasake ganinsa ko sau d'aya ne,

       Bazatayi 'kasa a guiwa ba, gurin cimna burinta, tabbas sai tacika burinta,

Har aka kusan tashi ba tasake ganinshi ba, hakan yasa hankalinta tashi, wata zuciyar ta ce tashiga rarrashinta.......

   Ana tashi tafita waje ta tsaya daga gefe tana duban masu fitowa Nierjer ce ta hangeta...

Amishty, mai kikeyi anan? Kizo muje Kinga antashi karmu rasa abun hawa,   mtss Nierjer, nemansa nake sonake insake ganinsa kafun intafi,.... Amishty kardai fad'amasa zakiyi kina sonsa.....

    Mtss matsalarki kuskuren FAHIMTA,  ke kanki kinsan wannan baya cikin d'abi'ata kawai dai so nake inbarmasa alamar 'kaunata a gefe kafun da kansa yabiyo ni, d'an qaramun tsaki Nierjer, tayi,

   Kafun tace, confidence d'inki akan komai yana bani mamaki, dariya amishty tayi garki manta Nierjer, wannan d'in muradina ne burina ne, kedai kawai... Watch me and see how I will win the game.... d'an rass gaban Nierjer, yayi Kodai amishty taji mai nace ne?

Hangosa da tayi ne, yasa tayi saurin kallon amishty gani tayi ita bata ganshi ba,

           dan haka taja hannun amishty had'i da fad'in Bea muje daga baya mayi maganar,

Amishty da bata lura da komai ba, tace Nierjer kindai hanani ganin, sanyin idaniyata ko?

Batace komai ba, tana ri'ke da hannunta har Suka Kai gurin wata mota, bud'ewa tayi Amishty tafara shiga kafun tashiga,
            kasancewar wanda zaija motar bai 'karaso bane yasa sukayi shiru suna jiransa, side d'in da Amishty take aka fara'kwan'kwasa wa,

            Nierjer, ce tafara hango shi kasancewar gurin da wadatuwar haske, Amishty kam bama tad'ago ba bare tasan waye, jin da tayi ansake dokawa ne, yatilasta mata d'agowa dan taga wani mai nacin ne,

      Caraf idonta yasauka akan nashi, wani irin fad'uwa gabanta yayi,
            Nierjer kuwa jitayi kamar ta si'ke dan haushi,

Wiping glass d'in tayi, a d'an yangance tadubeshi had'i da fad'in how ca can I help you?

       A ta'kaice yace ohh sorry,

Gani tayi ya koma gun zaman, driver yabud'e yazauna,

Mamaki ne yakama Amishty da Nierjer, mamakin su ne yasake nunkuwa lokacin da, wasu Yan mata biyu suka zo,

d'ayar ce tayi saurin cewa, sorry Yaya hammad" Na"eema ce ta tsaida mu, bayan, nadad'a mata cewa kafa bude mana motar, tazo mutafi saita tsaya surutu, yi ha'kuri nawan kaji? ta'karasa fad'a cikin wata irin kwantacciyar murya,

          Komai baice ba, kawai 'ko'karin tada motar yakeyi,

Dasauri mai maganar, tabude kusa dashi tazauna wacce aka kira Na"eema ce tabude bayan zata zauna, karaf idonta yasauka kan, su Nierjer, da amishty,

          Kallon su take yayinda Suma suke kallonta,

Yaya"hammad wa' ennan kuma fa?

           Cikin sayin muryarsa mara son hayaniya yace, get in to the car... shiga tayi mamaki nasake kamata, sai da tayi magana sannan, d'ayar ta lura ma da mutane,

          Juyawa tayi ta'kare musu kallo sannan tamaida dubanta kan hammad, bude baki tayi zatayi magana, surayyah... yakira sunanta da alamun tayi shiru,

Dole tayi shiru ba wai dan tana so ba, sai dan tasan shine mafi alkhairee a gareta.,

Amma zuciyar ta, cike take da tambayoyi, a game da matan datagani a motar sa, duk da tasan shi d'in ba ma'abocin Yan mata bane, amma zataso sanin dalilin shigar su motar sa, kodan irin sonsa datake dakuma wahalallen kishinsa dake damunta,

           Ba wanda yasake cewa komai, a 'bangaren Amishty abu biyu ne, keyawo a kanta, sake ganinsa a karo na biyu, taji dad'in hakan, saidai, wacece wannan data zauna a kusa dashi, meye alaqar ta dashi datake kiransa nawan, zata so sanin matsayin ta a gunshi,

Saidai tun kafun tasan wacece ita, tayi wa kanta alqawarin matuqar budurwasa ce tofa saita rabashi da ita, ko ta halin Yaya,

                 Nierjer, kam tarasa mai takeji, bakin ciki ko farinciki,?

Parking yayi a daidai 'kofar gidansu teema, shiru baice komai, ba dan haka suka fita,

          Suna fita Nierjer, ce ta tsaya cewa mungode fa,

Amishty kam tuni tayi gaba cikin tafiyarta tamkar wata role model,

Shiru yayi bayan sunfita, kafun yaja motar,zuciyarsa cike da tunanin, wannan wacece,? mai takeji dashi? tashigar masa mota batare da izinin sa, ba, Ya kyaleta yakawota har gida, amma hakan baisa yasamu koda kalmar thanks ba,

     Murmushi, yayi, take surayyah dake lura dashi ranta yasake 'baci, dan sossai taji wani kishi yakamata,

      Amishty kuwa suna shiga gate d'in gidansu teema tadafe kai, tana jimanta wa kanta yadda zata ci ubanta a gida, tunda take rashin jinta bata ta'ba kwana a wani gidan ba, sai nasu,

    Yaukam tasan tilas ta kwana a waje, meye mafita gobe da safe? Wata zuciyar tace, sai me dan andakeki aiba kasheki za'ayi ba,

                 Ko bakomai ai wanka yabiya kudin sabulu, bu'katar maje hajji sallah,

    Nierjer, ce tad'an bigeta, firgit tadawo daga duniyar tunanin data Lula,

          Bea wai yanzun Sai mu kwana a gidan nan, bayan, kuma Amarya tana d'akinta? to Nierjer, a ina kikeson mu kwana idan ba anan d'in ba?
   Mtss, tayi tsaki tayi cikin gidan,

             Da dan hayaniyar mutane wadan da suka dawo daga gun dinner, kai tsaye d'akin teema nada suka nufa shima da mutane amma ba sossai ba, cire rigar Jikinta tayi tasamu zani tad'aura,

Kwanciya tayi zuciyar ta na lugude, wani sashen na son sake ganin wannan hammad d'in,

           Wayarta taciro, tashiga chart, dan yadan debe mata kewa,    a haka bacci barawo yayi gaba da ita,...... cike da neman mafita,

*Washe gari*......

Tanayin sallar asuba, tahau kakamta kayanta, saida tahada komai, sannan tafice daga gidan, ko Nierjer, bata tsaya tayarwa ba,

Da'kyar tasamu abun hawa,

          A daidai 'kofar gidansu, aka sauketa, sallamar mai adaidaitar tayi, tsayawa tayi ta'kurawa'kofar gidansu ido,

    Zuciyarta naci gaba da bugawa, wani irin da nasani na shigarta,

Wani irin hawaye ne yasirnano mata, zuciyarta na wani irin rawa, haka ta'kokarta tanufa gidan yayinda duk takun da tayi sai 'kirjinta yabuga,.........



_Xinnee smart_ 👌🏻

Fortsæt med at læse

You'll Also Like

20.7K 1.5K 40
labari ne akan Najma, wacce hasada, kyashi da yayu nata ya sanya a suka mata auren dole , inda zata fuskanta k'alub'e iri-iri a rayuwa. ku biyoni don...
2M 98K 37
Presenting the story of ISHIKA MEHRA Whose innocence made the king bow down to her AND ABHIRAJ SINGH RATHORE Whose presence is enough to make the per...
31.9K 990 46
ROMANTIC LOVE STORY,IS ALL ABOUT AN ORPHAN WHO SUFFERED ALOT FROM HER STEP MUM,BUT LATER HAVE A BETTER LIFE WITH THE HELP OF 3 PEOPLE,,JUST READ ND...
700 99 61
A ka ce dukiya maganar mai ita takeji, hak'ik'a na k'ara gasgatawa a lokacin da idanuwana su kayi tozali da wannan katafaren d'akin da ya k'awatu da...