'kanwarta Mareeya tashigo,

Sallamu"alaikum,
"shiru bata amsa ba, kasancewar ta Lula duniyar tunani, d'an girgizata tayi, a sanyaye tadubi 'kanwar tata,.

Surayya" lafiya kuwa?

Murmushin ya'ke tayi,, lafiya mareeya...

A, a garkiyimun 'karya, surayya tunani fa nasamu kinayi,ki fad'amun gaskiya mai yafaru?

Ajiyar zuciya tasauke, mareeya, Yaya hammad.. ne,

Kallonta mareeya tayi,

Yaya hammad, kuma? ai inace tuni kuka wuce gurin..... Amma mai ya had'aku?

Shiru tayi kafun tafad'a mata duk abunda yafaru,

Dafata Mariya tayi....

Kinga Aunty surayya "namiji yanzun kofa aurensa kikayi sai kina had'awa da addu'a, bare kuma tun farko dama kece kika fara nuna 'kaunar ki a gareshi dan haka dole ki koya jure komai daga gareshi,

Kai kawai ta iya d'agawa,

fita Mariya tayi tabarta, zuciyar ta cike da sarqaqin tsoron rasa hammad,.....

*Wannan kenan*

Zama Yaya"Ali yayi yana gaida umma bayan dawowarsa daga asibiti, amsawa umma tayi had'i da tambayar sa, gurin aikin,

      Alhmdllh, yabata amsa, shiru yayi nad'an lokaci kafun yace..... Umma zancen Aisha ne, yakawoni, jin abunda ya fad'a yasa umma maida hankali kanshi, cigaba yayi da magana umma naje gun Abba kasuwa naimasa bayanin wani abokina ummar yanason ta yacema yau idan anmasa izini zaizo sugaisa kuma wlh umma' dagaske yake,

         Kallonsa umma tayi, to shi mahaifin naku mai yace?

umma, ai kinsan halin Abba akan Aisha, cewa yayi wai idan dai ta amince shikenan,.... ni a ganina umma ai bawai sai anjira amincewar ta ba, ko kuwa?

   To Aliyu nikam saidai ince Allah ya tabbatar da alkhairee,

Amin"

ya fad'a bawai dan hakan yaso tace ba, so yayi tace sai Aisha ta auri ummar ko bataso, amma ya'kudurta a ransa shikam dole Aisha ta amince da ummar,

              Mi'kewa yayi yanufa d'akinta, samunta yayi a kwance kan abun sallah, idonta a lumshe duk da dai da alamu ba bacci takeba, saboda
yanayin yadda take kad'a 'kafa,

             Tsawa yadaka mata, wanda yatilasta mata tashi firgigit, dubansa take a tsorace dan duk tsiyarta Aliyu na saita ta,  

Kallonta yayi a wulaqance, ke kinajina? dasauri ta gyad'a kai had'i da fad'in Eh,

Gud"abokina ummar nan zuwa yau danku gana, ki tabbatar bakiyi abunda zai tunzurashi ga fasa aurenki ba.....

Kallonsa tayi idonta cike da alamun zakasha mamaki, kinji ai mai nace, amsawa tayi da Eh naji,

  Tsaki yayi yafita,

Yana fita, tayi wani uban tsalle, Kanbuuuuu, dama Yaya"Ali wannan Umar d'in abokinsa yake nufin zan aura mai shegen kai kamar gwangiri,?

     Godforbid' over my dead body, wlh ai da in auri wannan mai kama da wadanni gwara in mutu banyi auren ba, mtss wannan ma ai bazaiyi wuyar yaudaruwa ba.....


Haka kuwa akayi da dare, Umar yazo gidansu Aisha, ba 'bata lokaci tafito, bayan sun gaisa yasake fad'a mata dalilin zuwansa, sannan yanemi amincewar ta bata'bata lokaci ba tafad'a masa ta amince dashi,

sossai Umar yaji dad'i dan yadad'e yana sonta kawai dai shakkar fad'a mata yake ne, dan ganin kamar tafi'karfinsa,

      Ashe ba haka bane, a ganinsa,

Bayan sun d'an ta'ba fira yayi mata sallama yatafi,

Haka yadinga zuwa fira gunta sossai tasake masa, Shikuwa sai jin dad'i yake yasamu kyakyawar Macce mai 'kaunarsa, a 'bangaren Yaya"Ali da umma ma, sunji dad'in yadda bata kunyata su ba,

    Itakuwa a d'age take kallonsu, a cewarta time ne zai sake sanar dasu sun mance wacece Aisha.......

   Yauma kamar kullum yazo fira, yana zuwa ta shirya tafita,

Sallama taimasa, ya amsa fuskarsa cike da farincikin ganinta dan sossai yakeson Aisha shiyasa wani lokacin idan yazo sai yaji kamar gar yatafi,

       Fira yafara rattafawa, na irin yadda idan yakoma gida yake missing d'inta,

d'an munafukin murmushi tayi na ganin plan d'inta zaiyi aiki a yanzun batare da wata matsala ba,

d'an karkacewa tayi tashiga zayyana masa ai itama sossai ta kanyi kewarsa musamman muryarsa nan mai dad'i,

Shikuwa kamar sauna yashiga washe baki, caraf kuma yace,

Yawwa... Wai nikam bakida waya ne? dariyar mugunta tayi a ranta kafun tace Eh wlh banda,

Haba haba.... ai yakamata kiyi waya my dear, kodan indinga jin muryar ki, idan ina gida ko gun aiki, kokuwa? Ya fad'a dason jin ta bakinta,

     Eh nima zanso hakan.... tafad'a a sanyaye,

To bari mugani zuwa jibi akwai kud'in danake saka ran samuwarsu tom insha'Allah zandubamiki ko tecno ce, d'an murmushi tayi had'i da fad'in

to Ngode fa,

      Haba bakomai ai, bari intafi, nan sukayi sallama, yatafi,

Shiru tayi a d'aki bayan tacire hijab d'in Jikinta, murmushi tayi had'i da fad'in saura planB.............................








_Xinnee smart_ 👌🏻

            KO BAZAN AURESHI BA......... Where stories live. Discover now