Sake Baki Ma'inah tai tana ganinsa da idanun mamaki wai me ma Zaid yakeyi anan asibitin tareda ita any'a kuwa Zaid Muhammad Zabir ne ZMZ Bulders CEO take gani Ko dei gizo Idanuwanta suke mata "Me kakeyi anan Sir?  Nan ta ke yami'ke cikin sassanyan murya yace "Ma'inah from now on please call me Zaid because we are teaming se mun samo miki Justice I mean Maisha must pay for her deed.
Dasauri ta girgiza Kai "No sir, Maisha Y'ar uwa ta ce kuma ba nason ayimata komai sabida kai ba'rene cikinmu bakagama sanin ha'laiyar muba tukunna, Ni ce mai laifin anan, so please you just have to mine your own business Sir.

          ***************
Ku'kur!, kurkukkur!, Kakeji 'karar adedeitarda Maisha take ciki, se yanzu suka 'karaso asibiti. Babu abunda kakeji cikin keken se mugun tsakin da Ma'isha take tun shigewarta tana huci haushin Adedeitar takeji tamkar ta ta'kashi ta6ace kowa yahuta.  "Wannan banzan machine d'in naka wallahi gwara kawai ka 6a66alata kahuta da wahala domin iskace kawai take wahalar da Mai kayan Kara.

Mai Adedeitar bai amsaba, haka ta kwaso akwatunanta tafice "Malama kud'in fa? Muguwar tsaki ta tsakar masa "Ba'nida kud'i toh, dawannan akolar keken naka kake wani tambayata kud'i, Money hungry. Murguza masa ba'ki tasakeyi sannan tafara tafiya.

Allah ya Isa, Amsarda ya maido mata kenan sannan yaja machine d'insa yatafi. Ko 'Dar Maisha batajiba haka ta'karaso cikin asibiti tun akofa akasa ta ijiye tarkacenta sannan ta'karaso, gun reception tafara zuwa tana tambayansa ko akwai wata mai kamada ita wacce akayi admitting a asibitin, Aiko dasauri ya amsa mata cewa sunanan sama d'aki mai lamba shida tareda CEO Asibitinsu. Ko godiyarta bai samuba haka tahauro sama a guje tana Allah Allah suhad'u da Zaid tun kam ta 'karaso ciki sabida ganin Ma'inah awannan lokacin zai iya sata hawan jini domin akan Zaid zata iya hallaka mutum har lahira.

Aiko tana sa 'kafa karshen matakala se ga Mutumin "Zaid" tafad'a cikin farin ciki, wayar dake hannuntane ya fad'o 'kasa yayinda ta'kara kuremasa Ido tanacewa I'm sorry Zaid please karkayimin haka, Zaid wallahi Sanka nake, Kuma kai ne tsanadiyar fad'an damukayi Ni da Mainah, wallahi zan iya jure komai Amma banda rashin ka, please you need to Understand me Sir I love you so much, Inaga kawai kafad'amin abunda zanyi maka wanda zaka yarda dani har muyi aure  Kuma idan kanason nabawa Ma'inah hakuri fine wallahi zanyi adalilin ka..... 

Bai tan'kamataba wayarsa yafitar cikin aljihu Kai tseye ya'kira layin Security, minti d'aya Basu 'karaba nan da nan suka 'karaso wajen "Take her out" yafad'a cikin sanyin murya Wanda idan bakasa hankali akansaba ba lallai ne kagane abunda yakecewa ba. Babu musu suka kwaso Maisha sama, wacce batasan hawaba bare sau'ka jinta tai kurun ahannun katti inda suka sauketa kasa har gate in fita, akwatunanta suka jefota dasu sannan aka rufe gate.

"Innalillahi wa Inna ileihi rajiun,  Y'ar Sambo Maidugu yau ake wulakanta, Maisha Sambo Maidugu yarinya Mai millioyi da kadarori aka wulakanta ayau. Toh Wallahi this will be the first and last wannan bazata 'kara faruwa dani ba.
Mikewa tai cikin tsananin 6acin rai ta gingimo akwatunanta tamkar mahaukaciya ta tseida mai taxi. Tukin awanni biyu ne kacal suka 'karaso gidanta shi wannan mai taxi 'n ma Sanda sukayita rigima har suka tara jama'a awajen dalilin biyan kud'in mota, akarshe wani mutumi ne yabiyamata sannan kowa ya watse.

"Banza d'an wahala. Tana fad'in wannan tafara bubbuga kofar gate in gida tun tanayi a hankali har tanemo tsanda tanata bibbigewa tana ihu cewa Mai gidan ce abud'e mata. Amma duk wannan shiruu takeji babu amsa ko motsi aciki. daganan ne tafara kwalawa Mai gadi 'kira, har yanzu dei babu motsi cikin gidan alamu sun nuna cewa duk an korosu.
Layin wayan Habu mai gadi tasaka, cikin damuwa tayita goda layinsa bubu network shima da alamu ya koma 'kauyensu.
Salati Maisha tafara saukarwa tana mamakin Saminu, yaushe sukayi maganan gidan har yafara tsara dokokinsa aciki, Kuma shi waye da zai koromata masu aiki wa'inda suka dad'e da juna tun tana kan'kanuwa.

   
***********************

Abba har ka fito, ya jikin naka? Asad yami'ke cikin girmamawa yana kokarin kar6omasa jakar dake hannunsa.   "Kai gafara nan Malam bakada hankali ne Kodei makaho ne kai?  Makaho kuma? Asad ya'kara kuremasa ido cikin mamaki yace Abba ban ga'ne abunda kake nufi ba kuma...

Tagwaye (Identical twins) Where stories live. Discover now