Part 1

12K 521 72
                                    


___TAGWAYE💏 BY BASMA BASHIR

Da sunan Allah mai Rahma mai jin kai.

Note👇👇👇
Ina mai matukar bukatan had'in kanku tareda shawarwari dakuma votes, kuna iya yin comment domin nasan ra'ayoyinku😍😍😍 Thank You

❤❤TAGWAYE❤❤

Gida ne kantameme mai d'aukan ido, ka'ce ba'a 'kasar nan tamu Nigeria aka ginataba. Kana shiga wani iska mai matukar gamsarwa zakaji ajikinka sabida yawan Flawowi dakuma ruwa wanda turawa suke 'kira Swimming pool acikin gidan akwai dabbobi irinsu 'Dawisu, Karnuka da tsunsaye gwanin ban sha'awa tamkar wurin shakatawa ta Gwamnati.

****
Mota ce baki wuluk 'kirar Cross Tower ta gangaro kofar gidan tana Horn babu sassautawa sekace daga sama tafad'o. Mai gadi tun baigama uzurinda takaishi bayan gidaba yafice aguje yana had'a gumi sabida kuncewarda cikinsa yayi tunda safe yaketa zirga zirga cikin bayan gida.

Sanin halin Madam d'in tasu yasa Malam Habu yafice aguje yadanna remote dake makale a saman gate d'in sannan tawangale.
Kamar ko ya sani mai gidan ce MA'ISHA tashigo babu alaman sassauci tattare da tukinta 'Kiiiiii ta taka birki a dedei wajenda tasaba ajiye motar.

Fitowa tayi "Hadeddiyar y'arinya mai kimanin shekara ashirin" tana taku d'aya d'aya tamkar babu jini ajikinta, Bakar gilashin dake makale a idanuwarta ne tacire cikin 6acin rai 'Habubakar na tsallameka, kafara tattara kayanka tunda wuri sabida banson kaqara koda awa guda anan gidan ka fahimta'. Ma'isha tafad'a batareda juyowaba. Hajiya kimin afuwa, na'san nayi kuskure amma dalilinda yasa banfito nabude mikiba, Hajiya wallaahi tunda safe naketa gudawa cikina ba lafiya.

Wannan kuma kai kajiyo sabida banice nad'aura maka ciwon cikinba, And beside nasan tsiyan talaka daman ku bakwa rabuwa da ciwon ciki se kuyita fama domin ni Ma'isha Tilon Y'ar Alhaji Sambo Maidugu nafi Qarfin wulakanci wallahi.
Tana fad'an haka tajuya a fusace tayi cikin gida, Tana bude kofan Parlor fiskarta ya chanza wanda ya bayyana murmushi mai kwantar da hankali; Baby Sorry nabarka kai kad'ai a gida kuma nasan kayita jirana koh?
Wani d'an saurayine ya amsa mata; Babu komai beb kinfi karfin haka, ke ai agogoma dakanta wataran se'ta jiraki.

Fashewa da dariya Ma'isha tayi 'Amma Faruq bakada dama wallahi haka kace koh. Ehh mana Ma'isha Ammafa kinajin dadinki Y'ar Alhaji Sambo Maidugu yanzu ke kad'ai kike rayuwa cikin Wannan kataparen gida?
Ma'isha tana shiryamusu abinci a dining yayinda take amsa mishi; Uhmm ni kad'ai nake rayuwa anan kuma wallah rayuwata anan d'in tafimin rayuwa achan gidan so D'ari. Domin ni bazan iya rayuwa da wannan Y'a data kwacemin dukkan farin ciki a rayuwata ba na tsaneta.

Faruq yamike cikin d'aurin kai yaje yakamata suka zauna akujera yana bata abinci a baki 'Baby wallahi nima ina tayaki kishi, yanzu da'ace ke kad'ei ce Y'ar Alhaji Sambo Maidugu wallahi ina mai tabbacin cewa kina chan kasashen waje tareda Abbanki kuna kasuwanci amma yanzu wannan Twin sister'n naki mai farar kafa...
Twin What? Ma'isha tamike cikin 6acin rai ta tsinke shi da mari a fiska 'Faruq tashi kabarmin gida bana 'kaunarka kuma daga yau se yau karka sake kashigomin gida dasunan kazo muyi zance na tsaneka sabida duk mai had'anida MA'INA makiyi nane.
Mikewa Faruq yayi wuf yarungumota yana hawaye 'I'm Sorry love kiyi hakuri.

Waye kuma wannan Ma'isha? Irin firgitar da Ma'isha tayi dakuma tsoron daya bayyana a idanuwarta yasa zakasan cewa wannan Dattijon dayayi magana mahaifinta ne Alhaji Sambo Maidugu. Dattijo ne mai farar fata. shi da Ma'isha dei kamar an tsaga Kara kamaninsu take, Kamar yedda Ma'isha da Y'ar uwarta Ma'ina sukeda mugun kamanni wanda ko iyayensu basa banbantasu se wajen sutura da d'abi'u sabida anan kam sunyi hanun Riga.

Faruq koh bai tseya wata wataba dirkowa yayi tawindow ya haye katanga yaceci ransa sabida kowa yasan halin Alhaji Sambo Maidugu yakan iya d'aure mutum akan Tagwayen nan nasa Ma'isha dakuma Ma'ina. 'Abba kayi hakuri Saurayi nane sunansa Faruq' Tafad'a cikin sanyin murya.
Tsinketa da mari yayi zuciyarsa natafasa da bakin ciki dakuma danasanin barin Ma'isha dayayi tazauna a Irin wannan babban gidan ita kad'ei har nasahon shekara goma, domin tunda take karama shekaranta goma tadawo nan gidan tana rayuwa ita kad'ei se masu kula da ita dakuma masu aiki.
"Ki tattara kayanki yanzun nan ba se anjuma ba kizo mutafi gida domin daga yau na yanke shawara zamanki a wannan gidan takare". Alhaji Sambo yafad'a ransa a6ace yakai layin securities d'insa awaya inda yagayyatosu gidan Ma'isha domin azo atattara kayan Ma'isha akai Alhaji Sambo's residence dake unguwan Maitama Abuja.

Ma'isha kuwa kuka take sosai, idanuwarta suna zuba tamkar ambaliya. Yana furta zancen barin gida hawayen suka tseya chak!! Nan ta'ke tamanta da marinda yayi mata ta rud'e tamkar ankawo mata tsakon mutuwa 'Abba bazan iya rayuwa awanchan gidan ba kayimin afuwa' tafad'a guiwowinta a kasa tana hawaye 'Abba I'm sorry bazan iyaba.
Ma'isha yau in mutuwa zakiyi sedei kimutu amma zakibar gidan nan kuma idan kasheki Ma'ina zatayi gwara kawai kifara salati domin ayau zaki koma gida d'aya da Y'ar uwarki Ma'ina sannan kisani kafin inbar Nigeria tsena deideita tsakaninku, Sabida matsalar ma daga gareki take wanda tun kina 'kankanuwa kika d'aura mata kiyayyarda ko a tarihi babu wanda yata6ajin hakan....

Azuciya Ma'isha ke tunanin hanyarda zatabi abar wannan zancen nakomawa gidan Alhaji Sambo Maidugu domin abayyane yake kuma kowa yasan cewa bazata ta6a had'a gida tareda Ma'ina ba, Abba ma dei tasuniyar gizo da kokinsa kawai yakeyi....

❤❤❤❤❤❤❤❤❤
Beef pie, sausage, Fried brown rice, chicken Sos, coconut juice, Almond, rice berries, fish pie, fresh fruit drink dakuma traditional Maiduguri Amala. 'Finally mun kamalla girke girkenda muketa famanyi tunda safe Alhmdulillah 🙏 '. Ma'ina tafad'a cikin farin ciki yayinda tayi tsalle sukayi tapi da Stephine (ma'aikaciyar gidan) Madam munyi kokarifa yau idan Oga yadawo dole seya bamu Maki Dari bisa Dari a wannan girkin tamu.

Washe hakori Ma'ina tayi "Sosai ma, aiko yau Daddy tseya bamu maki 100+ kan wannan girkin. Wata mata ce fara kalar larabawa tashige kitchen d'in ta tsamesu 'Ma'ina dear zoki shirya Abbanki zai iso nanda minti goma. 'Momy minti goma kuma? shi da yace tun karfe sha biyu dedei zai sauka daga jirgi' Ta amsa cikin shugwa6a. Murmusawa umma tayi sannan takama hannun ta suka wuce D'aki, Yayinda ma'aikatan gidan masu uniform suka tattara abincin Abba duk aka shiryamasa a babbar parlorn sa dake Sama.

***
Gida ne kantameme cikeda kayan zamani dakuma kayan mo're rayuwa iri daban daban, Inda Hajiya Safeenah Sambo tareda Y'arta Ma'ina Sambo Maidugu kad'ei suke rayuwa aciki, Sunada ma'aikata bila adadin yawansu. Kuma duk shigarsu iri d'aya wanda kan nuna cewa ma'aikata ne nagidan Alhaji Sambo Maidugu.
Kasancewar zaman kad'eicinda Ma'ina keyi yasa tasaba sosai da ma'aikatan, duk suka had'u suka zama abokan juna, Ako yaushe Burinta shine Suhad'a kai ita da Y'ar uwarta MA'ISHA suzauna gida d'aya kuma suyi rayuwa Irin yadda kowa ke 'yin rayuwa da Y'an uwansa a gida gwanin sha'awa. Sedei tanada tabaccin cewa hakan bazata ta6a faruwaba domin ko da mafarki tayi, Asubahin farko zata tashi tayi Sadaqa...

ASALINSU; FLASHBACK
❤❤❤❤❤❤❤❤

Alhaji Sambo Maidugu dakuma Alhaji Saminu Maidugu Tagwaye ne wajen Malam Isma'il da Hajiya Fadimah...
Sambo da Saminu sun taso su kad'ei Malam Isma'il ya mallaka domin aranarda sukazo duniya ranar mahaifiyarsu tabar Duniya. Sun tashi cikin talauci da yunwa.....

********
Iya abunda yasawwaka ayau kenan😪 Dama hausawa sunce laifin dad'i karewa. Kubiyomu a TAGWAYE part 2 domin jin cigaban labarin.

Vote and Comments pls ❤❤❤

KEEP FOLLOWING PLEASE
❤❤❤❤❤❤❤

Tagwaye (Identical twins) Where stories live. Discover now