24

19 1 0
                                    


✨ *ZAHARADDEEN* ✨

          
                   By

       *Hijjartabdoul*

               24.

*****Suna zaune su dukan su a madaidaicin parlourn gidan ga haske tar tar ko ina sai satin gida su Dalha da Halima ke yi, Halima duk kitchen ɗin gidan ya fi burgeta, ta ringa buɗe cupboards ɗin tana rufewa. Su shiga su fita ruwa a tsaitsaye suka samu suka sha tsabar zumudin sabon gida ɗaki kuwa sai da suka kusan faɗa wannan yace wannan yake itama tace wannan take so, daƙyar Maryam ta raba faɗan akan ita tayi haƙuri ta barshi ya zaɓa tukunna tunda shine ƙarami. Daada de shikam waje ya samu daga compound ɗin gidan kan ɗan tudu ya zauna, kawai dakon jiran Ɗalhat yake, sai de har aka sha ruwa babu shi babu labarin sa, dan ordern abincin ma da ya musu daga restaurant wani ya bawa yace ya shiga da shi, ba shi ne yaga Ɗalhat ba har sai goma na dare. Ɗalhat kuwa yana sane yaƙi zuwa sai da aka sha ruwa ya je restaurant ya ci abinci ya koma gida yayi wanka sannan ya tafi tarawi daga nan suka yi karatun su sai goma sannan ya nufo gidan.

Sosai ya ji gaban sa na faɗuwa, yana fargabar yarda zai ɗauki lamarin nasj shi da Maryam. A hankali ya tura gate ɗin ya shiga, sai hayaniyar Halima da Ɗalha kawai kake ji, kamar wa su ƙananan yara. Sallama yayi a parlourn tare da buɗewa ya shigo, akan carpet ya tarar da Daada da sai yanzu ne Mama ta matsa masa akan ya ci wani abu, gobe ma fa azumi za su tashi da shi. Sallamar da Ɗalhat yayi ne yasa shi ɗagowa ya kalle shi, be samu damar amsa masa ba, sai Mama ce ta amsa masa, yayin da su Ɗalha dake gefe wurin dining ɗin da ba'a sa ba suka shimfiɗa abin sallah suka zauna suna hayaniyar su. Jin da suka masa ne yasa su rugawa da gudu suka zo wajen su, yayin da Maryam kawai ta tsaya tana kallan su cike da burgewa tana murmushi. Itama ta  sowa tayi ta zauna a kusa da ɗan uwan ta, ya tankwashe irin zaman cin tuwo.

"Ina jin ka".

Cewar Daada da ya haɗa girar sama da ta ƙasa. Sunkuyar da kan sa Ɗalhat yayi.

Yace, "Daada banzo da niyyar cutar da ku ba. Hasalima na zo ne domin ta kai na. Domin rayuwata ta inganta Daada".

Sai ya share hawayen da ya zubo masa, ya ɗago ya kalle shi, suka haɗa ido.

Yace, "Kamar yarda ka sani, sunana Ɗalhat. Ni da Maryam kuma ƴaƴa ne ga Alhaji. Madaki".

Zabura Daada yayi yana tashi tsaye, yana kallan sa cike da wani irin shock na mamaki, ita kan ta Mama tsayawa tayi tana kallan sa ita da Maryam ɗin. Sunkuyar da kan sa Ɗalhat yayi.

Yace, "Kuyi haƙuri da ɓoye muku da nayi, nayi ne ba dan komai ba sai domin ba za'a taɓa yarda da cewar ni ɗan sa ne ba, a duk sanda na so na bayya na maku hakan nakan kasa, sannan kuma na ji irin furucin da Daada yayi akan sa. Shi yasa ma na kasa sanar da ku ainahin su waye mu".

"Yanzu me yasa ka sanar da mu?

"Na sanar da ku ne saboda auren Maryam da za'a zo nema, na sanar da ku ne kada kuyi zargin wani abu daban, bana so duk wani abu ya ƙara haɗa ni da wancan gidan har sai Allah yasa na cimma abinda na fito nema".

"Me ka fito nema?

Daada ya sake tambayar sa batare da ya zauna ba.

"Na fito nemawa rayuwa ƴan ci da kuma dogaro da kai".

Shiru yayi ya ɗago ya kalli Daada yace, "Dan Allah ka zauna".

Ba musu Daada ya nemi kan kujera ya zauna. Yayin da Ɗalhat ya fara bashi labari su, su waye.

"mun ta so  cikin gata, kulawa, taraiya, jin daɗin more rayuwa babu wanda bamu samu ba. Duk wani da muka yi dai-dai ne, mun ta so inda babu kwaɓa bare ƙyara da hana mu. Abu ɗaya aka nuna mana akai shine muyi karatu, wannan karatun shima ba wai dan kammu aka umarce mu da muyi ba sai dan kan sa, sai dan ya gina kan sa da kan sa, bamu ba. Duk wani abu da ya san zai kawo masa cigaba a rayuwar sa shi yake yi, da muka so muma duk wani abu da yace muyi shi muke yi, munyi karatu ba dare ba rana, ban aiki tuƙuru domin mun faranta masa rai. Mun yi manakisa, mun yi zagwon ƙasa duk a domin kasuwancinsa yayi sama, duk da cewar yayi fice a Nigeria da wajen ta amma a kullum so yake burin sa ya cika, a kullum so yake yi ya fi kowa".

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now