Abin da wanda ya ji wani ciwon a Jikinsa Zai Ce Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Ka sanya hannunka a wajen da yake maka ciwo a jikinka, ka ce; بِسْمِ اللهِ (ثَلاثاً) Bismil-lah (3) Da sunan Allah (nake neman waraka). (Sau uku). Sannan ka ce; أَعُوذُ بِاللهِ وَقُدْرَتِهِ مِنْ شَرِّ مَا أَجِدُ وَأُحَاذِرُ. (سبع) A'oozu billahi waqudratih min sharri ma ajidu wa-ohazir. (7). Ina neman tsari da Allah da kuma ikonsa daga sharrin abin da nake ji (na ciwo) kuma nake jin tsoronsa. (sau bakwai).
YOU ARE READING
HISNUL MUSLIM
General FictionLittafin Hisnul Muslim, Addi'o'i da suka dace da Sunnar Annabi. FALALAR ZIKIRI Allah Madaukakin Sarki ya ce: Fazkuriniy Azkurkum Washkuruliy Wala Takfuruni. Ku ambace ni zan ambace ku, ku gode mini kada ku butulce mini" [Bakara, aya ta 152]. Ya'ay...