ADDU'AR CIN ABINCI 31

180 4 0
                                    

Addu'a Idan Abin Hawan Mutum Ya yi tuntube; بِسْمِ اللهِ، bismillah. Da Sunan Allah.

Addu'ar Cin Abinci Idan mutum zai ci abinci sai ya ce; بِسْمِ اللهِ. Bismi l-lahi. Da sunan Allah Idan ya manta to sai ya ce (yayin da ya tuna) بِسْمِ اللهِ فِي أَوَّلِهِ وَآخِرِهِ. Bismi l-lahi fi awwalihi wa akhirihi. Da sunan Allah a farkonsa da karshensa. Wanda Allah ya azurta shi da abinci ya ci, to ya ce; اللّهُمَّ بارِكْ لَنَا فِيهِ وَأَطْعِمْنا خَيْراً مِنْهُ. Allahumma barik lana feehi wa-at'imna khayran minh. Ya Allah! Ka sanya mana albarka a cikinsa, kuma Ka ciyar da mu wanda ya fi shi alheri. Wanda kuma Allah ya azurta shi da madara ya sha, to ya ce; اللّهُمَّ بارِكْ لَنَا فِيهِ وَزِدْنا مِنْهُ. Allahumma barik lana feehi wazidna minh. Ya Allah! Ka sanya mana albarka a cikinta, kuma Ka kara mana ita (madarar).

Addu'a a Bayan an Gama Cin Abinci اَلْحَمْدُ للهِ الَّذِي أَطْعَمَنِي هَذَا وَرَزَقَنِيهِ مِنْ غَيْرِ حَوْلٍ مِنِّي وَلاَ قُوَّةٍ. Alhamdu lillahil-lazee at'amanee haza warazaqaneehi min ghayri hawlin minnee wala kuwwah. Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, wanda Ya ciyar da ni wannan (abinci) Ya azurta ni da shi, ba tare da wata dabara ko karfi daga gare ni ba. الْحَمْدُ ِللهِ حَمْداً كَثِيراً طَيِّباً مُبَارَكاً فِيهِ، غَيْرَ مَكْفِيٍّ وَلاَ مُوَدَّعٍ وَلاَ مُسْتَغْنىً عَنْهُ رَبُّنَا . Alhamdu lillahi hamdan katheeran tayyiban mubarakan feeh, ghayra makfiyyin wala muwadda'in, wala mustaghnan 'anhu rabbuna. Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, yabo mai yawa, kyakkyawa, kuma abin sanya albarka a cikinsa, (Allah) wanda ba a dauke masa azurta bayinsa, kuma ba a rabuwa das hi (a bar nema daga wurinsa), kuma ba a wadatuwa ga barinsa; shi ne Ubangijinmu.

Addu'ar Bako Ga Wanda Ya Gayyace Shi Cin Abinci اَللَّهُمَّ بَارِكْ لَهُمْ فِيمَا رَزَقْتَهُمْ، وَاغْفِرْ لَهُمْ وَارْحَمْهُمْ. Allahumma barik lahum feema razaqtahum, waghfir lahum warhamhum. Ya Allah! Ka albarkance su a cikin abin da Ka azurta su das hi, kuma Ka gafarta musu, Ka ji kansu.

Addu'a ga wanda Ya Shayar Da Mutum, Ko Ya Nufi Haka اَللَّهُمَّ أَطْعِمْ مَنْ أَطْعَمَنِي، وَاسْقِ مَنْ سَقَانِي. Allahumma at'im man at'amanee wasqi man sakanee. Ya Allah! Ka ciyar da wanda ya ciyar da ni, Ka shayar da wanda ya shayar da ni.

HISNUL MUSLIM Where stories live. Discover now