ADDU'AR TAFIYA 51

747 5 0
                                    

Addu'ar Tafiya: اَللهُ أكْبَرْ، اَللهُ أكْبَرْ، اَللهُ أكْبَرْ، سُبْحَانَ الَّذِي سَخَّرَ لَنَا هَذَا وَمَا كُنَّا لَهُ مُقْرِنِينَ، وَإِنَّا إِلَى رَبِّنَا لَمُنْقَلِبُونَ، اَللَّهُمَّ إِنَّا نَسْأَلُكَ فِي سَفَرِنَا هَذَا الْبِرَّ وَالتَّقْوَى، وَمِنَ الْعَمَلِ مَا تَرْضَى، اَللَّهُمَّ هَوِّنْ عَلَيْنَا سَفَرَنَا هَذَا وَاطْوِ عَنَّا بُعْدَهُ، اَللَّهُمَّ أَنْتَ الصَّاحِبُ فِي السَّفَرِ، وَالْخَلِيفَةُ فِي اْلأَهْلِ، اَللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُبِكَ مِنْ وَعْثَاءِ السَّفَرِ، وَكَآبَةِ الْمَنْظَرِ، وَسُوءِ الْمُنْقَلَبِ فِي الْمَالِ وَاْلأَهْلِ. Allahu akbar, Allahu akbar, Allahu akbar, subhanal-lazee sakhkhara lana haza wama kunna lahu mukrineen, wa-inna ila rabbina lamunkaliboon, allahumma inna nas-aluka fee safarina haza albirra wattakwa, waminal-'amali ma tarda, allahumma hawwin 'alayna safarana haza, watwi 'anna bu'dah, allahumma antas-sahibu fis-safar, walkhaleefatu fil-ahl, allahumma innee a'oothu bika min wa'tha-is-safar, waka-abatil-manzar, wasoo-il-munkalabi fil-mali wal-ahl. Allah ne Mafi girma, Allah ne Mafi girma, Allah ne Mafi girma tsarki ya tabbata ga (Ubangiji)) wanda ya hore mana wannan (abin hawa); ba mu kasance masu ikon sarrafa shi ba. Hakika mu masu komawa ne zuwa ga Ubangijinmu. Ya Allah! Muna rokon Ka Nagarta da tsoron Allah a cikin wannan tafiya ta mu, da kuma aiki wanda Kake yarda da shi. Ya Allah! Ka saukake mana wannan tafiya ta mu, kuma ka nade mana nisanta. Ya Allah! Kai ne ma'abocinmu a cikin wannan tafiya, kuma Halifanmu a cikin iyalanmu. Ya Allah! Ina neman tsari da Kai daga wahalar tafiya, da abin gani mai sanya bacin rai, da kuma komawa mummuna ga iyali da dukiya. Idan ya dawo daga tafiyar tasa, sai ya fadi wannan addu'a kuma ya kara da cewa; آيِبُونَ تَائِبونَ عَابِدُونَ لِرَبِّنَا حَامِدُونَ. Ayiboona, ta-iboona, 'abidoona, lirabbina hamidoon. Mu masu komawa ne, masu tuba, masu bauta, kuma masu godiya ne ga Ubangijinmu.

HISNUL MUSLIM Where stories live. Discover now