ADDU'AR SHIGA BAN ƊAki 4

189 8 0
                                    

Addu'ar Shiga Bandaki.
(بِسْمِ اللهِ)اللّهُـمَّ إِنِّـي أَعُـوذُ بِـكَ مِـنَ الْخُـبْثِ وَالْخَبائِثِ.
(Bismil-lah) allahumma innee a'u'zu bika minal-khubthi wal-khaba-ith.

Addu'ar Fita Daga Bandaki.
غُفْرَانَكَ.
Ghufranak. Ya Allah! Gafararka (na ke nema)

Zikiri yayin fara Alwala.
بِسْمِ اللهِ.
Bismil-lahi.

Zikiri Bayan Gama Alwala.
أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَـهَ إِلاّ اللهُ وَحْدَهُ لا شَريـكَ لَـهُ وَأَشْهَدُ أَنَّ مُحَمّـداً عَبْـدُهُ وَرَسـولُـهُ.
Ashhadu an la ilaha illal-lahu wahdahu la shareeka lah, wa-ashhadu anna Muhammadan abduhu warasooluh.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai, babu abokin tarayya a tare da shi; kuma ina shaidawa cewa Muhammadu bawansa ne. kuma
اَللَّهُـمَّ اجْعَلْنِـي مِنَ التَّـوّابِينَ وَاجْعَـلْنِي مِنَ الْمُتَطَهِّـرِينَ.
. Allahummaj-alnee minat-tawwabeena waj'alnee minal-mutatahhireen. Ya Allah! Ka sanya ni a cikin masu yawan tuba, kuma ka sanya ni a cikin masu tsarkaka.
15. سُبْحَـانَكَ اللّهُـمَّ وَبِحَمْدِكَ أَشْهَـدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ أَسْتَغْفِرُكَ وَأَتُوبُ إِلَـيْكَ
Subhanakal-lahumma wabihamdika ashhadu an la ilaha illa anta astaghfiruka wa-atoobu ilayka. Tsarki ya tabbata gare Ka ya Allah tare da yabo gare Ka. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, ina neman gafarka kuma ina tuba gareKa.

Zikiri Yayin Fita Daga Gida.
بِسْمِ اللهِ ، تَوَكَّلْـتُ عَلَى اللهِ وَلاَ حَوْلَ وَلاَ قُـوَّةَ إِلاَّ.
Bismil-lah, tawakkaltu alal-lah, wala hawla wala kuwwata illa billah. Da sunan Allah (nake fita), na dogara ga Allah, kuma babu dabara, babu karfi sai da Allah.
اللّهُـمَّ إِنِّـي أَعـوذُ بِكَ أَنْ أَضِـلَّ أَوْ أُضَـلَّ ، أَوْ أَزِلَّ أَوْ أُزَلَّ ، أَوْ أَظْلِـمَ أَوْ أَُظْلَـمَ ، أَوْ أَجْهَلَ أَوْ يُـجْهَلَ عَلَـيّ.
Allahumma innee a'uzu bika an adilla aw udalla, aw azilla aw ozall, aw azlima aw uzlama, aw ajhala aw yujhala alayya. Ya Allah! Ina neman tsarinka daga na bata ko a batar da ni, ko na zame ko a zamar dani, ko na yi zalunci ko a zalunce ni, ko na yi wauta ko a yi mini wauta.

Zikiri Yayin Shiga Gida. بِسْـمِ اللهِ وَلَجْنَـا، وَبِسْـمِ اللهِ خَـرَجْنَـا، وَعَلَـى رَبِّنَـا تَوَكَّلْـنَا . Bismil-lahi walajna, wabismil-lahi kharajna, wa'ala rabbina tawakkalna.
Da sunan Allah muka shiga, kuma da sunansa muka fita kuma ga Allah kadai, Ubangijinmu, muka dogara.

HISNUL MUSLIM Where stories live. Discover now