ADDU'AR TA'AZIYYA 28

1.1K 4 0
                                    

Addu'ar Ta'aziyya إِنَّ ِللهِ مَا أَخَذَ، وَلَهُ مَا أَعْطَى، وَكُلُّ شَيْءٍ عِنْدَهُ بِأَجَلٍ مُسَمَّى.فَلْتَصْبِرْ وَلْتَحْتَسِبْ. Inna lillahi ma akhaz, walahu ma a'ta, wakullu shayin 'indahu bi-ajalin musamma…faltasbir waltahtasib. Hakika abin da Allah ya dauka nasa ne, kuma abin day a bayar das hi ma nasa ne, kuma kowane abu a wurinsa yana da ajali abin Ambato… sai ta yi hakuri ta nemi lada (na hakurin rashin da tayi) أَعْظَمَ اللهُ أَجْرَكَ، وَأَحْسَنَ عَزَاءَكَ، وَغَفَرَ لِمَيِّتِكَ. A'zamal-lahu ajrak, wa-ahsana 'azaak, waghafara limayyitik.Allah ya girmama ladanka, ya kyautata hakurinka a kan abin da ka rasa, ya gafarta wa mamacinka.

Addu'a Yayin Shigar Da Mamaci Kabari بِسْمِ اللهِ وَعَلَى سُنَّةِ رَسُولِ اللهِ. Bismil-lahi wa'ala sunnati rasoolil-lah. Da sunan Allah, kuma a kan sunnar Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Addu'a Bayan an Binne Mamaci Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance idan aka gama binne mamaci, sai ya ce; "Ku nema wa dan uwanku gafara, kuma ku roka masa tabbatuwa, domin yanzu ne ake masa tambayar kabari". اَللَّهُمَّ اغْفِرْ لَهُ اللَّهُمَّ ثَبِّتْهُ. Allahumma ghfir lahu, Allahumma tahbbithu Ya Allah! Ka gafarta masa. Ya Allah! Ka ba shi tabbata.

Addu'ar Ziyarar Makabarta. اَلسَّلامُ عَلَيْكُمْ أَهْلَ الدِّيَارِ مِنَ المؤْمِنِينَ وَالْمُسْلِمِينَ، وَإِنّا إِنْ شَاءَ اللهُ بِكُمْ لاَحِقُونَ، وَيَرْحَمُ اللهُ الْمُسْتَقْدِمِينَ مِنَّا وَالْمُسْتَأْخِرِينَ أَسْأَلُ اللهَ لَنَا وَلَكُمْ الْعَافِيَةَ. Assalamu 'alaykum ahlad-diyari minal-mu'mineena walmuslimeen, wa-inna in shaal-lahu bikum lahikoon,{wa yarhamu l-lahu-l- mustaqdimina minna wa-l-musta'khrina} nas-alul-laha lana walakumul-'afiyah. Aminci ya tabbata a gare ku, ya ku ma'abota wadannan gidaje daga muminai da musulmi, kuma mu in Allah ya so masu riskuwa ne da ku. Kuma Allah ya ji kan wadanda suka gabata daga cikinmu da wadanda suka yi saura. Ina rokon Allah aminci daga bala'i gare mu da gare ku.

HISNUL MUSLIM Where stories live. Discover now