ADDU'AR GA MARA LFY 23

449 4 0
                                    

Addu'a Ga Mara Lafiya Idan Aka Ziyarce Shi: Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance idan ya ziyarci mara lafiya sai yace masa; لاَ بَأْسَ طَهُورٌ إِنْ شَاءَ اللهُ . La ba'asa tahoorun in sha'al-lah. Ba komai, tsarkaka ce in Allah ya yarda. أَسْأَلُ اللهَ الْعَظِيمُ، رَبَّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ أَنْ يَشْفِيكَ .(سبع مرات) Asalul-lahal-'azeem rabbal-'arshil-'azeem an yashfeek (7). Ina rokon Allah mai girma, Ubangijin Al'arshi mai girma, ya warkar da kai. (sau bakwa). Manzon Allah, tsira da aminci su tabbata a gare shi, ya ce; "Babu wani bawa Musulmi da zai ziyarci mara lafiya wanda ajalinsa bai riga ya zo ba, sannan ya fadi wannan (addu'a) sau bakwai face ya sami lafiya".

Falalar Da Ke cikin Ziyarar Mara Lafiya. Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yace; "Idan mutum ya ziyarci dan uwansa Musulmi (da ba shi da lafiya) to yana tafiya ne cikin lambunan aljanna yana tsinkar 'ya'yan itaciyarsu, idan ya zauna sai rahama ta lullube shi. Idan da safe ne Mala'iku dubu sba'in za su yi ta yi masa salati har ya shiga maraice. Idan kuma da maraice ne mala'iku dubu saba'in za su yi ta yi masa salati har ya wayi gari.

51-Addu'ar Mara lafiya da ya yanke kuna daga rayuwa. أَللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي وَارْحَمْنِي وَأَلْحِقْنِي بِالرَّفِيقِ اْلأَعْلَى. Allahummagh-fir lee, warhamnee wa-alhiknee birrafeekil-a'la. Ya Allah! Ka gafarata mini, Ka ji kai na, kuma Ka riskar da ni da abokin zama mafi daukaka. Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yayin da ajali ya zo masa, sai ya rika sanya hannayensa a cikin ruwa yana shafa fuskarsa da su yana cewa; لاَ إِلَهَ إِلاَّ الله، إِنَّ لِلْمَوْتِ لَسَكَرَاتٍ. La ilaha illal-lah, inna lilmawti lasakaratin. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; hakika mutuwa tana da magagi mai dimautawa. لاَ إِلَهَ إلاَّ اللَّهُ وَاللَّهُ أَكْبَرْ، لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ، لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَلاَ حَوْلَ وَلاَ قُوَّةَ إِلاَّ بِاللهِ. La ilaha illal-lah, wallahu akbar, la ilaha illal-lahu wahdah, la ilaha illal-lahu wahdah, la shareeka lah, la ilaha illal-lahu lahul-mulku walahul-hamd, la ilaha illal-lah, wala hawla wala quwwata illa billah. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Allah ne Mafi girma. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai. Babu abin bautawa da gaskiya sai >Allah, Shi kadai, babu abokin tarayya a gare Shi. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, mulki da yabo nasa ne. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma babu dabara, babu karfi sai da Allah.

Abin Da Ake Lakkana wa wanda ya Kusa Mutuwa Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Wanda maganarsa ta karshe ta kasance: لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّه. La ilaha illal-lah.

HISNUL MUSLIM Where stories live. Discover now