GOBE NA (My Future)

Por KhadeejaCandy

142K 16.8K 5.7K

Babu mace da zata labarta yadda wata macen take ji har sai ta taba kasancewa a cikin halin da wacan macen ta... Más

00
GN-01
GN-2
GN-3
GN-4
GN-5
GN-06
GN-07
GN-08
GN-09
GN-10
GN-11
GN-12
GN-13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52
53
54
55
56
57
58
59
60
61
63
64

62

2.6K 357 106
Por KhadeejaCandy

Sai da ya fito daga wankan sannan na shaga, da sabulu kawai nai wankan domin babu soso a ciki sabulun ma ba irin na mu na Nigeria ba ne, bayan na gama na daura karamij tawul din har na nufo kofa na fito sai kuma wata zuciyar tace min kara dai na maida tufafim jikina kar na fita da wannan guntun tawul ai da kunya.
  Ina kokarin daukar kayan na saka sai jin nai an yaye labulen bandakin daman ba kofa ba ce bandakin na glass ne sai lalulen da aka saka dan kare wanda yake wankan.

“Ba ki gama ba ne”

Ya fada yana kallona tun daga saman kaina har kasan kafafuwana. Tsaye nai da kayan ka kasa sakawa na kasa ajewa na kasa fitowa wata irin kunya mai tsanani ta rufe ni. Sai da ya hade yawu sannan yai murmushi ya juya yana fadin.

“Fito ki saka tufafin ki, ni ba wani abu zan miki ba”

Kallon jikina nai tawul din karami ne sosai ta yadda idan na duka za a iya ganina idan kuma ban rike shi da kyau ba zai iya subuce min ya fadi. A haka na daure na fito ganin babu wata mafita na nufi gurin akwaitina da zimmar na fito da doguwar riga na saka, sai jin mutum nai a bayana ya dora hannayensa saman kafadata yana sharce min ruwan da ke kai bakinsa saitin kunnena ya rada min.

“Ki daina jin kunyata, ni mijinki ne kuma zaki wahalar da kanki ne kawai, ni kaina ina da kunyar amman akan halila gaskiya babu wannan ina sakewa nai yadda nake so, ni da ke abu daya ne a yanzu”

Ya karasa tare da tsosa kunnena, wani yarrrr na ji rabon da na ji irin haka har na manta, kamar wacce aka daurewa baki haka na zama da kansa yaja hannuna zuwa gaban akwatinsa ya bude ya dauko wani mai mai kamshi ya zuba a hannunsa ya fara shafa min kamar nai magana sai kuma a kasa, haka ya ji ko'ina na jikina ya shafa min man har a cikin yatsun kafata, sannan ya fara kokarin kwantar da ni saman gadon a nan kam Allah ya bani ikon magana

“Ban yi sallah ba”

Bakin da nai magana da shi ya kurawa ido gaba daya idanuwansa sun canja kana kallonsa kasan natsuwarsa ta dade da barin jikinsa, can kuma ya kalli cikin idona sai kuma ya sake kallon bakina tare da kai hannunsa ya taba lisp din a hankali sannan ya sake ni ya juya ya nufi bandaki, ni kuma na mike tsaye daidai ina gyara tawul din dake kokarim subucewa gaba daya, kamar an koroshi haka ya dawo da gudu ya rika ni ya fara kissing din bakina yana wani irin haki yana shafani kamar wanda aka ce za a raba da ransa idan be sumbance ni ba.
Ban san iya lokacin da mu ka dauka a haka ba, tun muna tsaye har tsayin ya gagara muka kwanta saman gadon, wanda hakan ya bashi damar kai hannunsa a kirjina yai wasa da shi yadda ransa yake so. Sai da aka soma kwankwasa kofar sannan ya daga ni da sauri ya nufi kofar sai dai be bude ba sai ya tsaya daga jikin kofar.

“Waye?”

Ya fada yana cizon lisp dinsa tare da aje numfashi a hankali.

“Kai fa nake jira tun dazun”

“Hajiya gani nan zuwa yanzu please I'm sorry”

Ya fada yana maida numfashi sai da ya tabbatar ta tafi sannan sake nufo ni yana murmushi.

“Na manta Hajiya na jirana idan na fita zance ke kika tsayar da ni a nan”

Bance masa komai ba nai kasa da idona, wannan karon kafafuwansa biyu ya raba ya kai bakinsa gurin hancina sai da ya tsotse shi tasss sannan ya dagani ya fara kokarin cire tufafin jikinsa. Juyaawa nai na bashi baya tare da yan Bedsheet din na rufe jikina, ina jin sautin dariyarsa da kuma maganganun da yake fada na rashin kunya har ya shige bandanki, nima dan murmushin nai ina lumshe ido, ni kaina a yau wani shauki ya ziyarce ni wanda na manta rabon da na ji irinsa, wata irin natsuwa da annashuwa suka sauko min, na kasa daina murmushi har ya gama wankan ya fito, ya sake shiryawa cikin wasu riga da wandon ya fesa turare sannan ya kwanto bayana yai kissing din gefen wuyana yasa hannunsa ya kama hannuna yatsunsa cikin nawa.

“Ki yi bachi ki more”

Juyowa nai da sauri da zimmar nai masa magana sai bakina ya gogi nasa numfashina ya gauraya da nasa, babu abunda yake kallo sai bakin nawa.

“Talk”

Ya fada bakinsa na gugar nawa, a dole nima a haka nai masa magana bakina da nasa na gogar juna.

“Ina son naje nima ai”

“So kike mu je can mu taru mu lalace? No za ki tsaya a nan ki huta kamar yadda Hajiya tace idan sun ba ni gado bayan kin huta zan aiko a dauke ki, kuma zan siyo miki sabon line da zaki rika amfani da shi a nan so that ki kira Mama ki sanar mata mun iso”

Ya karasa tare da kissing dina sannan ya daga ni ya nufi akwatinsa ya rufe ya dauki abubuwan bukata ya saka aljihu,sai kuma ya sake nufo ni da kansa ya dago ni ya rumgume ni ya sake kissing dina sannan ya fita tana dago min hannu. Da kallo na bishi har ya fice ina mamakin hali da dabi'unsa idan aka fada maka Ahmad zai iya zanzarewa yai haka saka rantse da Allah karya ne kace ba zai aikata ba, ni a rayuwata ma ban taba auren namiji marar kunya kamar Ahmad ba, shi komai nasa kirkiri yake kuma da gasken gaskiya to wa ma zai ganshi yace shi aka kawo jinya?
Fitarsa da kamar minti bakwai aka kwankwasa kofar dakin
Tashi nai jikina nata kamshin turarensa na dauki rigata na saka sannan naje na bude, wata farar mace na gani dauke da tray din abinci ta miko min, sai na rufe dakin na juyo na dawo, burger burger and snacks sai drink da safafen kwai, ban kula abinba na nufi bandaki da murmushin daya kasa bari kumatuna, wanka nai sannan nai alwala na fito har lokacin murmushi nake ina jin wani irin shaukin kaunarsa a raina. Haka na bi na rama ko wace sallah sannan bude abunda aka kawo na ci wanda zan iya ci na bi lafiyar gado na kwanta bachi son raina nai ta bachi kamar dan ni kadai akai bachin.

Ban farka ba sai kusan la'asar shima kuma bugun kofar dakin ne ya tashe ni wannan karon wata makar mace ce mai zubin yarbawa ta kawo min tuwo da miyar taushe ga namomi a ciki na yi mamaki sosai ashe a acan ma ana samun irin abincin mu, sai da muka gaisa da ita na karba tana tambayar daga wani garin na zo nan.

“Gasau Zamfara”

Sai ta amsa min da ta san garin sannan tai min sallama ta tafi, duk da ban ji kiran sallah ba dana duba agogona ya nuna min hudu har da wani abu a lokacin, hanzarin shiga bandakin nai na yi alwala ya fito nai sallah sannan na ci abincin na koshi na sha ruwa na sake bin lafiyar gado na kwanta na cigaba da bachina.
Dana auna lokacin magariba yayi sai na tashi nai sallah sannan na jira isha'i itama nai, ina ta jiran Ahmad ya aiko a dauke ni be aiko ba har dare ya soma misalin tara matar nan ta sake kwamkwaso dakina ta kawo min doya da miya, ina ci ina lumshe ido domin doyar ta yi laushi sosai ga dan zaki zaki kana aji kadan wata kila sun saka madara ne dan alamu ya nuna haka yadda doyar tai fari.

  ‘To fa komai a nan banza ne, ko a nigeria da rayuwa take da tsada ai wasu na kan yi doya da madara da miya balle a nan da komai yake banza’

Na fada a raina ina ta kara auna doyar da miyar kifi, bayan na gama cin abincin ina kokarin kwantawa sai na ji an buga kofar, da kuzarina na nufi kofar ya bude, sai nai arba da Hajiya tana sanye da riga da wando sai karuwar rigar sanyin data dora sama kamar ba ita da dankwalin da tai rolling kanta da shi har da su gilas, kasa nai da kaina na gaisheta ta amsa min tana cire madubin idon sannan na bata hanya ta shigo ciki.

“Za mu je da ke can gurin Gwarzo ne”

“Jikin nasa da sauki ko?”

“Da sauki sosai ba su dai ba su dai babu wani result ba amman kana ganinsa ai kasan da sauki kan dan yace ya daina jin komai yanxu, ina jin dai har da addu'ar nan da muka hada masa da rubutu, kin san wani lokacin iska ma suna haka fa”

“Haka ne Hajiya Allah ya kara lafiya”

“Amin ki saka rigar sanyinki mu tafi”

Na mike na dauko rigar sanyin da Ahmad ya saka min na dora saman doguwar rigata sannan na dauki mayafin abayar na rufe kaina muka fita tare da Hajiya. Taxi muka shiga amman kamar wandanda suke a cikin motar gida haka muke a cikin taxin, ni kam bana aikim komai sai kallo ashe garin ya fi kyau da dare ko'ina haske ne ga mayan allunan talla kala kala har da na jaruman india.

“Halimatu?”

Hajiya ta kirani sai ya amsa a hankali na juyo na kalleta.

“Zan tunatar da ke wani abu ban sani ba ko kin sani ko kuma kina kan hanyar sani ne, mijinki yana da kishi sosai, dole sai kin yi hakuri da shi ta wani bangaren kuma ki yi kokarin kare masa mutuncinsa, mijinki yana son girmamawa, ya fada min cewar yana kaunarki kuma yana matukar tausayinki, ki yi kokari ki kare martabarki karki bari kaunarki da tausayinki da ke zuciyarsa ya gushe, sannan kuma mijinki yana da fushi sosai ba duk abu ne yake bata masa rai ba, amman idan ransa ya bace baya sauraren kowa har sai ya sauko, amman kuma baya riko daga fushin nasa ya sauka shikenan za ki ga komai ya wuce, ki yi ta hakuri da shi wani lokacin yana da wuyar mu'amala duk da na lura yana sonki sosai, sai dai kasancewar ki bazawara zai saka ki ga ya miki wasu abubuwan da za ki ga kamar yana kyamarki ko baya son ki, sai dai na san idan kika yi hakuri komai zai wuce, kanwarsa ma na nan Siyama, duk da tana da girma amman bata da hankali da natsuwa na magana da mu'alama wani lokacin, ita ma sai kin yi hakuri da ita, ni kaina da nake mahaifiyarsa sai kin yi hakuri da ni, nima wani lokacin ina da tawa matsalar kin san kuma duk wanda yace zo mu zauna to yace zo mu saba ne dole wata rana sai an samu rashin jituwa a zamantakewa, ina fada miki wannan ne sabod bana fatar wani abu ya hada da Mijinki har ya kai ga kun rabu Allah ya tsare, ina fatar ki zama matarsa ta har abada, matar da mutuwa ce kawai zata raba ku, ina matukar jindadin yadda nake ganinki ke da mijinki, sai nake jin kamar be tana aure ba sai a yanzu ne zan yi suruka”

Na natsu sosai na saurari each and every word da ya fito daga bakinta, a lokacin daya na ji hawaye na cika idona, a yau Hajiya ta yi min abunda wata uwar mijin bata taba min ba, ta nuna min lallai ƴa ta dauke ni.

“Kada Allah ya nuna min ranar da zan yi miki wani abu na bacin rai Hajiya”

“Amin”

Ya miko min line.

“Gashi yace a baki, na sa ne ki yi amfani da shi kamin a samo miki na ki”

Na karbi line ina dubawa sannan na ciro wayata na bude na cire dayan line na saka nasa. Katuwar asibiti ce mai kama da ma'aikata da dare ne amman ko'ina na gurin kamar rana, gata fes an gyara ko'ina kamar ka kwanta. Ni dai bana aikin komai sai rabon ido ina bin Hajiya sai jin nai an kamo hannuna ta baya a hankali da sauri na waigo sai na ganshi cikin rigar asibitin mai blue yai min alama da nai shiru sannan ya saki hannun nawa yai hanzari ya cin ma Hajiyarsa ya sha gabanta.

“Hajiya ga ni nan fa”

Tsaya tai tana masa kallon mamaki.

“Miye haka zaka fito daga dakinka kana a matsayin marar lafiya?”

“To ai na ji sauki Hajiya zaman daki ni kadai ba dadi”

“Allah ya kyauta ni zan koma na kwanta na gaji sosai”

Har ya juya sai ya rumgume ta yana mata godiya.

“Ya kamata kam tunda kika zo baki runtsa ba Allah ya biyaki”

“Amin Allah ya maka albarka ya baka lafiya”

Ya fada tana murmushi sannan nima tai min sallama ta juya daga ni har shi binta mu kai da kallo sai ta fice gaba daya sannan ya sake kamo hannuna ni ko na kalli jama'ar dake kai da kawo a wajen ina jin kunya.

“Ke nan ba ruwan kowa da kowa”

Ya fada yana nuna min wani dake rike da hannun matarsa, sai na dan matsa kusa da shi ina kallonsa uniform din sun masa kyau ya saje a cikinsu kamar wani bature cike da kulawa na ce

“Ya jikin ka?”

“Na ji sauki”

“Amman likitocin ba su fitar da result din ba haka Hajiya tace”

“Sun fito da result mana”

Na kara kallonsa da sauri.

“Da gaske?”

“Eh”

“Me suka ce?”

Sai ya kawo kunnensa kusa da nawa ya rada min.

“Sun ce wai ina da ciki ........”

Ban san lokacin da dariya ta subuce min ba haka na bude baki kamar mahaukaciya na fara dariya babu kakkautawa kowa sai kallona yake, shi ma dariyar yai ya rumgume cike da farinciki ya saka kaina a kirjinsa ya rungume ni tsantsan.

“I love you”

Daga dariya na koma hawayen da ban san na me bane jindadi ko akasin haka? Ban sani ba ko abunda Ahmad yake min zai daure ban sani ba ko rayuwarmu zata cigaba da tafiya a haka ko kuma na dan lokaci ne, amman tabbas shine kalar mijin da na dade ina mafarki, mai sani dariya da nishadi a kowane lokaci, mijin da zan kallo na yi farinciki na jidadin ina aurensa mijin da zan kalla ya burge ni wanda iya yai kwalliya zan ji nishadi a raina, mai kula da ni mai damuwa da matsalata mai tausayina kuma mijin da yan'uwansa za su kaunarce ni mahaifiyarsa ta dauke ni kamar yarta ashe wannan ranar zata zo? Allah kasa wannan farincikin nawa mai daurewa ne. A zuci nai maganar a fili kuma sai na sauke numfashi a hankali ma dago muka gada ido naja hancinsa ina murmushi, sai wani abu yai min da fuska kamar da gaske ya ji zafi.
Yana rumgume da ni muka shiga dakinsa da aka tanadar masa, gadon asibitin ba daya ba ne da iirin namu na naija kirarsa da fadinsa ba daya ba ne, komai an tanada a adakin sai wani dumi kake ji gwanin dadi kamar ba a asibiti ba, da kansa ya zaunar da ni saman gadon sannan ya zauna yaja ni zuwa jikinsa ya rumgume can kuma ya ji kamar rumgumar bata masa ba sai ya kai hannu ya cire rigar sanyin da ke jikina.

“Tun dazun kina nan cikin raina sai mamarinki nake”

Ya fada yana sauke min numshinsa a fuska, ni kuma na lumshe ido ina sauraren sakwannin da yake aika min, da na ji abun na kokarin wuce gona da iri ne yasa na tashi tsaye.

“Ina ganin ya kamata ka kwanta saboda na huta”

Kallona yai da wasu rikitaccin idonsa sai nai saurim kawarda fuskarta na zauna saman kujerar da ke kusa da gadon.

“Ke yanzu na miki kama da wanda zai kwanta yai bachi? Taso mu kwanta”

Ya taso ya janyo hannuna, duk yadda na so na ki kwana a saman gadon hakan be samu ba, domin ba aminta ba ni da shi muka kwanta saman gadon a tare, aiko bachin da be yi ba kenan sai kusan daya na dare, ni kam tun ina jin hannunsa na kai sako a jikina har bachi yai gaba da ni.
Ko da na farka sai ganina nai ni kadai a akan gadon ya lullube ni da Bedsheet shi kuma yana saman kujerar zaune yana tasbihi da yar carbin nan da ake makalawa a hannu. Saurin zabura nai mike zaune sai ya sakar min murmushi.

“Good morning”

Sauka nai saman gadon ya nuna min bandaki na shiga, na juya kan fanfon ya na ji zafi dayan bangaren kuma sanyi, sai da na kira shi ya zo da kansa ya hada min sanyi da zafi sannan nai wanka na fito na sallah a kan carpet din dana gani a gurin, ban maida under Wears dina ba domin sun lalace sai na saka abayar kawai nai sallah.

“Me kike son ki ci?”

“Duk abunda zaka ci”

“Ni ke kin ishe ni ai ba sai na ci wani abu ba”

Na yi kasa da kaina sai yai murmushi ya miko min hannunsa.

“Fada min mana sai na saka miki order”

“Zan samu irin abincin jiya?”

“Uhmmmm amman ba ki tunanin cin wani abun dabam, ai kin ga nigeria kika baro, ya kamata ace kin dandana abincin su na nan, da safe ma rasa nai mi zance a baki shiyasa nace su kawo miki burger da snacks, da rana kuma nai miki order irin naki”

Na zauna saman kafafuwansa kamar yadda ya bukata sannan yasa hannayensa na zagaye wuyansa da su.

“Ashe ana samun abincin nigeria a nan”

“Eh amman akwai tsada sosai”

“Zo muje wani restaurant din mu ci abinci a can”

Ya fada yana wasa da yatsun hannuna.

“Za su bari ka fita?”

“Eh mana kayan gida zan saka sai mu tafi”

Haka kuwa akai ya saka tufafinsa wando da riga ya dora rigar sanyi sama nima ya saka min tawa sannan ya rika hannuna muka fita tare, taxi muka shiga shi ya fadi inda zamu je mai taxin na sauke mu ya ciro kudin kasar ya mika masa sannan ya maida wallet dinsa muka nufi wata hotel wacce ba tai girman wacce muka sauka da farko ba. Sai da ya biya komai ya nuna id dinsa sannan suka ba mu makullin daki, wannan dakin be yi girma da haduwar wacan dakin ba, a nan ya kira wata number da hausa ma naji yana magana da matar sannan ya fada mata ta kawo mana tuwo da miyar taushe zai aiko mata da address din inda yake ta waya sannan ya bukaci ta sake kaiwa a inda ta kai jiya, number dakin daya fada ne yasa na gane Hajiya za a kaiwa.
Sai da ya gama tashi wayar sannan na saka number Mama na kirata muka gaisa har take shaida min a can yanzu karfe uku da rabi ne na asuba sabanin nan da yanzu tafiyar ta waye ma. Hakan yasa nace karta tashi kowa ta bari idan rana ta yi sai na kira ta mu gaisa da su Namra, da kansa ya bukaci na bashi ya gaisa da Mama tai masa ya jiki sannan sukai sallama.
Sai da muka ci abincin muka koshi sai labari ya canja, ashe a cin abincin kadai muka zo har da daukar wani sabon karatu mai darasi mabanbanta, tun yana yi ina hanawa har na gano da gaske yake a dole kyale shi da abunda yake halalinsa, ko wace kusurwa ta jikina sai da Ahmad ya isar mata da sako, ko wane bangare na jiki inda jini da jijiya ke aiki sai da yasan da zaman Ahmad a wannan safiyar, ba ma kamar bakina da kirji domin numshina har wani nisan zango yake ya dawo, at first nima na mori abun kuma na taimaka masa yadda ya dace domin ni kaina nayi marmarin rayuwar, kamin mai aiko sakon ya iso da kansa.

Waya aike ki? Miyasa kika yi? Waya ce ki aminta tun yanzu? Shine abunda nai ta mamaitawa akaina, kusan ko a lokacin da nake budurwa ba ji azabar da naji a yau ba, wata kila saboda abunda na sha ne ko kuma saboda na hadu da Gwarzo namiji ne, wanda ya dade be hadu da abunda ko wane lafiyayen namiji yake muradi ba kamar yadda ya fada min a cikin abunda ba zan iya jiransa da yana maye ba ko kuma bachi balle na ce mafarki, a zahirin yai ta sakarmin wasu kalaman da sun fi karfin hankalina da tunani balle har na haddace su, da gasken gasken hawaye na ke da idanuwa na azaba, kamar an saka wuka an yanke gurin haka naji, wani zugi na tashin hankali ke fitar min har kasan kafafuwana, jinin da ya zubar min har tsoro na ji a zatona wani abu na gurin ne ya samu matsala babu abunda na tuno sai maganar Hajara cewar na shirya dan sai na fadi wanda ya aike ni lallai kuwa yau zan fada. Unkura nai na tashi amman na kasa sai naji kamar an zare min lakka a jiki.

“Sannu”

Ya fada yana shafa fuskata kamin ya sumbace ni, sai kuma yanjo ni jikinsa ya rumgume, saukar hawayensa na ji a cikin gashin kaina hakan yasa na dago da sauri na kalleshi sai ga fuskarsa da murmushi idonsa a lumshe sai wani abu yake da baki kamar wanda ya ci yaji. Maida kaina nai jikinsa na kwantarda kaina.

“Da gaske ke bazarawa ce Lims? Da gaske ke kika haifi su Namra? Ko cs akai miki aka cire su? No wait da gaske kamin ni akwai namijin da yai mu'alama da ke?”

Na yi shiru na lafe a kirjinsa kamar ba ni. Sai ya soma shafa bayana.

“You're beyond my expectations, ban san abunda zan fada miki ba ban san kalmomin da zan hada na furta miki ki gansu ba, amman lims when i say kin hadu ina nufin haduwa makura iyakar kurewa, i just can't believe kin taba aure Wallahi balle ace kin haihu, ke din ta musamman ce”

Ya fada kissing my hand, sannan ya dago ni daga kirjinsa ya kurawa fuskata ido sai kuma ya sake rumgume ni sosai yana sauke ajiyar zuciya.

“Idan zan yi ma Allah godiya sai na rasa da wace kalmar zan yi amfani, ta ina zan fara gode masa? Al-hamdulillah thumma Al-hamdulillah”

Ya furta yana kara lullube min jikina da Bedsheet din da muke rufe ni da shi.

“Ya kamata mu koma asibiti kar Hajiya ta zo bata same mu ba”

“A a sai mun gaji tukuna”

Ya fada yana kara rumgume sai kokarin komawa ruwa yake da sauri na bar jikina ina jin kamar zan fashe da kuka.

“Mum gaji da Wallahi”

“Kin gaji dai ke”

Ya fada with smile on his face, sannan ya sauka saman gadon ya nufi bandaki.

“Bari na ga kan toilet din na hada miki ruwa”

Ba mu bar hotel din ba sai kusan la'asar a nan mu kai azahar da la'asar sannan muka koma asibiti, babu kalar albarka da be saka min ba babu irin godiyar da be min ba, each and every 30 minutes sai ya tambaye ni wai daman haka zauwara su ke? Shi ko yan matan da yake aure be taba arba da wacce ya samu abunda yake so a gurinta ba kamar yadda ya samu a gurina, har fada yake wai lallai mata suna suka tara.
Da muka dawo cikin asibitin tafiya kawai nake ina daure ina nuna kamar babu komai amman ni na san akwai komai ba irin na safiyar wacan daren amarci nawa dana kasa tafiya daidai ba ne, wannan kam ina tafiya sai dai ina jin azaba sosai da sosai.
  Tun da Ahmad ya girma a nan sai yai wayo kusan kowace safiya sai mun tafi hotel din da sunan karyawa a can kuma bama dawowa sai dare, tun ina jin nauyin kar Hajiya ta gane har na barwa Allah domin na lura ko sau daya bata taba tambayar ko a waya yana ina ba? Ko kuma tace daga ina muka dawo idan mum tararda ita a asibiti, sai dai shi ne ma zai ce yau guri kaza mukaje na ga gari, alhalin ba gaskiya ba ne, idan na kalleshi sai ya kanne min ido daya ko ya daga min gira.
  Satin mu daya a asibitin sannan suka sallame shi bayan sun yi bincike iya binciken su ba su gano komai ba, sai dai hakan be hana su dora shi akan magani ba, tare da wasu shawarwari ciki har da motsa jiki wanda suka ce yana da kyau ga lafiya.

Washe garin ranar da suka sallameshi ne muka kamo hanyar Nigerian cikin farinciki da kaunar juna, Hajiya kam tun kam mu dawo ta sanarwa kowa cewar danta ya samu lafiya, a raina nace ni kam ai na fi kowa sanin ya samu lafiya kam, ba mu bar kasar ba sai da Ahmad ya dauke mu ni da ita muka shiga wani shagon siyerda kayan sakawa da na ado muka siyo sannan muka shiga na yara na siyoma su Namra da Amal teddy Adnan da Aiman kuma mashin din wasar yara da wani madubi mai canja kala, Inna muka na siyo mata turare ita da Mama.
Sai a lokacin na gane ashe kayan mu na nan sun fi nasu na can arha domin duk abunda muka siya idan Ahmad ya fada min kudinsa a kudin Nigeria sai na jinjina abun.
Karfe 2:00pm daidai jirginmu ya sauka a Abuja babban birnin taraiyar kasa FCT. 







_____________

Fatar kun yi sallah lafiya Allah ya maimaita mana 😍🙏
  

Seguir leyendo

También te gustarán

53.6K 7.2K 67
Original Title Saving the Tragic Adonis •Associated Names 拯救美强惨反派[穿书] •Type Web Novel (CN) •Genre Comedy School Life Shounen Ai Slice of Life •Author...
345K 18.8K 56
A Love Story ( Own Characters ) ဘုဏ်းဇေယျာကျော်xရှင်းသန့်တည်ကြည် " မင်းသားလေး...မင်း ငါ့အပေါ် သိပ်သဘောကောင်းတာပဲ၊ ငါ့မေမေကပြောတယ်၊ အသက်ကြီးလို့ လက်ထ...
151K 16.7K 122
💥New BL ဒါဒါတို့ရေ... ရှေးခတ်ကျေးလက်တောရွာကို ကူးပြောင်းမှ ကြိုက်ပါတယ်ဆိုတဲ့ဒါဒါလေးတို့အတွက် အသစ်လေးလာပါပြီ .... ရှားပါးတဲ့ MC Gong ပါနော် Gp လေးက...
27.7K 3.9K 42
Love Crossing Sheikh lovely daughter with mafia badass King, how comes destiny and passionate met