GOBE NA (My Future)

By KhadeejaCandy

142K 16.8K 5.7K

Babu mace da zata labarta yadda wata macen take ji har sai ta taba kasancewa a cikin halin da wacan macen ta... More

00
GN-01
GN-2
GN-3
GN-4
GN-5
GN-06
GN-07
GN-08
GN-09
GN-10
GN-11
GN-12
GN-13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52
54
55
56
57
58
59
60
61
62
63
64

53

2.4K 333 262
By KhadeejaCandy


ABDALLAH POV.

Misalin tara da yan mintuna ya shigo gurin Hajiyarsa kana kallonsa kasan yana cikin damuwa. Yayyen Hajiya ya tarar a falon wato Hajiya Altine da Hajiya Rukaiya, sai da ya gaishe su sannan ya wuce dakin mahaifiyarsa, yadda ya same ta zaune saman carpet rike da carbe fuskarta da damuwa sai ya kara jefashi a cikin nasa damuwar. Kusa da ita ya zauna bakin gado yana kallonta da Fuskarsa da ke bayyana damuwarsa karara.

“Hajiya barka da dare”

Ta dago ta kalleshi kana ganin idonta ka san ta sha kuka.

“Barka dai Husaini, ya aikin”

“Alhamdulillah, Hajiya ki rage saka kanki a damuwa, In-Sha-Allah za a ga Abdulhamid”

“To Allah yasa ni abun yanzu har tsoro yake ba ni, jikina yayi sanyi sosai, idan na duba sai na rasa abunda Abdulhamid zai yi wa wani da zai cutar da shi mutumen da magana ma bata sha masa kai ba, Allah yasa ba yan fillar kai ya hadu da su ba, domin na san masu neman kudi fansa da su suka kama shi da yanzu sun kira sun fadi abunda suke bukata”

Jimmmm Abdallah yai kamin ya kalleta a natse ya ce.

“Hajiya zaki iya tuna lokacin da akai yi Halima fyade?”

“Na sani”

“Mutumen da yai mata fyade wani kirista ne, kuma abokin Abdulhamid ne, ban san miya kai shi gidan ba har yai ma Halima fyade, a yanzu kuma ina kyautata zaton kamar da sa hannunsa gurin dauke Abdulhamid”

Cikin tashin hankali Hajiya ta kalleshi.

“Kamar kai ya akai ka sani?”

“Halima ta fada min mutumen ya dawo yana sonta, saboda cikin da tai shi kuma haihuwa yake nema, bata aminta da shi ba amman ya dage yana son ta aure shi, shiyasa na fada mata gaskiyar cewar shi yai mata fyade, sai dai ita bata san yana da alaka da Abdulhamid ba, ni kai dai na sani nima kuma saboda na taba ganinsu tare har hotuna sun yi tare, shi mutumen police”

“To me zai saka ya dauke Hassan?”

“Saboda ni na fadawa Abdulhamid gaskiyar daya kasa yarda da Halima a lokacin da abun ya same ta, ke da shi kuna ganin kamar ta aikata zina ne, yayi ta bakinciki yana fadar cewar shi Abraham zai ciwa amana, wata kila yai masa magana ko yai masa wata barazana shi kuma Abraham din ya dauke shi”

“Amman miyasa baka fadi wannan ba? Sai yan sanda su bincike shi mutunen?”

“Hajiya idan baka iya kama barawo ba, sai barawo ya kama ka, shi Abraham din police ne kuma da na bincika sai na samu labarin cewar baya cikin garin nan a office dinsa ma har an saka wani, amman mu saurara na kwana biyu tukuna tun da mun kai report din gurin Police kuma ana Addu'a, ko minene zai bayyana In-Sha-Allah”

“Amman irin wannan ai kama shi za ayi a bincike shi ko kuma ita Halimar, waya sani ko ma ita ta saka shi ya sace shi saboda ta dauki fansa balle ta ji zai yi aure, kuma ta ga shi Abraham din yan sonta”

“Haba Hajiya wane irin Halima kuma?”

“Zata iya yin komai wannan yarinyar da kake gani, ni sam ban yarda da ita ba ma”

“Babu hannunta a cikin nan, kuma na fada miki ki bari nan da kwana biyu idan ba mu ga wani abun ba, sai mu fada musu wanda muke zargi”

“To ko ma dai minene Allah ya bayyana shi”

“Amin”

Yayi kusan awa daya a dakin sannan yai mata sallama ya fice. Aiko kamar fitarsa take jira ta fito falo ta labartawa yan'uwanta abunda ya faru dukansu sun cika da mamaki.

“Wannan maganar ai ba abar a kyale ba ce”

Cewar Hajiya Altine, sai Hajiya ta amsa ta tana ware hannu.

“Ni ma shi na gani ban zafafa abun ba ne saboda a gabansa ne, na san zai iya shiga cikin lamarin tun da uwarsa ta shigo ciki, yadda kika san ta wanke gaba ta zuba masa ya shanye haka yake da ita, ko sunanta baya son a ambata a wani abu”

Hajiya Rukaiyah ta dora da.

“To waya sani, ko wani abun tai masa, amman duk yadda akai ta san inda Abdulhamid yake”

“Nima shi nake tunani, saboda bakinciki zai yi aure gashi ita ba tai ba zai iya sawa tace shi mutunen ya sace shi, ko kashe shi ma zasu iya yi, ko kuma su masa wani illar, kuma Allah kadai yasan gaskiyar lamarin nan wata kila ma daman can ta san abokinsa nw ta aure shi dan su kashe shi su ci dukiya Allah ba basu sa'a ba, Allah ya gani ko da akai auren nan ba zan ce miki yaron nan yana son Halimatu ba, be taba nuna min ba, kuma a lokacin ma ta neman lafiyarsa yake amman sai ya zo min da maganar aure daga sama, ban san yadda akai ta janyo hankalinsa ba ma, kamar abun magani, cikin kankanen lokaci akai komai”

“Kin san abunda za ayi? Ko yanzu ita ya kamata a kama, idan ta ji wuya dole ta fadi inda shi Abraham din yake da Abdulhamid din, wannan ai ba maganar bari ba ce”

Cewar Hajiya Altine tana tabe baki alamun mamaki ya gama cikata.

“To yanzu a kira Yusuf a fada masa, gobe tun da farar safiya a doka masu sammako a kamo yar iskar, yarinya ta same mana fitina a cikin dangi”

Hajiya ta fada tana kara yamutsa fuska. Hajiya Altine ta ce.

“Haka za ayi, daman Yusuf din ya fada min ai akwai inda suke saka mutum su saka masa wata hula duk iskancinsa sai ya fadi abunda yake gaskiya, bari na kira shi....”

Ta karasa tana danna number dan nata rai a bace, Hajiya kuma ta zauna saman cushion tana ta rawa da kafa tana kara kashe ido, babu komai a zuciyarta sai tsanar Halimatu.

HALIMATU POV.

Na iso gida cikin wani yanayi da ban taba samu kaina ba, ni dai ba zan ce ina son Ahmad ba, haka kuma bana kin shi, sai dai a yau kalamansa sun kashe min jiki sosai.
Mama ta yi mamakin ganin na dawo gida da wuri bayan a a lokacin na saba dawowa ba sai yamma, karya nai mata na ce mata yau babu aiki da yawa shiyasa aka tashemu. Har na yi kamar na labarta mata abunda ya faru da Abdulhamid sai kuma wata zuciyar ta hana ni, domin na san ita ma din zata zargi Ahmad da saka a ka masu kamar yadda nima zuciyata take zargi, kuma zata iya cewa zatai wa Hajiya jaje gudun kar ace bata ji ba idan taje kuma dole zata bada labarin abunda na fada mata ne, idan kuwa Hajiya ta ji haka zata zarge ni, so rufin asirina kawai nai shiru da bakina na bar abun a cikina, har sai ya bayyana.
Babu irin tunanin da ban yi ba a ranar har cikin daya ina abu daya, dan son gano abunda Abdulhamid da Abraham suke aikata marar kyau, idan na saka wannan na kwance wacan na kulla wannan, sata yake? Tare da Abraham din suke fashi? Ko kuma wata sana'ar ce dabam? Duk wani mugun aiki da zan kwatanta Abdulhamid da shi sai na ga kamar ba zai iya aikatawa ba, wata kila ma dai Abraham din shari yai masa saboda kar ya cutu shi kadai, domin ko a lokacin da na ke aurensa ban ga wata alama da ta nuna rashin gaskiya a tare da shi ba, duk da yake baka iya gane gaskiyar mutum mai boyo, Abdulhamid kuma yana daga ciki irin mutanen nan da suke boye abu, soyayyar da muka da shi ma a lokacin da nake budurwa a boye muka yi saboda baya son kowa ya sani.
Haka dai nai ta sakesake na har dare raba ban yi bachi ba, domin tun ina jin alamar bachi bachin a idona har ya fitar min gaba daya, tashi nai na fito bakin balcony na zauna ima ta kallon taurari kamar mai kidayarsu, babu komai a tare da ni sai tunani kala kala. Can ciki ciki na ji wayata dake kan drawer tana vibration alamar kira yana shigowa wayata. Sai na tashi na koma dakin, hannu na kai na cire carjin sannan na dauki wayar sai nai arba da number Ahmad, gabana ne ya fadi kamin mamaki ya rufe ni, miyasa ya kira ni yanzu? Abunda be tana ba, ko kirana a gida balle a wannan lokacin da agogon wayata ya nuna karfe biyu saura, to ko dai fada min zai yi an sako Abdulhamid? Ko kuma wani abun zai fada min dabam, kiran na daf da tsinkewa nai picking na kara a kunne sai dai ban yi magana ba sai da na fito balcony. Ina ta jiran yai magana be ce min komai ba, idan na duba wayar sai na ga kiran na tafiya har sai da na gaji da kaina na ce

“Hello”

“Lims, kema kin kasa bachi kamar ni kenan?”

“Eh”

“Kin san me? Dakina yai min ba dadi sai na fito na zauna harabar gida sai kidayar taurari nake, yanzu kuma haka nan kawai na ji ina bukatar jin muryarki, duk ban yi zaton za ki dauka ba”

Ya fada da murmushin da zan iya jiyowa, kana jin muryarsa ka san ransa kal yake fa farinciki. Na yi shiru ban ce masa komai ba.

“Fada min miya hanaki bachi?”

“Ni ma ban sani ba, na samu kaina da kasa bachin ne”

Murmushinsa mai sauti ne ya daki dodon kunnena.

“To je ki kwanta, so that's ki tashi da wuri i need to see early in the morning”

“Okay”

“Sweet dreams Lims, ki rufe idonki ki tuna duk wani beautiful memories we share together za ki yi bachi, kuma ina rokon ki yi mafarkina take good care of yourself for me pls”

Be jira abunda zan ce ba ya yanke wayar, for the first time na samu kaina da shiga calls list na kurawa number ido for no reason, before murmushi ya biyo fuskata, sai da na sake kallon taurarin sannan na tashi na koma daki na kwanta. Lumshe ido nai thinking all the good memories we share together kamar yadda ya fada, babu abunda na fi tunawa kamar tears din da muka share with one tissue, and location da yai maganar wai ko dai ina son sa ne? Samun kaina nai da murmushi, kamin wani lokacin bachi yai gaba da ni.
  Na farka raina Fresh har wani shauki nake ji, domin ina aiki ina yan wake wake na, ina cikin shiryarwa su Namra su tafi makaranta muka ji muryar wata mace wacce hausa bata isheta sosai ba.

“Dan Allah wacece Halima”

Zumut nai na fito ance son kira kamar bazarawa, na amsa da cewar ga ni ina kallon matan ashe ba daya bace sai dai dukansu su biyun suna sanye ne da uniform din yan sanda. Kamar jira suke na amsa suka nufo inda nake suna fadin.

“Zamu je da ke office din mu ki amsa wasu tambayoyi”

“Me nai?...”

Ban gama rufe baki ba suka rika ni muka fara ja in ja da su, da gudu Hafiza ta zo ta buge hannu police din ta hau ta da masifa.

“Mi tai muku? Haka kawai za ku shigo cikin gida mu kamata? Wace duka ta baku izinin shiga gidan mutane anyhow”

Police din ta nuna ta a fusace.

“Ke mahaukaci ki san abunda kike yi, karki ce zaki taba police zan ci mutuncinki, marar kunya kawai”

“Yes louder pls mu nan gidan sai mu kashe mutum ba komai ba ne a gurin mu, dan haka mun fiki tantiranci”

Cewar Hafiza tana zare mata ido kamar ba da police take fada ba. Sai da Mama ta daka mata tsawa sannan ta umarce da ta dauko min Hijabina.

“Amman Mama...”

Hafiza bata gama fadar abunda zata fada ba Mama ta tari numfashinta.

“Dauko mata Hijabinta na ce, duk inda za a je indai tana da gaskiya gaskiyarta zai fito da ita, Allah yana tare da mai gaskiya”

Ranta be so ba taje ta dauko min Hijabi na karba na saka, sai da muka fara tafiya sannan yarana suka fashe da kuka, ba ma kamar Amal wacce ta biyoni har kofar gida tana kiran sunana.

“Momy.....”

Ban san lokacin da hawaye ya wanke min fuska ba, ko ba komai sun tozarta ni, sun saka ni a motar police patrol, duk wanda zai gan ni a ciki dole na zargi wani laifin na aikata, duk kuwa da kasancewar ban san abunda nai ba, ga kuma mutane da suka tara mana a kofar gida, domin motar har da maza sai suka tsaya daga waje. Ina jin lokacin da Inna take tambayatar wane station ne za a kai ni sai mai tukin motar ya amsa mata da.

“State CID”

Har muka isa gurin ban daina tunanin abunda na aikata wanda zai saka ayi min wannan kamun ba ban san na yi fada da kowa ba, ban san na yi wa wani kazafi ko kage ba, ban san mi na tarewa wani ba. Abun da kamar wulakanci domin muna isa suka saka ni a cell suka rufe, ko minti biyar ban yafe ba ba na hango Inna tare da Aisha da Mama da, like ten minutes wani kanen mahaifin mu ya iso gurin tare da yayansa.
  Na yi minti talatin a ciki sannan aka fiddo ni aka nufi wani office da ni, ina shiga na samu Hajiya a zaune tare da yan'uwanta, kallo daya na yi mata na gane dalilin kamoni da akai. Mutumen da ke zaune a gabamu yana karanta min abunda ake zagina da shi dan Hajiya Altine wato yayar Hajiya, na san shi ya san ni amman a yau sai kamar be taba ganina ba.

“Ni ban san inda Abdulhamid yake ba, kuma ban san inda Abraham yake ba, nan fa cid ce babba kuma kai police ne Yusuf kai baka sani ba ni ya za ayi na sani?”

“Karki fada min maganar banza karki sake kiran sunana ki dauka ba ki taba ganina ba a rayuwarki”

Shine abunda ya fada min a tsawace, sai na kalli Hajiya na ce.

“Ba kiyayya ta shiga tsakanina da Abdulhamid ba, soyayyah ce kuma shi ya ji ba zai iya zama da ni ba ya rabu da ni, me zai saka ki yi min wannan zargin? Me nai miki Hajiya wannan maganar wace irin kiyayya ce?”

“Au baki sani ba? Munafuka, ai auren da kika masa ba na Allah bane, kin janyo hankalinsa saboda ki ci dukiyarsa tun da kin ga shi yafi dan'uwansa kudi, to shi aiki yake yana sai da motoci, dan uwansa kuma likita ne kawai, ko cikin nan Allah kadai yasan gaskiyarsa kin dauka ba zai yarda ta magana tun da kin shanye shi kamar yadda kika yi ma Abdallah, duk yadda akai da hadin bakinki aka sace min d'a, tun da kin ga zai yi aure kin ji bakinciki, wai dan har baki da kunya kike soyayya da kanensa? Kin taba ganin inda aka auri yaya kuma yana da rai a auri kane? Wato gaki autar mata ko, ban cin kin raba kansu kuma ki shiga ki mulke mu son ranki ga bayi, kin ma ci uban rainin wayo Wallahi”

Haka tai ta jera min bakaken maganganu sai abunda ta mance, jikinta har rawa yake kamar zata dake ni. Ban taba jin nadamar aikata wani abu ba kamar auren Abdulhamid a wannan lokacin, sai dai bawa be isa ya wuce kaddararsa ba.

“Za ki fada mana da arziki ko kuma sai cilasta ki?”

“Ban san komai a kai ba”

Na fada ina hawaye, bana son fadar komai saboda kar na jefa Ahmad a matsala, kuma idan Hajiya ta san ta dalilina ne zata kara zargina ne.
Haka aka raya aka kada aka juya aka na tsaya kai da fata ina fadar ni ban san komai akai ba. Daker aka bawa kanen mahaifina damar shigowa cikin office din wanda shi ma kanene ga mahaifinsu Abdallah, babu irin maganar da be yi da Hajiya ba amman ta ki saurarawa ita ala dole sai na fadi inda danta yake.

“Hajiya zumunci kike kokarin lalatawa, abunda kike yi be kamata, da uban yarinyar da mijinki uwarsu daya ubansu daya, akan me za ki yi wannan abu? Idan Alhaji yana da rai ke kin isa ko hararar zuri'arsa ki yi? Wallahi na tabbatar da ace Alhaji yana da rai yau ba za ki kwana a gidansa ba”

“To sai kaje ka taso da shi a yanzu ka saka ya sake ni, ni ba ku ga abunda tai min ba ta raba kan yayana, da gangan ta kulla soyayyah da Husaini yanzu kuma ta zo ta auri Hassan, yaro ya bata ga ayoyi tambaya akanta sai ku ce na kyaleta saboda ni ban san zafin haihuwa ba? Wallahi ko Alhaji ne a raye ba zai yarda a taba masa yayaba”

Kamar wacce take fada a ciki unguwa haka ta rika daga muryarta tana fadi abunda ranta yake so, Baba Buhari sai yai shiru kawai yana mata kallon takaici. Muna office din har la'asar, ganin na ki amsa laifina na ki na fadi komai yasa Yusuf din yace a shiga da ni wani daki, sai ya hada ni da wasu mata police suka tafi da ni wani bangare na gurin, suka shiga da ni cikin wani daki mai hudu, a yadda na fahimta abun kamar hadin baki ko ma nace cuta ce zallarta domin a iya sanina ko maza sai idan an dokesu kuma an kwana biyu ba su fadi kowa ba sannan ake saka a gurin, amman ni kamar daman can suna jira na ne. A rayuwata ban taba ganin inda aure ya zama kiyayya ba kamar nawa da ya zame min haka da Hajiya.

“Ba zaki fada ba?”

Dayar ta fada min cikin tsawa.

“Ni ban san komai ba”

Na amsa ta har lokacin zuciyata bata ayyana min na fadi komai ba. Wata hula suka saka min a saman hijabin da ke kaina, sai kuma suka cire min Hijabi suka saka min hular, wani namiji dake gafena na ga ya kunna wani abu sannan na daki hular kan nawa, a maimakon na fara bayani kamar yadda aka ce min mutane suna yi sai na nemi hankalina na rasa.


AHMAD POV.

Murmushi yake yana kurba tea dake hannunsa, ya nade kafafauwansa yana zaune gaban Hajiya, ita ma murmushin take tana fadin.

“Haka nake son mace tana da tsantsaye da rayuwa, kasan da wata ce kana bata motar nan zata hau murna ta karba jiki na rawa”

“Sosai ma Hajiya, kuma Wallahi wannan abun ya kara min kirmarta sosai a idona, sai na ji ta kara shiga raina sosai Wallahi”

“Amman ka mata magana kuwa?”

“Har ynzu dai, ki taya ni da addu'a, tana da dan taurin kai dan kadan kuma tana da wuyar sha'ani shi ma kadan, saboda tana tsoron rayuwa”

“Allah ya tabbatar da alheri yasa kuma ya karba maka”

“Amin Hajiya Amin”

Ya amsa cike da jindadi addu'ar mahaifiyarsa, sannan na aje mug din ya mike tsaye.

“Bari naje office”

“To Allah ya tsare, ka dai kusa zama babban mutum kamar da”

Murmushi yai ya fice yan shafa kansa. Driving yake zuwa office cikin nishadi da annashuwa, haka nan kawai idan ya tuna yayi waya da Lims da daren nan sai yaji wani dadi ya lullubeshi. He arrived in time just to see her face yana son yadda yake tsawa jikin windows yana hangota musamman idan zata bude windows din office dinta. Haka yai ta tsaye a gurin tun yana duba agogon ya ga nine saura har ya koma ya zauna can kuma ya taso ya tsaya ya koma ya zauna har kusan 11am abunda bata taba ba, domin duk dadewarta bata wuce 9 ko 9:30.
  A take ya ji duk ya damu, wayarsa ya dauka ya kira wayarta sai ya jita kashe, a lokacin ne ya fara tunanin ko dan abunda ya faru jiya yasa yau ta ki zuwa aiki kuma ta kashe wayarta? Sai duk yaji ya shiga damuwa, har kusan 3pm ba wani labari, line ta ya sake gwadawa, sai yai sa'a wannan karon ya shiga, kamin a dauka duk ya matsu.

“Hello Lims”

“Ba Halima ba ce kanwarta ce Hafiza, Halima tana gurin yan sanda”

“What? Miya faru?”

“Dazun suka zo suka kamata da safe, ba irin wulakanci da ba su mana ba nan gurin wai suna zarginta da hannu a batan tsohon mijinta, tana can hannunsu sun kulleta”

“What? Wane station din ne?”

“State cid office”

Kashe wayar yai ya mike tsaye cikin zafin rai da rashin natsuwa na kira lauyansa, sai da yai masa bayanin komai sannan ya fada masa cewar su hadu a can din.
@360 na isa gurin, ko motarsa kadai ka kalla kasan babban mutum ma'ana mai ji da naira balle kuma shigarsa ta suit da yai, yana shiga cikin gurin lauyansa ya iso, duk wani shiga da fita da ake ciki lauyansa ne yake magana bashi ba, suna shiga office din aka kira Hajiya ta iso tare da Hajiya Rukaiya, ba su zauna ba Abdallah ya shigo office din shima.
Ahmad na kallonsa ya watsa masa wani mugun kallo.

“Kai kasa aka kamata kenan?”

Abdallah yai kamar be ganshi ba ko inda yake zaune be kalla ba balle har ya amsa shi. Hajiya ta kalli Ahmad da kyau tace.

“Waye kai? Ko kai ne Abraham din? Ni na saka aka kamata ba shi ba”

“To kina nan zaune za a fito da ita, kuma idan akan Abdulhamid ne ni zaki saka a kama ba ita ba, nine silar kama shi da akai yi ba ita ba”

“Kai Malam karka fada mana maganar banza, idan baka san darajar iyayenka ba ni san nawa, karka ce zaka yi ma mahaifiyara rashin kunya”

Abdallah ya fada a fusace. Sai Ahmad ta tabe baki yana kallonsa.

“Kasan darajarta ka bari ta ci mutuncin wacce bata da laifi?”

“Hey my friend don't tell me rubbish”

“An fada maka who are you?”

“Ai kai za a tambaya, ka so nan kana wani nuna isa wa kake a gurin Halima? Wallahi idan na so ko kallonka Halima ba zata sake yi ba stupid human being”

“Oh really? Ni ko zan nuna maka wani abu ne a gurinta, ka jira nan da one month sai na nuna maka waye ni a gurin Halima, sai ka gane darajata ta fi taka a gurinta”

Yana fadar haka ya mike tsaye da zimmar zai fita sai ga lauyansa ya shigo yana fadin su tafi gata can an saka a mota. Ba shiri Hajiya ta mike tsaye.

“Ina Yusuf din yake? Ya za a saki yarinya bata fadi komai ba? Ni ina dana yake”

Juyowa Ahmad yai ya kalleta.

“Dan ki yana Abuja hannun DSS kije ki yi fada da su idan kin isa, and idan wani abu ya samu Halima dukanku ba zan kyale ku ba har kai”

Ya karasa yana nuna Abdallah. Abdallah ya masa wani mugun kallo.

“Look at you fool sai na nuna maka baka isa da Halima ba trust me.... ”

Ahmad be sake ce masa komai ba ya fice. Abdallah kuma ya hau rarrashin zuciyarsa domin ji yake kamar ya hau Ahmad da duka, Hajiya kan jikinta gaba daya ya gama sanyi jin Abdulhamid yana hannun DSS.

______________________

Guess what will happen next....!

Continue Reading

You'll Also Like

52K 2.8K 56
" what are you telling me bro inba mutum bace to WACECE ita who is she" dan cizon lips dinsa saal yayi " if you don't believe me come and see for you...
27.6K 3.9K 42
Love Crossing Sheikh lovely daughter with mafia badass King, how comes destiny and passionate met
284K 22K 186
Eldest Daughter Was Reborn အကြီးဆုံးသမီး Description အရင်ဘဝတွင် ကျန်းယန်ရှန့် သည် သူမ၏ သုံးစားမရသည့်ဖခင်နှင့် မိထွေးဖြစ်သူကို အရွဲ့တိုက်ပြီး ဆေးလိပ...
68.1K 7.6K 59
Daada, Ku saka mata Munawwara, ku kira ta da Madina. Watakila albarkacin sunayen biyu rayuwar da bata da zabi a kanta ta zo mata da sauki ko yaya ne...