GOBE NA (My Future)

Por KhadeejaCandy

142K 16.8K 5.7K

Babu mace da zata labarta yadda wata macen take ji har sai ta taba kasancewa a cikin halin da wacan macen ta... Más

00
GN-01
GN-2
GN-3
GN-4
GN-5
GN-06
GN-07
GN-08
GN-09
GN-10
GN-11
GN-12
GN-13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52
53
54
55
56
57
58
59
60
61
62
63
64

28

1.9K 228 31
Por KhadeejaCandy

ABDALLAH POV.

Be iya zuwa gurin aikin ba kamar yadda ya tsara zuwa tun farko, gaba daya ji yake kamar ba shi da lafiya, ji yai baya bukatar ko'ina sai gidansa. A take ya dauki hanyar gidan, a ka'idan zai shiga gidansa yana shiga da sallama kuma fuska a sake ko da kau yana cikin damuwa yana kokarin yin hakan saboda yaransa, duk damuwarsa ko wata matsala nasa baya son tana shafar iyalinsa musamman yaransa Abdallah mutum ne mai tsananin son yara ko da ba na shi ba balle kuma na shi, wannan yasa duk irin matsalar da suka samu da Suwaiba matarsa baya taba bari yaransa su gane.
  Babu kowa falon at that time, daman yara suna scul Suwaiba kuma tana dakinta, kai tsaye dakinsa ya wuce yana jin wani irin zazzabi na rufe shi, kwantawa yai saman gadonsa yai ruf da ciki ya rumtse idonsa sosai. Yana jin wayarsa na ringing ya ki ya duba mai kira ma balle yai deciding zai dauko ko a'a, ya kusan awa daya a haka sannan ya bude idonsa ya tashi zaune yana duba wayar, Abdulhamid ne ke kiransa. Sai da ya busar da iskar bakinsa sannan ya danna picking.

“Abdallah”

“Na'am”

Ya amsa yana gyaran muryar.

“Ya kuka yi da ita?”

Shiru yai for few seconds sannan ya ce.

“Tace ta fi bukatar sakin ko dan cutar da take dauke da ita”

Daga dayan bangaren Abdulhamid yai shiru kamar mai nazari har Abdallah ya dauka ko ya kashe wayar sannan yai magana.

“Idan kuma na ce bata dauke da cutar fa? Zata zauna?”

“Amman miye gaskiyar lamarin ne?”

“Maganar gaskiya bata dauke da cutar”

“Then miyasa ka ce tana dauke da ita?”

“Ina son na gane wani abu ne, kuma ina tunanin idan na ce mata haka zan ji wani abu daga gareta, amman na ga hankalinta sam be tashi ba, even i thought zata yarda ta zauna saboda tunanin idan ta fita za a kyamace ta, but then i realized idan har na cigaba da zama da ita, zan iya cutar da ita kuma ni ma zan cutu, domin har ga Allah zuciyata ta kasa natsuwa da ita, ta wani bangaren ina ganin kamar rabuwar shi ya fi alheri”

“Amman Abdulhamid miyasa za ka ce tana dauke da cutar, na kasa yarda da kai, wani lokacin sai kai ta abu kamar marar tunani”

“Idan taje wani gurin ta yi gwajin ai za a tabbatar mata idan tana dauke da cutar ko akasin haka”

“Ina fatar rabuwar ta zame muku alheri kai da ita”

Shine kawai abunda Abdallah ya fada ya kashe wayar ya kaita a goshinsa, babu abunda ke ransa sai irin halin da Halimatu zata shiga.

“What if Abdulhamid yana da lafiya? Da duk wannan zai faru? Da ko kin yi cikin ba zai gane cewar ba na shi ba ne, ni na jefaki a wannan matsalar, saboda ni ne silar wannan matsalar....”

Ya furta yana kara rumtse idonsa, kokarin da yake na kawarda damuwar abunda Halimatu ta fada masa ne, gudun kar wani abun ya same ta, and the most of all zai wanke Abdulhamid daga rikon da yai masa a zuciyarsa. Bude idonsa ya sake yi ya lalubo number Halimatu ya aika mata sako.

“Na zurfafa a son ki na sani, na nuna miki son kaina na sani, na kaurara da yawa na sani, kina da gaskiyar ki yi yarda da duk wani abu da zuciyarki ta fada miki, amman ina dada jadadda miki karki kuskura fadawa Abdulhamid wannan maganar”

After the sms ya kwanta saman gadon yana jin kamar ba shi da wani kuzari. Abubuwan da ta fada masa is painful suna ta kona masa zuciya, after like two hours ya kira wani a asibitin ya fada masa cewar ba zai sami damar zuwa ba a yau. Tun da ya kwanta babu fuskar da yake ganin sai ta Halimatu old memories yake tunawa daga lokacin da take yan mata ba tai aure ba, a lokacin duk be fara son ta ba har tai aure shi kuma ya bar kasar duk be fara son ta har ya dawo yai aure ya haifi yarsa ta fari be fara sonta ba, sai da suka hadu a family meeting a lokacin tana da aurenta har ta haifi yara uku, tun daga ranar Allah ya dora masa sonta, yanayin jikinta mu'amalarta kyauta da komai nata sai ya rike burge shi, musamman da ya samu labarin waye mijinta da irin kalubalen da take fuskanta a gidan aure sai ya fara tausayinta yana ganin kamar shi ya dace ta aura ta samu jindadi, kamar yadda yake jin cewar idan ya aureta zai iya haifar ɗa namiji tunda ita duk tana haihuwar maza da mata, and bugu da gari ga sonta da yake.
But why he fell in love with her? Sai yanzu yake ta ganin laifin kansa, he know maybe da be so duniyarta da tunaninta be bata haka ba ta bata munana masa zato ba. Har scul bus ta kawo yaransa daga makaranta yana a dakinsa kwance, yana jin hayaniyarsu amman damuwar da ke ransa ta hana shi tashi ko da zaune balle har ya fito falo.
  After yayi sallah azahar a cikin dakin Suwaiba ta shigo ta zauna kusa da sallayar tana karantar damuwar mijinta.

“Lafiya dai? Na ji ka dawo tun dazun kuma baka fito ba”

Kallonta yai yana kirkirar murmushin da yaki ya fito a kumatunsa balle har ya tsaga bakinsa, a kokarinsa na boye mata damuwarsa ya kirkiro mata wasa.

“Ba fushi kike da ni ba”

“Wannan dabam, kana cikin damuwa ga idonka nan ya nuna”

“Bana jindadi ne, dazun da na fita sai da nai amai shiyasa na dawo”

“Ka sha magani?”

Hannunta ya kama.

“Ina likita har ake tambayar na sha magani?”

“Na kawo maka abinci?”

“No ba yanzu ba”

Kamin ta sake cewa wani abun su Inteesar suka shigo dakin ita da kanwat suka fado jikinsa. Sai Suwaiba ta rika kokarin daga su.

“Kyale su tafiyarki”

Ya fada yana shafa kansu, tashi tai ta fice tana musu fada wai kar su dami Daddynsu ba shi da lafiya duk kuwa rashin gamsuwar da tai na cewa ba shi da lafiya din da gaske.
   Sama sama ya tambaye scul sannan ya ciro wayarsa ya cire mata key ya mika musu su game so that su kyale shi ya samu natsuwa, a gurin ya kwanta su kuma suka tashi suka bar dakin suna murya Daddy ya ba su iPhone dinsa su yi game.
  Har yanzu jikinsa ya kasa sakewa yana ta jin kansa kamar marar lafiya irin wanda ya dade kwance yana jinya, tsakanin fitar su Inteesar da kwantarwarsa be wuce 40 minutes ba Suwaiba shigo dakin rike da wayarsa fuskarta a jagule.

“Abdallah miye haka?”

Saurin bude ido yai jin muryarta kamar mai shirin yin kuka, sakon da ya aikawa Halimatu ne dazun take nuna masa, tuni kwalla sun cika idonta. Tashi yai zaune yana kallon fuskarta, gaba daya sai abun ya kara jagule masa shi ya manta ba be goge ba, and ko da ma be goge ba why zata karbi wayarsa a hannun yara ta masa bincike?

“A lokacin da nai zargi cewa kai ban yi daidai ba, yanzu miye haka? Yar'uwarka kuma matar dan'uwanka Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un....”

Hannu ya kai ya rikota ya zaunar da ita bakin gadon sannan shi ma ya tashi daga kan tile din da yake ya zauna bakin gado ya rike hannayenta.

“Babu alakar komai a tsakaninmu”

“To wannan wane irin sako ne? Miye ma'anarsa? Na kasa gane wace irin alaka ce a tsakaninku? Idan nai zargi ka ce min ba haka ba, Abdallah da me na rage ka?”

“Ba ki rage ni da komai ba, idan ina wani abun da be kamata ba zaki fi kowa sani”

Fashewa tai da kuka ta runtse ido, kamar yadda shi ma ya rufe idon ya hada kansa da nata yana hawayen da be yi zaton za su sake zubo masa ba.

“Ashe ba za ki iya shaidun mijinki ba? Ba kisan abunda mijinki zai iya yi da wanda ba zai iya ba? Wani ba zai zo yace miki ga mijinki can a dakin wata karuwa ba ki karyata shi? Har yanzu ba ki san waye Abdallah ba Suwaiba?”

Bude idonsa yai yana kallon idanuwanta da ke rufe suna zubar da hawaye still goshinsa da nata suna hade guri daya.

“Me kika son nai miki ki yarda da ni? Rantsuwa kike son nai miki? Ko qur'ane kike son na dafa miki? Ko kuma Halimatun kike son na dauko miki da kanta ta fada miki?”

Kai ta girgiza ta jimke hannunsa sosai a cikin nata alamar ta yarda da shi, sai dai har yanzu kukan take mai sauti. Kansa ya daga ya janta jikinsa ya rumgume yana hade yawun bakinsa tare da saka dayan hannunsa ya share hawayensa.

“Wani lokacin wani abun yana faruwa da mu saboda yana daga cikin kaddararmu, wani na dan lokaci ne kawai na jarabawa, wani kuma har a abada zai zauna da kai”

A fili yai furucin yana sauke ajiyar zuciya, kamin ya koma zancen zuci.

‘Da ace na san zan hadu da ke Halima da ban dawo kasar nan ba, ko da na dawo da ban zauna garin nan, hakika duk wanda aka jarrabe shi da son wani an fi kowa yi masa babbar jarabawa, Allah kadai yasan abunda yake nufi da ni’

Ya kara rumgume matarsa yai ya kai bakinsa saitin kunnenta.

“Babu komai a zuciyata yanzu sai tausayin Halimatu, ki kwantar da hankalinki ki daina damuwar kanki da matsalar nan dan Allah”

“Dama kaunarta kake yi Abdallah wata kila da zan fi samu natsuwa fiye da ka fada min cewar tausayinta kake, tausayi ya fi so tsatsa a zuciya Abdallah”

“Ki daina saka kanki a cikin damuwa, Halimatu ta riga ta auri dan'uwana, ba zan taba iya aurenta ba a yanzu ko da ko Abdulhamid ya rabu da ita, duk wani abun da zan mata ko nai ma yayanta zan yi mata ne kawai dan kyautata da kuma tausayinta da na ke, Halimatu yar'uwata ce ko ba komai dole na taimaka mata ballantana akwai yan'uwanta, kuma duka familynsu babu wani mai karfi da Halimatu zata iya jingina da shi yai mata irin abunda na ke mata”

Ta gamsu da bayanansa abunda bata gamsu da shi ba, shine zancen cewa ba zai auri Halimatu ba ko da Abdulhamid ya sake ta, ko da dai hausawa suna cewa ana barin halak dan kunya, amman a yadda Abdallah yake damuwa da lamarin Halimatu abu yana daure mata kai, ta sani abun kunya a gurinsa ace dan'uwansa ya saki mata shi ya aura, dan uwan ma twins brother dinsa, amman ta kasa yarda tausayin Halimatu kawai yake ta san ba tausayi ne kawa ba har da so, wannan abun ya tsaya mata a zuciya, abun da ciwo ace kana tare da mijinka zuciyarsa tana begen wata.

HALIMATU POV.

I thought ba zan sake zubar da kwalla ba, i promise my own self ba zan sake shiga damuwar wani namiji ba, but i feel like ban kyautawa Abdallah ba, i feel like na yi kuskure na fada masa haka, miyasa ba zan bari har sai asiri ya tonu ba? Amman da na bar maganar a cikina da har yanzu zargin Abdallah yana a cikinta. And now da ba Abdallah ba ne wanene? Babu wanda zan iya zargi a iya hangena da tunanina, wata kila yan fashin ne da gaske! Amman miyasa ya shafa cikina har ya tambaya da gaske ina dauke da ciki, miyasa yace wannan karon ba gurin mijina suka zo ba? A gaban madubi nake zaune ina kallon kaina hawaye na sauko min, nazarina ya ki ya kare, tunanina ya ki ya gano komai. Ban matsa daga inda na ke ba har sai da na ji motsin motar Abdulhamid.
Bandaki na shiga na wanke fuskata na fito bakin gado na zauna.

Sai ga shi ya shigo ya zauna kusa da ni, ban kalleshi ba amman jikina ya ba ni cewar kallona yake.

“Abdallah ya fada min kin ce kin fi son sakin, ni kuma ba zan ki yi miki abunda kike so....”

Yana fadar hakan ya saka hannunsa aljihu ya dauko takardu guda biyu ya miko min.

“Ina miki albishir din cewar ba ki dauke da cutar hiv na fada miki haka ne kawai saboda na ga reaction dinki”

Hannu na saka na karba at first na yi zaton ko takardar gwajince sai nai arba da abunda ya kusan raba zuciyata gida biyu.

_Ni Abdulhamid na saki matata Halimatu saki daya a yau_

Bayan rubutun saki sai kuma na kwanan wata a kasa, Wallahi na yi zaton kukan a lokacin amman sai na nemi shi na rasa babu ko alamunsa a tare da ni, a dayar takadar kuma cheque din kudi ne dubu dari biyar.

“Wannan na minene?”

“In case of....”

Ya amsa min muryarsa na rawa. Sai na girgiza masa kai ya dora cheque din a saman gadon.

“Bana da bukata”

Ina furta hakan na nufi wardrobe dina na bude na dauko akwaiti na fara zuba kayana, abubuwan da ya kamata ace na zuba a ciki ba su na zuba sai tarkace jikina na ta rawa kamar wata marar gaskiya. Ina kokarin rufe akwatin ya zo ya rike akwatin sai na daga kai na kalleshi, hawaye fal a fuskarsa a maimakon ni da aka saka na yi kuka ban yi ba, sai shi da yai sakin yake kuka.

“Zan kula da komai, idan kina bukata za ki iya yin iddarki a nan”

“Bana da bukata”

Sai ya kada min kai kamar wani yaro da mai bashi umarni, mikewa nai tsaye na dauko hijbina sai ya rike.

“Ba za ki bari sai da dare ba?”

“Gida na ke son zuwa”

Nan ma kan ya gyada min.

“Bari na kai ki, zan saka a kwashe komai na ki a kai miki”

Ya fada yana ficewa daga dakin, ni kuma na bi bayansa rike da jakar hannuna, da kuma takardar sakin, har lokacin ban ji kuka ko wani abu makamancin kukan a tare da ni ba, sai dai zuciyata ta yi wani irin nauyi kamar dutse. Ko da na fito har ya tashi motar ya bude min front seat, ni kuma na bude back seat of a shiga na zauna, sai ya fito ya rufe front seat din ya bude gate ya fita da motar sannan ya koma ya rufe ya dawo cikin motar. Sai da yai nisa da tukun ya faka motarsa gefen titi ya jinginar da kansa jikin sitiriyarin motar ya fashe da kuka kamar karamin yaro. Kamar hadin baki sai nawa idanuwan suka cika da kwalla.

“Why? Why all this?”

Ya furta cikin sautin kuka, sai ya dago kansa ya jingina da kujerar motar, ina iya jiyo lokacin da ya sauke ajiyar zuciya ya kai hannu ya share hawayensa ya cigaba da tukin, sai da muka iso kofar gidan mu sannan ya juyo ya kalleni.

“Zan iya maida auren idan kina so”

Kai kawai na iya girgiza masa alamar a'a ma bude motar na fita, sai da na taka har bakin kofar gidan na saka kafata, sai na ji babu abunda na ke bukata sai kallon Abdulhamid. Juyowa nai na kalleshi, lokacin da ya turo da motoci aka dauke ni aka kai gidansa nake tunawa yau kuma gashi ya dawo da ni da kansa, zancen mahaifiyata na bata son a fara kirga min aure ya fado min a rai, da na san zan haka GOBENA zata kasance a gidan Abdulhamid da ban aureshi ba, ban ji ina tsanarsa ba, sai dai na nemi soyayyarsa da ke zuciya na rasa, hawaye yake kamar yadda ni ma nake yi. Hannu na saka na share hawayena duk kuwa da na san fuskata ba zata iya boye kukana ba, sannan na shiga ciki gidan, iyakar kokari na yi dan na tsayar da hawayena amman abun ya faskara haka na shiga gida ina hawaye.

Inna da Mama da Baba da Hafiza duka suna tsakar gidan zaune ko wane fuskarsa dauke da far'a da alama nishadi suke. Baba na kishingide saman tabarma Inna na tsaye jikin kofar kitchen din dake tsakar gidan, Mama kuma na zauna a saman kujerar mata kusa da Baba Hafiza ce zaune a kofar dakin Mama tana shan rake, suna ganina da yanayi sai duk jikinsu yai sanyi.
Gaban Baba naje na gurfana rike da takardar a hannuna ina hawaye na kasa daga kai na kalleshi.

“Shi aure yana da rayuwa da mutuwa kamar mutum da rayuwa, idan lokacin mutuwarsa yai babu mahani, kuma abu kalilin kan iya sakawa ya afku ko ya mutu, ko da dalili ko babu, dan haka ki sawa rayuwarki sallama ki dauka cewar ajalin aurenki a gidan Abdulhamid ne yai”

Da sauri na dago na kalleshi, jin magana mai dadi da kwantar da zuciya da samar da natsuwa daga bakinsa, tun kan na furta ya fahimci cewar aurena ya mutu. A take na share hawayena ina gyada masa kai alamar na gamsu.

“Saki nawa yai miki?”

“Daya ne Baba daya yai min”

Na furta muryata na rawa, sai Mama tai karaf ta ce.

“Amman me kika masa mi ya hada ku?”

Kamin na ce komai ba Baba ya daga mata hannu.

“Ba yanzu ba, tashi ki je ciki ki huta, Allah yai miki albarka”

Ban san lokacin da murmushi ya kubuce min ba, kaunar mahaifina ta kara cika min zuciya, ya famshe ni daga tambayar da ban san mi zan fada a matsayin amsa ba.

“Madallah da kai Baba, ina ma ko wane uba kamar kai yake? Madallah da uba irinka, madalla daka zama jigo ga Halimatu....”

Na fada ina hawaye cike da shaukin sonsa, Hafiza ce ta taso daga bakin kofar da take zaune ta zo da gudu ta rumgume Baba tana kuka tana fadin.

“Ina kaunarka Baba Allah kara maka lafiya”

Dariya yai ya tashi tureta daga jikinsa ya tashi zaune. Ni kuma na dago na shiga dakin Mama. A dare Mama bata iya hakura ba har sai da ta ji dalilin mutuwar auren, ni kuma ban boye mata komai ba cikin har da fyade da kai min da abubuwan da suka faru, sai dai ban yarda na fada mata cewar Abdallah na ke zargi ba.
Na ga rashin jindadin mutuwar auren a fuskarta, daman wace uwa ce zata zo auren yarta ya mutu? Balle Mama da take daukar abu ta saka a rai, su Salma da Hafiza ma da suke yan mata ba su yi aure ba abun ya dame ta balle kuma ji ace aure na biyu ya mutu. Sai dai duk da hakan ta nuna min zama da Abdulhamid din ba mafita ba ne sakin ya fi tunda har yana zargina. Da yamma Su Adnan suka dawo daga islamiya, ganina suka hau murna kamar wacce suka shekara ba su gani ba, ganin na kai har bayan i'shai yasa Namra ta fara tambaya wai nan zan kwana.

“ A nan zan kwana, yanzu na dawo kenan sai illla ma shaa Allahu”

Wani irin tsalle ta daka ta dire tana murna ta kama hannuna ta rike.

“Momy da gaske?”

Na gyada mata sai ta kara rumgume ni tana ta murna.

“Yeee mun huta Momy ta dawo”

Iya murnar da yata take na ganina a kusa da ita ya isa da tabbatar da cewar yarana sun yi marmarina duk kuwa da suna zuwa su ganni ko na gansu idan bukatar hakan ta kama, sai dai ko wane d'a yana bukatar mahaifiyarsa a kusa da shi, amman ni na bar su na auri Abdulhamid, a yau ya saka min da haka! Da tunanin abun na kwana a zuciyata har safe.

   Washe gari Baba ya kira ni a dakinsa ya tambaye ni abunda ya faru, a nan na tsige masa tun daga biri har wutsiya, a ganina shi mahaifina ne be kamata na boye masa komai ba. Shi ya ba ni shawarar zuwa asibiti na sake yin gwajin hiv dan tabbatarwa. Ban yi wata wata ba na shirya na tafi gurin gwajin. Ban dawo ba sai yamma domin daga asibitin na wuce gidansu kawata Hajara, a lokacin da na labarta mata mutuwar auren sai ta fashe da kuka kamar an mata mutuwa.

“Wannan wane irin abu ne yake ta bibiyarki Halimatu? Tun farko sai da na ce ki auri Abban Ikram da yanzu duk wannan abun be faru ba kika ki”

Kai na girgiza mata.

“Wallahi sai ya faru, abunda Allah ya rubuta ya samu bawa babu mahani, na yarda da wannan”

“Allah sarki Halimatu, ga ki da tauhidi ga yarda da kaddara, Allah ya yaye miki wannan abu da yake bibiyarki”

Ta fada cikin kuka ni kuma na amsa da amin. Bayan sallah magariba na koma gida, sai na tararda tsakar gidamu cike da kayana na daki, alamar Abdulhamid ya aiko min da su kenan kamar yadda yai alkawari, mama ce take labarta min cewar a gurin kawo kayan har da mahaifiyarsa wai tai ma baba bayanin komai, wata kila shi ya turo ta dan ta wanke shi kar a ga laifinsa, wata kila kum ita ta saka kanta a tunanin ba zan fada musu gaskiyar lamarin ba, mama ta fada min har da cheque din kudi ta bawa baba ya ki ya karba, hakan kuma ba karamin dadi yai min, domin bana bukatar komai na Abdulhamid a yanzu.

Da kaina na shiga na fadawa Baba result dina cewar ban daukr da shi, yayi murna matuka dai kuma ya sake ba ni shawarar zuwa wata asibitin na sake yin gwaji. Ban watsar da shawararsa ba, na tafi kusa asibiti uku ana min gwaji result na fada cewar bana dauke da cutar, daman can ni hankali na be taba tashi akan hakan ba, ko da Abdulhamid ya fada min ban ji komai a raina kuma ban san dalilin hakan ba. A dakin da na bari cikina na koma da kaya na jera komai kamar wacan karon, a nan kam gaskiya na ji babu dadi sosai domin a takure na ke duk kuwa da kasancewar gidan ubana ne amman gidan yawa ne, ba irin gidan nan ne na masu kudi ba da za a ce kowa da dakinsa.
   Ranar da na cika kwana uku da dawowa sai ga Aminu ya zo kofar gidan ya aiko da siyayya wai a bawa yaransa kuma yana kiransu, an fada min haka yake musu a yanzu duk bayan kwana biyu ko uku, ni kau na rasa dalilinsa na yin hakan bayan dacan ba haka ya saba ba. Be san ina cikin gidan ba na sani tun da ba kowa ya san aurena ya mutu ba, na san yana cikin mutunen da za su yi murna da mutuwar aurena domin ya sha fada min a lokacin da nake gidabsa cewar babu namijin da zai iya zama da ni sai shi saboda bakin halina. Fita yai da da su yai musu waya siyayyar ya hado musu da kudi sannan ya dawo da su suka shigo gida suna ta murna.
A daren mun dade muna tattaunar maganar yadda a yanzu hankalinsa ya dawo gurin yaransa, abunda ya bawa kowa mamaki a gidan mu, Mama ta karkarta min hankali da wata maganar wai ko shine mutumen da yai min fyade.

“A a mama ba Aminu ba ne, na san siffar Aminu ciki da waje, yadda yake idan ya saka tufafi kanana kaya ko manya kuma yadda yake mu'amalarsa, da shi ne da tuni zan gane, ko kadan wannan mutumen be yi min yanayi da Aminu ba, idan har shine dole zan gane, kuma me ma zai saka Aminu yai min haka, mutumen da baya kaunata, wanda ya kasa hakuri har ya dawo ya saki ni ta waya ya sake ni fa, mutumen ya wulakanta ni Mama Wallahi ko sunansa bana son ji”

“Ai saboda kiyayyar da yake miki na ke zaton haka, saboda ya jefa ki a matsala ki kasa zaman auren”

“Ko ma wanene ina rokon Allah ya bayyana min shi”

Na furta ina hawaye zuciyata cike da kuna, Mama ta amsa da amin. Mun dade muna fira a dakinta, cikin har da zancen Abdallah tana cewa da ma shi na aura ita tun farko shi ta so na aura amman na ki ni dai ban ce mata komai, saboda ban taba fada mata cewar Abdallah yayi ta neman na kashe aurena na aure shi ba....

AHMAD POV.

Tarin takardu ne a gabansa da laptop yana ta aikin cika wannan cire wannan saka wannan, aikin daya taru masa ne na satin daya shige wanda be be yi ba yake yi yau ganin yau assabar ce babu karatu.
Mug din coffee na gefensa lokaci zuwa lokaci ya ke dauka ya sha. Be tashi daga gurin ba sai da aka kira sallah azahar sannan na fito daga garden din
ya shiga part dinsa yai alwala ya nufi masallacin dake unguwar, after sun yi sallah ya shigo gida, as usual ya nufi part din Hajiya, yar aikinta kawai ya samu a falo hakan yasa ya nufi dakinta tun kan ya karasa ya jiyo muryarta ita da abokiyarta suna fira, har ya juyo da zimmar ya fasa shiga sai kuma ya juya ya shiga da zimmar ya tambaya iya Baby Namra.
  Sai da ya gaishe da abokiyar Hajiyar sannan ya kalli Hajiya ya ce.

“Hajiya ina Baby?”

“Bata nan, wannan mahaifiyar Ikilima ce, Hajiya ga danki nan ko da yake ai kin san shi”

“Na san Gwarzo ai tun ba yau ba”

Cewar matar tana dariya, shi kuma ya saci kallonsa ya sake kallon Hajiya ya ce.

“Ina taje Hajiya?”

“Gidansu kawarta Namra”

Kansa ya daga sama ya saka hannunsa ya dafe.

“Oh Hajiya kin san na ce miki kar a kaita can, matar nan ba mutunci ne da ita ba wata kila ma kallon banza zata mata, shiyasa duk bibiyar da take min ban yarda na kai ta ba”

“To ina ruwan yara da lamarinku, ta sha mun kai tana son zuwa can sai a hana ta? Su fa yarane babu ruwansu da wannan, kuma dazu ta fada min cewar Momyn kawarta ba a gidan take ba”

“Hajiya dan Allah ki aika a dauko ta, ni dai bana son abotar nan, bana son yawan fitar nan da take Wallahi”

“Zan aika amman sai da yamma, abincin ka yana part dinka”

Be sake ce mata komai ba ya juyo ya baro jikin kofar, sai a yanzu yake mamaki no wonder yau weekend kuma bata zo ta dame shi ba, da yanzu tana nan ta saka shi gaba da hana shi aikin nan tace sai su yi game ko ya fita da ita kamar yadda ya saba mata every weekend. A dayan bangaren kuma yana ta ganin karfin halin Hajiya na zon hada shi aure da bazawara dan shi dai kam ya raya a ransa ba zai taba auren bazawara ba.

“Allah kadai ya sani wata kila ma yarta bata da miji, miye na wani zuwa gidan iyayen mai son yarki a yi maganar auren da ke”

Ya fada yana kokarin zama sai jin haushi yake kamar ance masa zancen aurensu ya kawo ta.

HALIMATU POV.

   Washe gari ya kama Saturday babu scul sai islamiya, dan haka na tashi da wuri na gyarawa yarana suka tafi makaranta, har Amal a yanzu tana son zuwa islamiya duk wani kuiya da son jiki yanzu ta daina shi ganin babu ni a kusa da ita. Around 12 suka dawo daga islamiyar suka cire uniform suka saka kayan gida na zuba musu shinkafa da wake da akai a gidan, sai Amal ta murje ido ta kanne kafadarta ita sam ba zata ci wake ba, daman can na san Amal is not fan of wake da shimkafa amman na dauka ta canja ganin bana nan, a dole na tashi na dora mata indomie da kwai. Ina cikin kitchen din ta zo ta same ni ta rike rigata tana tabe baki.

“Momy za ki goyani”

Dariya yai ina mata kallon Mamaki.

“Wato kin ga Momy a banza ko? Amal kin fa girma yanzu ya kamata ki daina wani abun, yanzu ba kamar da kike ba”

Bata fuska tai tana kokarin kuka. Kanwata Salima tai dariya ta ce.

“Kin ganta nan wallahi dole sai an goyata a cikin gidan nan, ko dai Namra ta goyata ko wani a cikin gidan nan idan ba haka ba sai ta shige cikin daki tai ta kuka tana kiranki, yanzu kuma kin dawo dan haka ki yi ta goyon abarki daman can ke kika saba mata”

Dariya nai na kai hannu na dauke na dorata a bayana, ina kokarin kwance dankalin kaina na goyata da shi na ji Sallamar Baby Namra wato kawar Namra yar mutumen nan marar mutunci, da kuzarinta ta shigo da far'a har da yar ledarta a hannu. Gaba daya yan matan gidan mu suka hau yi mata oyoyo suna ta murna da zuwanta da alama dai sun saba da ita ba kamar yadda na ke tunani ba. Ita ma da far'a take ta gaishe su daya bayan daya sannan ta nufi dakin Mama inda ta san su Namra suna can.
  Ni dai ina goye da Amal ina dahuwar indomie sa gata ta shigo tare da Namra, Namra na nuna min ledar hannunta.

“Momy kalla turare da chocolate Hajiyarta ta ce ta kawo mana”

“Eyeee lallai kun gode”

“Laaaa Momy Good afternoon”

Ta fada tana mamakin ganina

“Ykk ya makaranta?”

“Fine”

Sosai yarinyar take kama da mahaifinta, sai dai ita tana da far'a da son mutane ba kamar shi ba. Kana ganin fuskarta ita da Namra ka san suna murna da ganin junansu, daman kwana biyu nan suna da damuna da maganar zuwa gidan ni kuma na banzantar da maganar sai ga ta a yau ta zo. Amal ma sauka tai daga bayana ta bi bayansu.

Ina sallame sallar la'asar Adnan da Namra suka shigo tambaya wai za su je waje su yi wasa, har ta bukaci na bata kudi ta biya kudin lilon da ake kusa da mu su biya su hau, ban musa musu ba na dauko jakata na ciro naira hansin na mika mata suka fita da gudu har suna rigengen. Wani irin faduwar gaba ne ya same ni sai na ji kamar na kira su na ce su dawo, gaba daya na ji babu dadi, ban kuma san dalilin hakan ba, zuciyata tai ta bugawa da karfi kamar zata fito tsabar faduwar gaban da nake, a take na soma ambaton Allah, sai dai ban wani damu ba ganin yamma ce na san shaidanun aljanu ma suna saka haka.  Bayan na gama azkar na dauko wayata na shiga YouTube in duba wasu videos har biyar da rabi tai sannan na fito tsakar gidan kamar yadda muka saba zama na zauna cikin ya'uwana. Sallama akai mana muka amsa sai yaro ya shigo yace wai ana kiran Baby Namra direban ta ne ya zo daukarta. Kamin mu ba shi amsa Adnan ya shigo gidan da gudu har ya faduwa wasu yara na biye da shi jikinsa duk kasa ya fado kaina.

“Momy Namra Namra....ta fada rijiya..... ”

Ban san lokacin da na ture shi ba na mike tsaye na daki kirji idanuwana a waje.

“Wace Namra?”



Jiya na yi 5k words yau kuma na yi 5k+ words 🤔 wace addu'a kuka min ne?🙄 Pls ku ba ni ita nai ma Halimatu ta koma gidan Abdulhamid 💔😪

Seguir leyendo

También te gustarán

52.7K 7.1K 110
မပိုင်း၄၅၆ကနေစပြီးဖတ်ပေးကြပါဦး
TSINTUWA Por Ta masu gari

Ficción General

1.5K 195 11
Top-notch season 2 Kin karanta SAHLA A PARIS? BANI DA LAIFI? ABINDA YA BAKA TSORO fa? To yanzun gamu da ASHRAF, SANIN GAIBU da Kuma TSINTUWA! Tsintuw...
37.1K 5.7K 65
Nashi Ƙaddara ta kasance ɓoyayya. Bagus Azeez kenan mai tsintar kansa cikin ƙaddarori ma bambanta da bai san ta ina suke faruwa ba. Seyyidah Murshida...
6.4K 798 30
Labarin Asma'u da Abdallah. da kuma irin kaddaran da kowannen su ke dauke da ita.