GOBE NA (My Future)

By KhadeejaCandy

141K 16.8K 5.7K

Babu mace da zata labarta yadda wata macen take ji har sai ta taba kasancewa a cikin halin da wacan macen ta... More

00
GN-01
GN-2
GN-3
GN-4
GN-5
GN-06
GN-07
GN-08
GN-09
GN-10
GN-11
GN-12
GN-13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52
53
54
55
56
57
58
59
60
61
62
63
64

26

1.7K 205 13
By KhadeejaCandy

Na yi mamakin ganin kawata Sa'adatu tana jirana a farkon shiga falona, ko wa nuna mata gidana ma oho ni har na manta da ita a cikin duniyar nan. Tun kam Abdulhamid ya faka motarsa ta mike tsaye tana ta kallon motarmu. Har ya faka motar ya bude ya fita be ce mim komai ba kamar yadda nima ban ce masa ba tun bayan shigowa a motar.
  Irin kallon nan da ta saba na yan bariki ta fara yi min kamin ta mikawa Abdulhamid shi tare da gaisuwa. Shi kuma ya amsa mata da fuskarsa ta rashin sakewa da mutane, ma'ana ba yabo ba fallasa ba kamar Aminu ba da idan ya ganta bakinsa har rawa yake wajen amsa mata gaisuwa.

“Wa nake ganin kamar Sa'adatu?”

“Ba kamar ba ce ni dince, tun da kin yadani ni ai na nemo ki”

Na yi dariya kamar yadda ita ma tai tana bin Abdulhamid da kallo har ya shige falon sannan ta kalleni.

“Shine angon na mu?”

“Eh shine”

Sai ta tabe baki har da wani lumshe ido ta bude.

“No wonder ake mana rowarsa, ashe kyakkyawa ne mai naira, gaskiya Halima kina dacen auren maza masu kyau da kudi, ko da yake kina da kyau ne shiyasa, da ni ke da kyaunki da yanzu na ci kudi”

‘Yes ina dacen aure a gidan hutun amman ba dan na hutu ba, sai dan na fuskanci wani kabulen’

Na fada a raina a fili kuma sai nai dariya na ce.

“A takaice dai mijina ya burge ki, gashi kuma shi ba kamar Aminu ba ne balle ku kulla”

Kallon rashin fahimta tai min tana yar dariya kamar ta ji kunya.

“Ban gane ba?”

“To ya za'ayi ki gane kuwa? Ke dai zo muje ciki”

Ina gaba tana biye da ni a baya har muka shiga falo. A kujerar da ke kusada kofar ta zauna ta zubawa Abdulhamid ido ni kuma na nufi two seater da yake zaune yana lasa waya na zauna a kusa shi, kamar wanda wani abun ki ya zauna kusa da shi haka yai saurin tashi ya nufi dakinsa, iyakar kokarin da nai na danne damuwar da na ji ne dan kar Sa'adatu ta zargi wani abu. Na tashi na shiga kitchen na dauko mata ruwa da lemun mu na hausa na kawo mata. Sai gashi ya sauko ko inda nake be kalla ba ya nufi kofa ya fice a uzurce.

“Halimatu wane irin zama kike da mijinki?”

Kamar daga sama na ji tambayar Sa'adatu tana mire baki.

“Kamar ya?”

“Ato kin san ni bakina baya shiru, na ga kamar akwai yar matsala a tsakaninku ko kuma shi haka rayuwarsa take?”

“Wai Sa'adatu sakin fuska yasa raini ya shiga tsakaninmu har ta kai kike iya fada min duk abunda ya zo bakin kina mu'amulantata yadda kika ga dama”

Sakin baki tai ganin kamar na taso mata da fada.

“Haba Hajiya ta, makano ne kawai zai shigo gidan nan yace be fahimci akwai rashin jituwa tsakaninki da mijinki ba, kuma wanda ya damu da kai ne ya damu da matsalar ne kawai yake nuna maka damuwarsa, kalle ki Halima Wallahi har kin fi auki a gidan Aminu dama da nan”

“Zuciyarki bata raya miki ko bana da lafiya ba? Babu abunda ya zo kanki sai rashin Jituwa?”

“Hmm yanzu dai Allah ya baki hakuri, mu bar wannan maganar, ya yaranmu ya su Amal?”

“Suna lafiya”

Na amsa mata ina kara hade fuska tare da dauke kai. Shiru ya shiga tsakaninmu kamin ta sake dauko wata maganar.

“Amman wai Halimatu ba kya kewar yayanki? Na ga Aminu ma da ke damu da yaya ba, yanzu yana ta shiga damuwar rashinku balle ke da kike tare da su kullum”

“Ke da kike iya barin Salim da Yusura kina zuwa wani gurin, ba tare da sanin irin kulawar da za a basu ba kika tafi hankalinki kwance har wani gari, balle ni da a gari daya ne kuma bautar Allah zan yi?”

“Ba ki gane ba ne, ni ai tafiyar kwana biyu ce ko uku, idan na dade na yi sati ke kuma aure ne fa, kin san wani lokacin baka sanin darajar abu sai idan baya kusa da kai kamar yadda Aminu yake a yanzu karki so ganin yadda ya koma abun tausayi duk inda ya zauna sai zancenki yake da na yaransa”

“Idan abu yana da muhimmanci a gurinka baka taba yarda ka rasa shi, tattalinsa kake, kana Ala ala kar ya subuce maka, domin duk ranar da ka rasa abun nan ka rasa shi kenan har abada, be kamata ki kawo min zancen wani namijin ba a gidan mijina, na dade da mantawa da Aminu ko wani abun daya shafe shi, ko da wasa karki sake min maganar Aminu”

“Ai na san Aminu ya kuntata miki amman Wallahi Halimatu yana cikin damuwar rashinki a yanzu, matar da ya aura ma ta rasa gane kansa”

“Wai Aminun ne ya turo ki yace ki zo ki fada min yana cikin matsala?”

Ta dan wara ido.

“Ahhh ni ina na ga Aminu da har zai ce min haka”

“Za ki gansa mana ke ai falkalsa ce, za ki iya sanin halin da yake ciki ko ma ya fada miki da kansa”

“Subhanallahi Haba Halimatu wannan bawa irin magana ce, na san dai ina raba wasu mazan, amman taya za ayi na raba mijinki Fisabilillahi, ni ba zan iya wannan cin amanar ba”

“Shiyasa a kike biyarsa kuna zuwa har wani garin kuna kwana, ke fa san komai da ke tsakaninki da Aminu, na samu ido ne kawai saboda na bar ku da Allah, shiyasa na tattara lamarinku na aje gefe, ba Aminu ba ko mai sunansa bana son ji yanzu balle shi din da kansa daga ke har shi na tsaneku tashi ki bar min gida”

Da sauri ta mike tsaye jikinta har bari yake.

“Kamar ba Halimar da na sani ba, da alama dai wani ya shiga tsakaninmu”

“Za ki fita ko sai na wulakanta ki”

Daukar jakarta tai ta juya da sauri ta fice tana waigena. Har bakin kofar gate na bita na tsaya sai da na tabbatar ta fice daga gidan sannan na rufe gate din na dawo cike da bacin rai.
  A lokacin dana zauna falo sai bacin ran abunda Abdulhamid yai min a gaban Sa'adatu ya tsaya min a rai, yanzu har ta kai Abdulhamid na kyamar zama a kusa da ni kuma ba zai iya boyewa a gaban mutane ba sai ya nuna? To ko dai ina dauke da cutar ne?ko kuma kiyayyar ce tai zurfi har haka a zuciyarsa. Ba yau kadai ba tun daga lokacin da abun nan ya faru na fahimci irin zaman da nake da Abdulhamid sai dai na yau yafi na ko yaushe.
Ba zan iya wannan zaman ba, sai kace an masa dole da ni ko kuma auren kiyayya mu ka yi? Idan har ya zai iya rabu da ni kai tsaye ba to ni zan iya neman rabuwa da shi domin rabuwar ce mafi a'ala a yanzu, zai fi samun natsuwa idan bana kusa da shi kamar yadda ni ma zan fi samun natsuwa idan na san bana tare da shi.
Ba Abdulhamid kadai ba ni inajin idan ma na rabu da shi ba zan sake auren wani namijin ba, domin na fahimcin gaba daya maza basa da kirki kansu kawai suka sani, ina ji a raina da ace ni ce ba zan iya yi ma Abdulhamid haka ba bazan iya rabuwa da shi ko nuna masa damuwa ba.

“Gaba daya mazan duniyar nan ba su da karki, gaba daya kansu kawai suka sani, su auri mace suna wulakantata suna yi mata yadda suka ga dama”

Na furta da karfi ina fashewa da kuka tare da dafe kai.

“Zan nemi saki, dole ne Abdulhamid ya sakeni, kuma ba zan sake aure ba, zan samu wani aikin zan rike yayana na cigaba da kula da su, ba zan sake yarda ciwon da namiji ya kashe ni ba, na gahi hakan nan wahalar ta isa haka...... ”

Wani abu na ji ya taso min ya tsaya min a kahon zuciya ya danne min numfashi, a guje naje na bude freezer na dauko ruwa mai sanyi na sha sannan na samu relief. Ji nai bana bukatar komai sai shan maganina shi kadai na ke sha ya lulani wata duniyar da nake mantawa da komai, gashi kwana biyun da nai ba sha ba har wani abu nake ji a cikin kaina kamar hayaki. Falon na dawo na bude jakata na dauko 2k na saka Hijab din da n cire na shiga bedroom na dauko keys na rufe gidan na nufi chemist din unguwar inda na saba siyen maganin.


AHMAD POV.

“Maganar gaskiya ba ka kyauta ba Gwarzo....”

Yayi saurin taron numfashinsa yana shafa kansa.

“Na sani.... Ni kaina bayan na mata fadan na ji cewar ban yi daidai ba, musamman da bata min tsawa ba kamar yadda nai mata, you know i hate mutum yai min tsawa”

“Ita ai ba laifinta ba ne laifin ma'aikantan gurin ne kuma.... ”

“Kuma What Rahim...? Sai son nanata maganar nan kake yi, i feel like na yi abunda be dace ba hakan be wadatar ba?”

Da mamaki Rahim yake kallon abokin na sa, daman can haka yake wani irin murdaden mutum ne mai wuyar sha'ani, shi ya kawo maganar abunda yai ma Halima, kuma ya fadawa masa be ji dadin yadda yai mata ba and now yana kokarin bleme Rahim akan ya bashi laifinsa.

“Muna magana ka ce you need to rest ka bar nan baka ce min ga gun da zaka je ba, ashe Exclusive City ka nufa, yanzu kuma ina zaune ne ka dawo ka bani labarin abunda ya faru, and now kana son ganin laifina, shiyasa kake samun rashin jituwa da mutanen ka, mutum ko naman jikinsa zai yanka ya baka sai ka ce da biyu yai, Hajiya ce kawai maganinka Wallahi, ba Hajiya ce kadai take saka matanka na guduwa ba Gwarzo Kai kanka matsala ne”

Tsaki yaja ya dauki hularsa ya saka ya fice daga falon yana ciro keys din motarsa a aljihu.
@360 isa gidan Hajiyarsa, as usual sai da ya fara shiga falonsa kamin ya wuce dakinsa, sai dai wannan karon be shiga da yanayin da ya saba ba, idan har bw shiga da sallama ba to zai shiga da far'a fuskarsa a sake sai dai yau babu ko daya. Be ma ankaro da ba kuwar da ke falon ba har sai da ta gaishe shi.

“Ina wuni”

“Lafiya kalau”

Ya amsa mata sannan ya zarce dakin Hajiya kasancewar be same ta a falon ba. A daki ya same ta tana aikin fesa ma jikinta turare da alama wanka tai ko kuma ta saka sabon kaya kamar yadda ya ga kwaliya a fuskarta.

“Gwarzo yanzu nake kokarin kiranka fa?”

Ta fada far'a fal tana aje turaren da ke hannunta.

“Amman dai a lokacin dawowa ta bwyi ba ko?”

“Ba wannan ba ne, ba ka ga bakuwa a falo ba?”

“Na ganta”

“Je ku gaisa”

“Mun gaisa ai”

“Je ku gaisa dai, ai ba irin wacan gaisuwar ba ka kalleta da kyau”

“Eh sai in ji me?”

“Ka ji kana sonta mana”

Kwantawa yai a kan kujerar da ke dakin yana girgiza kai.

“No no no no Hajiya, yanzu kuma ai bata mata na ke ba, ina ni ina mace yanzu”

Wani kallo Hajiya take masa shi kan be ma kula ba sai zuba zance yake.

“Da ma namiji ne sai naje na zauna mu sha fira amman mace a yanzu ni... No lalalalala, na dai namiji ne”

“Mace ta daina baka sha'awa a yanzu”

“Eh mana da ma namiji ne”

“Mazan ke burge ka kenan?”

Dagowa yai ya kalleta ganin ta zuba masa ido yasa ya tashi zaune.

“A'uzubillahi bafa can nake nufi ba, i mean da namiji ne dan'uwan sai mu yi fira”

Ya mike tsaye tare da zuba hannayensa aljihu ya fice daga dakin, dan yasan halin Hajiyarsa yanzu sai ta sauya ma zancensa ma'ana shi ko ba dagon zance yake so ba. Part dinsa ya nufo har lokacin hannayensa a aljihu yana takawa a hankali kamar mai jin wuyar cira kafar. Be yi  mamakin ganin kofar falonsa a bude ba tun da ya san mai masa haka a duk lokacin da aljanun nata suka tashi. Yana shiga ta zo da gudu ta rumgume shi tana dariya.

“Yes Daddy Oyoyo, Daddy na gyara maka dakinka na goge komai na sa turare”

Kanta ya shafa cike da kaunarta, yana murmushi.

“Good girl Allah yai miki albarka”

“Ameen Daddy za ka kai ni gidansu kawata Namra ko?”

Iskar bakinsa ya busar ya rika hannunta suka nufi kujera ya zauna, ya zaunar da ita saman cinyarsa sannan ya soma mata magana a hankali.

“Baby ke kullum kina zuwa gidansu kawarki nan amman ita ba kasafai take zuwa nan ba”

“Daddy ai su gidansu ba su da mota, shiyasa bata yawan zuwa, ni dai ina son zuwa gidan Daddy pls... ”

“And Baby na yi m maman kawarki fada”

Ya fada yana shafa kanta har yanzu jin yake be kyauta ba. Ta zaro ido tana rufe baki.

“No Daddy how?”

“Laifin tai min nai mata fada, so ko kinje gidansu ba zata miki yar fuska”

“Daddy tana aiki a karkashinka ne?”

“No”

“Then why kai mata fada?”

“Wani abun tai min wanda ya bani haushi”

Baby Namra ta yi masa wani kallo.

“Daddy waye be da gaskiya tsakanin kai da ita?”

“Ni ne”

Ya amsa kai tsaye sai ta sauka daga saman kafafuwansa.

“You should apologize to her”

Sakin baki yai be ce mata komai ba.

“For the sake of me Daddy bana son na bata da kawata Namra ina sonta, idan muje gidan ina jindadi akwai mutane da yawa a gidan kuma duka suna suna kuma Daddy scul din mu daya, Mommynta ta shafa kaina tace Allah ya min albarka Daddy why za ka yi fada da ita?”

Kokarin fashewa da kuka take, domin har cikin zuciyarta take son zuwa gidan su kawarta Namra and tana jindadin yadda yan gidan suke mu'amalantarta.

Hannayenta ya kama

“Zan kaiki gidan amman ba zan bata hakuri ba, ni nake da gaskiya ai”

“Amman yanzu ka ce kai ne da laifi fa”

“I mean na yi fadan da yawa amman dai ni ne mai gaskiya”

“Daddy.... ”

“Baby.... ”

Shi ma ya marairaice fuska kamar yadda tai yana kokarin rarrashinta Hajiya ta shigo falon.

“Gwarzo”

“Na'am Hajiya”

“Taso ka kaita gida”

“Bata wuce ba?”

“Eh kai zaka kaita gida, kuma ka tsaya ka kalleta da kyau”

“Tooo....”

Ya fada da dan mamaki, sannan ya saki hannun Baby Namra.

“Baby zan je na dawo sai na kaiki gidan ki bata hakuri a madadina kinji?”

Ta gyada masa kai tana share kwalla, Hajiya na gani hankalinta ya tashi.

“Baby ya akai? Me kike yi ma kuka?”

“Daddy ne ya tsokani momyn kawata Namra”

“Garin ya? Shi ne kika kuka kuma?”

Ta gyadawa Hajiya kai, shi kuma ya fice yana ta sake sake a ransa.  Falon Hajiya ya shigo sai ya samu yarinyar a zaune ta natsu sosai guri daya tana wasa da yatsun hannunta.

“Hajiya ta ce zan kai ki gida”

“Okay tau”

Ta mike tsaye tana daukar katuwar ledar da Hajiya ta bata tana unkurin tafiya sai ga Hajiyar ta shigo rike da hannun Baby Namra tana fadin.

“Ka biya da ita asibiti kanta ke ciwo, na bata magani ta sha tace min be daina ba”

Da okay ya amsa can kasan zuciyarsa kuma ya raya cewar lallai da gani hajiya na ji da bakuwar nan. Har gurin mota ta rakosu sai da ta shiga sannan tace..

“Ikilima ki ce ina gaishe da Hajiya na gode sosai sai na zo”

“In-Sha-Allah zan fada mata na gode Hajiya Allah ya saka da alheri”

“Ba komai Wallahi a sauka lafiya”

Sai da ya tashi motar aka bude musu gate sannan ta koma ciki. Tafiya kadan sukai Ahmad ya rage gudun da yake ba tare da ya kalleta ba ya ce.

“Ke ni ban san asibitin da zan kaiki ba, duk asibitin da zamu je yanzu sai mun bata lokaci kuma company mu yau basa aiki balle na kai ki chemist din dake ce, ku ba ku da likita ne da yake duba ku ko kika saba zuwa gurinsa?”

“Akwai wani likita da ke dubani, amman yanzu na sa ya tashi asibiti yana chemist dinsa”

“Ina chemist din take?”

“Tana can gurin tudun wada locos”

“Za ki gane gurin?”

“Eh na san gurin”

Be sake ce mata komai ya canja hanyar tafiyarsa zuwa gurin da ta fada masa, ita tai ta fada masa gurin har suka iso.

“Ki shiga ki ganshi zan jiraki a mota, duk yadda akai sai ki fada min zan ji da komai”

Ba musu ta bude motar ta fita shi kuma ya ciro wayarsa ya soma latsawa tare da kwantar da kujerar motar. Kamar hadin baki sai ga sakon karta kwana ta line Hajiya ya shigo.

_Ka samu wani abu ka bata, ko ka siya mata wani abun_

“To duk dai”

Ya furta yana murmushi, kamar wanda aka cewa dago, yana dago kansa yana hago Halima ta fito daga chemist din rike da leda baka. Bude motar yai ya fito, sai ya fito sai ya fara tambayar kansa me zai ce mata sorry? No ai ya girmi wannan yana jin idan yace mata haka ya kayardar girmansa. Amman ai ya kamata ya bata hakuri ko dan Namra, kuma tabbasa ya san be kyauta mata ba. zagaya yai ta inda take tafiyar dayan hannunsa a aljihu dayan kuma rike da waya ya sunkuyar da kansa kamar da gaske hankalinsa yana kan wayar ne.

“Ya akai lafiya? ”

Ta tambaya ganin kamar zai tare mata hanya. Dagowa yai ya kalleta sai kuma yaji nauyi bude baki yai mata magana.

“Ko nan din ma hanyarta ne? Ko kuma tsabar rainon wayo ne kawai da wulakanci irin na ka, ko na maka kama da yar tasha ne, domin yanzu na fahimci babu komai a tare da kai sai wulakanci kawai, a duk lokacin da na hadu da kai sai ka wulankanta ni ko kasa a wulakanta ni, kai na fahimci sam ba mutumen kirki ba ne, sai wani jijji da kai, kana jin kai wani ne kuma kai ba kowan kowa ba, abun kai min dazun na kyale ka ne kawai saboda ina ganin kamar ni ce bana da gaskiya but then i realized na fi ka gaskiya, kai sam baka da kirki sai wani son nuna isa kamar mai garin Gusau, to bari na fada maka karka sake cewa zaka min wani rainon wayo Wallahi zan mugun wulakantaka, dan na gane ku mazan nan ba ku da mutumci, by the way ina da miji ina da aure ina da yaya karka sake ka ce zaka min magana Mtscheeeessss.....”

tun da ta fara maganar yake kallonta har ta gama taja masa tsaki ta kara gaba ta bar shi a gurin da mamaki.

“I just....”

Ya fada yana daga hannunsa tare da bin bayanta da kallo, sai kuma ya ksa cewa komai ya jimke hannun.

“Am... Baya nan wai be shigo ba yau”

Ikilima ta fada shi kam har ya manta tare da wata suka zo, sai a lokacin ya soma lura da ba su kadai ba ne a gurin. Kasa kasa yake satar kallon mutane be taba jin tozarci irin wannan ba. Matsawa yai kusa da Ikilima.

“Mutane suna ganinmu lokacin da take min fada?”

“Yes da karfi fa take yi dole kowa ya kalleku ai”

Wani abu na ji kamar ya netse a kasa, saboda ya san people would think ko ya mata wani maganar banza ne. And she's right be kamata yai magana da matar aure ba, dan idan shi ne wani nai magana da matarsa zai iya masa komai ma, but shi ya manta da maganar aurenta ma.
Oh does she think sonta yake yi? Ko kuma ta maida shi wani banza ne take fada masa haka, har ya shiga motar be daina sake sake ba.

“She got lucky bana fada da mata, amman wallahi da namiji ne yai min haka sai an dauki gawarsa a nan i hate nonsense”

Ya fada yana fisgar motar kamar zai tashi sama, after few minutes ya bugu sitiyarin motar da karfi.

“Matar nan ba tai ba, i hate her so much, da ganinta mahaukaciya ce”

Ikilima dai bata ce masa komai ba bayan kallonsa da tai, tsoro dai ya gama kamata dan ta lura ransa ya bace sosai.

“Ai duk laifinki ne da kika kawo ni gurin nan, da ta isa tai min kallon banza ma, amman ji irin maganar da ta fada min son ranta, sai yanzu ai na gane bakar magana ta fada min”

Nan da nan jikin Ikilima ya fara rawa domin ta lura har fuskarsa ta canja sa gumi yake kamar marar gaskiya duk kuwa da irin ac da ke cikin motar.

“Har da wani wai kana jin kai wani ne, ai ni wani din ne ke ba kowa ba.... Mtchhhh”

Yaja tsaki yana jin kamar a gabanta ne ya rama, domin a duniyar nan yafi tsanar tsaki fiye da komai, da ka yi masa tsaki ko ka tofar masa da yawu kara ka mare shi ko ka zage shi.....

Continue Reading

You'll Also Like

881K 15.9K 56
" ဒယ်ဒီဘာပြောပြောဖြူဖြူတို့လက်ထပ်စရာမလိုပါဘူးကိုကို.." " ဒါပေါ့.. မင်းကမိဘကိုလည်းဂရုမစိုက်၊ပတ်၀န်း ကျင်ကိုလည်းဂရုမစိုက်ပဲနေနိုင်ပေမယ့်.. ငါကတော့ဆရာသ...
344K 27.2K 34
punishment type ပါ။ အဆင်ပြေမှဖတ်ပါ။
TSINTUWA By Ta masu gari

General Fiction

1.5K 195 11
Top-notch season 2 Kin karanta SAHLA A PARIS? BANI DA LAIFI? ABINDA YA BAKA TSORO fa? To yanzun gamu da ASHRAF, SANIN GAIBU da Kuma TSINTUWA! Tsintuw...
1.3M 37.5K 65
ယော.. ကျွန်တော်ကလူတော်..ဒါပေမယ့် လူကောင်းမဟုတ်ဘူး။ စာရေးသူ၏ စိတ်ကူးယဥ်မှုဖြင့် ရေးသောကြောင့် အပြင်လောကနှင့်ကွဲပြားနိုင်သည်ကို သတိချပ်ပေးစေလိုပါသည်။ လ...