ZARAHADDEEN

By hijjartAbdoul

1.6K 71 8

read and find out More

1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
16
15
18
19
20
21
22
23
24
25
26.
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
40
41
42.
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52
53
54
55
56
57
58
59
60

39

25 1 0
By hijjartAbdoul

39

*******Sai ƙarfe goma da kusan rabi ta tashi daga bacci, wani irin bacci ne tayi me cike da daɗi da annashwa, ta jima batayi irin wannan baccin ba sai yau, wata irin nutsuwar zuciya taji tana ji. Ga wani irin farin ciki da bata taɓa tsintar kan ta a ciki ba sai a yau ɗin nan. Murmushi fal fuskar ta, tayi juyi a karo na ba adadi, sannan ta tashi ta kalli ɓarin sa sai kuma tayi murmushi tana shafa wuyan ta, da'alama bacci yayi daɗi ko juyi batayi ba.

Wayar ta da ta gani akan side drawer ta gani an ɗaura takarda akai, ɗaukowa tayi ta buɗe.

"Idan kin tashi ina fatan kin tashi lafiya, ya kike? Ya kika tashi? Dan Allah ki koma wajen aiki, tun jiya suka turo suke da buƙatar mu. Ni yau na tafi company akwai baƙin da zan yi. Hajiya banda faɗa dan Allah, zuciya ta zata iya tarwatse ta fashe. Ki kula min da kan ki".

"Hashim zai zo, ki kaishi wajen Mu'azzam. Ki kula".

Murmushi tayi ta ajje, ta sake buɗe wata ƙaramar envelope ɗin dake gefe, taga mukullin motar ta ne. Yayi emoji ɗin banda haƙuri yasa am sorry ya kama kunne. Wani irin dariya ce ta ƙwace mata, tare da fara tashi tana gyara ɗakin. Wato mutumin ne ya sace Mata key ɗin motar, yana ji tana ta masifa akai amma yayi burus da ita bece komai ba. Har ta shirya tana murmushi ita kaɗai. Samun kan ta tayi da saka doguwar dake cikin kayan lefan ta, ta yafa mayafi, tare da rataya jakar ta taje gaban madubi tana kallan kanta.

Ita kan ta taga tayi kyau, inaga shi kuma? Ƙara kallan kanta tayi, kwalli tasa ka da lipgloss harda su powder. Da warwaro yau aka saka sai ta fito ɗas a macen ta. Idan ta ne kawai yayi ciki saman idan suka kumbura alamar kuka. Amma kwallin da ta saka sai ya fito da dara daran idan nata. Sake kallan kan ta tayi a karo na uku, sannan ta nemi hanyar fita, har zata fita sai kuma ta dawo da baya da baya tunawa tayi da ya taɓa ɗaura mata ɗan kwalli, hula ta samu ta saka ta sake gyara rolling ɗin sannan ta fita. Fuskar ta cike da murmushi. Sanda ta fita ta tarar da Ɗalhat da Hashim a parlourn na su, an kawo musu ruwa da abinsha.

Murmushin dake kan fuskar ta be ɗauke ba ta amsa musu, tare da samun waje ta zauna suna sake gaisawa, baƙaramin mamaki suka ji ba ganin ta a haka, ba su taɓa ganin tayi doguwar magana da ɗaya daga cikin su ba, kullum fuska a tamke, fuska a ɗaure ga kwarjini da Allah ya zuba mata kai kace wata uwar mata ce idan ta haɗe ran nan.

"Daman kina dariya?

Hashim ya kasa daurewa ya faɗa, zungurar sa Ɗalhat yayi.

Yace, "Kaga barni na faɗa".

Murmushi ta ɗan yi.

Tace, "Ina Maryam?

"Tana shagon Ameerah".

Cewar Ɗalhat, dan shi har yanzu ɗari-ɗari yake da ita. Wani murmushin kawai ta yi tace musu tana zuwa.

"Na rasa dalilin da yasa Yaya Deeni zai ce mu bita wallahi".

Cewar Ɗalhat yana kallan hanyar kitchen ɗin.

Hashim yace, "To wai meye ne? Gashi nan yanzu ta mana tarɓa ta ban mamaki ai. Da har kake gwada yarda zata mana".

"To ai nasan halin ta ne".

"To gashi ta baka mamaki".

Abinci ta ci kaɗan sannan suka fito, ta gaida Umma ita da Baba sannan ta musu sallama ta wuce, suma Sallamar  ta musu suka tafi. Hashim ne ya ce ta kawo ya ja ita ta koma baya, bata musa ba ta basu suka ja, tana kwantanta musu har office ɗin,duk da Hashim ya sani amma be nuna yasa ni ɗin ba.

"Wannan motar Daad ce".

Cewar Ɗalhat yana nuna motar A. Madaki. Hakan yasa ita da Hashim suka kalli wajen.

"Dad?

Hashim ya faɗa cike da mamaki sai kuma yayi wani gajeran murmushi.

Ya kalli Hafsah yace, "Wanne meeting ɗin zakuyi?

"Nima bansani ba, sai naje".

Jinjina kan sa yayi.

Yace, "Idan meeting ne na haɗa kar company, ki kirani zan shiga".

Da sauri Ɗalhat yace, "Ka shiga kayi me?

"Na shiga nayi replacing companyn mu".

"Amma Hashim gaskiya baka da hankali".

"Ni kuwa nake da hankali Ɗalhat".

"Please ki kira ni".

"Uhm".

Kawai tace ta fita, sai da fita a ran ta tace 'to da me zan kira ka ɗin' hakan kuma be san ta koma ba. Sanda ta shiga reception ɗin da kallo kowa ya bita ganin irin shigar da kyan da tayi ga fuskar ta tayi wani irin fayau da ita, sai wani annurin da bata san yana fita a fuskar ta ba. Babu wanda tayi wa magana daman ba magana take da kowa ba har ta shigo office ɗin su, suma suka bita da kallo, musamman su Zee da suke mata kallan kucaka yau kam ba ƙaramin kyau tayi musu ba. Daman mutun idan yana shiga ɗaya ka saba ganin sa a cikin idan yasa wani kayan sai kaga ya fi dacewa da shi fiye da tunanin mai tunanin. Yayin da wani sashe na zuciyar Aisha yayi wani irin sanyi dashi ganin cewa zata ga Zaraddeen, da ta tabbatar da blocking ɗin ta yayi.

"Yau za ga Darling Deeni".

"Darling wahala de".

Cewar Zainab, zata yi magana Khadijah ta matso alamar gulma.

Tace, "Bana ji ana cewa an kore su ba?

Zainab tace, "Ke raba ni da wannan gulmar ta companyn nan, ƙaryar fa?

Aisha tace, "kunga ba haka ba ne ba".

"To meye?

"A'a bakomai".

Ta faɗa tana jan bakin ta. Tana sake kallan ƙofa ko zata ga Deeni, sai de be shigo ba, sai tayi ƙwafa a ran ta tana ɗan yaƙe.

Hafsah kuwa samun wajen Mu'azzam tayi ta zauna,  ganin yaje ya dawo baya nan, ɗaukar tablet ɗin sa tayi tana duba schedules ɗin da suke dashi a ranar.

"Yau kuma kune a companyn na mu?

Cewar Mu'azzam yana zama, ɗan murmushi tayi masa kaɗan.

Tace, "Ehh ba".

"Amma kun dawo  kenan ko?

"Ehh ba".

Murmushi yayi shima bece komai ba, kafin ta ɗago ta kalle shi.

Tace, "Ya faɗa maka zan haɗa ku da wani?

"Ni kuma? Deeni?

Jinjina kai tayi alamar eh.

"Be sanar dani ba".

Shiru kawai tayi bata ce komai ba, har ta gama duba abinda zata duba. Ganin suna da meeting shabiyu yasa ta cewa.

"Kana zuwa meeting ne?

"Ina zuwa, yanzu ma muna da meeting ɗin ai. Da A. Madaki".

"Wanne irin meeting ne? Na cikin company ne?

"A'a masu zuba share ne za su zo, har daga waje ma".

Jinjina kai tayi tare da cewa tana zuwa, bata jima ba kuwa sai gata ta zo da Hashim, tunda suka shigo Mu'azzam yake kallan sa, ko shine wanda za su haɗu ɗin? Yayin da su Zainab aka fara iyayi ga ɗan gidan A. Madaki sune daman ba su taɓa ganin sa ba, dan duk wayanci suna ganin sa kwanaki yana zuwa, ba su san me yake zuwa ba amma suna ganin sa. Haka suka ta so wai zan suyi hoto da shi, dariya ma shi suka bashi, babu kalar wanda be gani shikam, a mata sai de ya bada labari amma ba'a de a bashi ba. Hakan yasa ko kallan inda suke be yi ba, kawai da murmushi ya bi su yayi gaba.

"Mata suna bada mu wallahi. Allah ya isan mu".

Cewar takwarar Hafsah, kallan ta Hausa tayi taga yadda take mita tana danna keyboard kamar shine ya mata laifi. Hararan ta itama tayi tunawa da mijin yana mata magana kuma ta amsa.

"Munafuka".

Itama ta faɗa tana jan jakar ta kamar ita ce ta mata laifin, tashi Mu'azzam yayi jiki a sanyaye ya bi bayan su, zuciyarsa har wani harbawa take yi, tunawa da yayi wai shine fa Yayan sa, wai Hashim. Anya ba mafarki Umma ke yi ba?

Cak A. Madaki ya tsaya da kallan papern dake hannun sa tare da ɗagowa ya zubawa Hashim dake shigowa ido har ya samu waje ya zauna a kusa da Hafsah, haka ma Mu'azzam shima a kusa da ita ya zauna, sai ya zamana cewar sun sa ta a tsakiya ne. Yayin da Hashim ya dake zuciyarsa yana jin yadda take tsalle amma ko kallan inda A. Madaki yake be kalla ba, fuskantar irin kallan da yake jifan sa dashi yasa shi ɗagowa suka hada ido, wani irin shegen sanyayyen murmushi Hashim yayi masa tare da jinjina masa kai yana lumshe ido. Amma duk da haka A. Madaki be kwantar da nasa hankalin ba, kada fa ya zo yaron nan ya fallasa shi a idan duniya, ga Camera na kallan su, wannan harda manyan mutane daga ƙasashe.

Cike da ƙwarewa aka fara gudanar da tattaunawar da ta haɗa da ƙwararrun ƴan kasuwa masu ji da ilimi da kuɗi, har aka zo kan Mu'azzam aka yi Hafsah. Sai da aka zo akan Hashim sannan A. Madaki ya fara murmushi yasan dole shi ya zowa kuma za suyi nasara.....

"Zaharaddeen Furniture".

Wani irin dum A. Madaki yaji ganin sa da kunnen sa suka ɗauke na wasu lokutan, ba su tashi dawowa ba sai da yaji ana masa tafi har an kammala meeting ɗin sun tashi, domin kuwa sun fara jin irin nasarar da Z products suke dashi, sai gashi ya kawo kan sa. Be san abinda ake ba sai da yaga ana miƙo masa hannu a gaisa, kwata-kwata be taɓa kawowa cewar Hashim ba companyn sa zai wakilta ba sai wani banzan sabon company can a gefe da ba'a san da shi ba a duniya.  Magazine guda aka ajje na irin abubuwan da Z furniture suke yi.  Sanda ana nuna masa kam yaga kaya ba kariya don sun fi na companyn sa, da kuwa ake sake sanar da shi irin share ɗin da suka zuba a companyn sai da ya nemi kusan ya fadi 70% wanne irin kuɗi ne su kuwa sa su haka?

Daƙyar yayi excusing kan sa ya fita, sai de yana fita babu su babu labarin su, be yi tunanin da Hafsah suka zo ha, hakan yasa ko ta kan ta be ba, gashi babu cameran tsaro a harabar companyn sai ta ciki itama ta iya reception ce.

*****"Gaskiya Hashim baka da hankali".

Cewar Ɗalhat bayan ya gama sauraron abinda yake sanar dashi, yayin da Hafsah je driving ɗin a yanzu Mu'azzam na gaba yana mata kwantancen gidan su.

"Da nayi me?

"70% naji ka ce ka zuba fa Hashim?

"Da wani abu?

Girgiza kan sa yayi.

Yace, "Deeni ne yace nayi haka ba yin kai na ba ne ba".

"Yaya Deeni kuma?

"Ehh".

"Amma taya?

"Shine yace na shiga, na zuba har 70%".

"Kuma yana ganin ba wata matsala?

Girgiza kan sa Hashim yayi alamar bansani ba. Ajiyar zuciya Ɗalhat ya sauke kafin ya juyo da sauri.

Yace, "Kar ka ce min Deeni ne wanda ya ci ku a Anadyr? Sanda ka je? Shine?

Jinjina kan sa Hashim yayi alamar eh.

"Idan kuma Daad ya gano shine mafarin matsalar sa kasan ba zai rabu dashi ba?

"Share kawai".

Cewar Hashim, a lokacin suka yi parking a wani lungu, dan sun tashi daga wancan gidan na unguwar su Ɗalhat, ga duk kwata a wajen. Tunda Hashim yake be taɓa ganin unguwa irin wannan ba, duk cakwali ga ƙazanta, duk a tunanin su inda suka yi parking ɗin ne gidan sai ji suka yi Mu'azzam na cewa su shigo nan ne,Daga Ɗalhat har Hashim kallan juna suka yi suna kallon kallo, kafin suka fara bin bayan su, suna jefa ƙafar sa a wurin da babu caɓi. Da haka suka shigo cikin gidan da ko ƙofa baya da shi. Gidan a share tas dashi ko ina fes, ɗaki biyu ne a jere a gidan sai Wata ƙofa da ita ma labule aka sa mata da'alama bayi ne a wurin, ko kitchen babu a gidan sai jikin katanga da wata mata ke  hura wuta gefe guda kuma tana jajjage cikin turmi. Jin Sallamar Mu'azzam yasa cewa batare da ta juyo ba.

"Mu'azzam har kayi me?

"Umma ina tare da baƙi".

Ya faɗa yana fara shimfiɗa musu abin zama. Yayin da ta juyo ta fara cin karo da Hafsat tana mata sannu da zuwa, sai ta ta so dukan ta dan taya shi shimfiɗa tabarmar tana musu lalle da zuwa, dan ko kadan idan be kai kan Hashim ba, yayin da daga shi har Ɗalhat tsayawa suka yi suka zuba mata ido daga ita har inda take rayuwar a cikin sa, wani irin ɗaci da ƙunci ne danƙare a cikin ran Hashim, wannan ita ce Mahaifiyar sa? Nan shine inda ƙannin sa da Mahafiyar sa suke rayuwa?

Wani irin rauni yaji yana lulluɓe shi, tuni ya ji idan sa ya ciko da hawaye,kawai bin ta da ido yake yi, da'alama ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba, daga yarda take tafiyar ma kaɗai ya isa ya tabbatar maka da haka.

"Umma ina Sumy ta barki kike aiki?

Ya faɗa yana komawa wurin wutar tare da ƙara izawa ya fara jajjaga kayan miyan dake turmi. Ita kuma ta je kawo musu ruwa a randar da ita kaɗai ce a wurin.

"Ta tafi makaranta, ai ba za suyi ta zama haka ba, karatu na wuce su ko kuwa de?

Beyi magana ba, ta sake dawowa ta kawo musu ruwan, sannan ta janyo ƴar kujera ta zauna.

Tace, "Sannun ku da zuwa".

Gaisuwa suka yi da Hafsah, kafin Hashim ya kalle ta idan sa taf ƙwalla, kasa ce mata komai yayi kawai kallan ta yake yi cike da wani irin tausayi ko shakka babu ita ce mahaifiyar sa wannan kuma shine ƙanin sa. Kallan sa da tayi ne yasa ta tsayawa da komai ta cigaba da kallan sa cike da wani irin mamaki ɗauke a fuskar ta, mutumin da kake tunanin ba zaka gan shi ba awurin idan ka gan shi sai ya fi komai baka mamaki.....

********"Mr. Deen. Kayi shiru ba zaka ce wani abu ba?

Ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke, ya zuba musu idan sa tare da musu sanyayyen murmushin nan nasa me sa mutum natsuwa.

"Nayi shiru ne saboda wannan haɗaka ce ta family, bani da iko ko hurumin yin magana ni kaɗai har sai kowa da kowa ya amince".

Shiru yayi yana murza yatsun hannun sa tare da murza goshin sa kadan yana yin baya da kujerar sa.

Yace, "Kada na wahalar da ku wajen dawowa, a gaskiya ba zamu haɗa hannu da kowa ba, mu zuba hannun jari ko mu karɓi hannun jari. Zaku iya tafiya".

Daga haka ya tashi, ya bar su a wurin, baki da hanci suka saka suna kallan sa.

"Moddibo idan sun tashi a rufe office ɗin".

Ya faɗa yana ficewa, da ido kawai suka bishi, wanne irin mutum ne wannan shi? A zo masa da abin Alkhairi amma ya watsa musu kasa a ido? Lalle wannan baya da mutunci, ko ba komai ya duba irin wahalar da suka sha wajen zuwa ai. Ganin Moddibo ya fara rufe windows yasa su tashi jiki babu ƙwari suka fice daga companyn gaba ɗaya.

Gani suka yi an ajje musu carton carton ɗin Yoghurt da Fresh milk, a bakin motar su wai an basu, haka suka ce ba sa so.

"Ku ɗauka ku mayar mana, bama tursasawa ga wanda be san muhimmancin kyauta ba".

Suka tsinkayi muryar Deeni ta faɗa cikin sanyi da kalama kamar babu wani faɗa a cikin sa., sai de abinda suka fuskanta game da shi, ya ji zafi da ciwon abinda suka zo masa dashi sai de be fito ya nuna musu ba kawai dannewa yayi ya kuma shanye, jikin su ne yayi sanyi kuma da irin abinda suka ji ya faɗa a yanzu. Motar sa ya shige ko kallan inda suke beyi ba ya fita daga harabar wajen, suma fita suka yi suna nanata abun da ya musu.

Gida Deeni ya je suka gaisa da Kawu, ya ci abinci yayi ƙasarun sa ta azahar dan kafin yaje ba'a yi La'asar ba, hakan yasa shi be yi ba, ya musu sallama ya tafi. Sai da ya biya ɗauko Fa'iz sannan ya ajje shi, shi kuma ya wuce.

Be zarce ko ina ba sai office ɗin Major Kabir, ba su taɓa ganin sa ya zo ba, hakan yasa tun daga gate ake masa binciken babu gaira babu dalili, ga wasu tambayoyi iri iri da ake masa, sai da ya ce shi ɗan sa ne sannan suka ɗan amince suka barshi amma duk da haka sai da ya ajje motar sa suka shiga tasu aka ƙara so da shi ciki, duk sun kira shi ance komawa su barshi ya shigo amma sai da suka masa wannan shegen binciken. Shi Deeni mamaki ma suke bashi, to idan wani abu za'a yi masa suna tunanin ba za'a iya ba ne ko me? Duk wayo da dabara ba su san cewar makashin ka ya fika dabara ba?

Daga jin sunan Deeni da computern ta faɗa yasa Major Kabir ɗagowa ya zubawa cameran ido yana kallon sa har ya shigo.

"Yau kuma kai ne ka zo ?

Cewar sa yana ta sowa daga inda yake.

"Ai ba zan sake zuwa ba, sai ka ce wanda nayi kisan kai".

Murmushi yayi masa ya miƙa masa hannu suka gaisa. Da kan sa ga kawo masa abin sha.

Yace, "Ka ce ka haɗu da bincike da mutanen".

Shima murmushin kawai yayi.

"Nasan ba zaka zo haka kawai ba, me ya kawo ka?

"Abbaaahh".

Ya faɗa irin ya da haka ?

"Eh nasan ko waye Deeeni na shiyasa nace haka".

Murmushi Deenin yayi yana shan abinda ya kawo masa.

Yace, "Akan Sabir ne, da abinda ya faru da su shi da Najma a makaranta".

"Wani abu ya faru ne?

Shiru Deeni yayi, kafin yace, "Abba, a lokacin da abin ya faru, wani abu ne ya sha maka kai da baka fahimci komai ba, bare kuma ka bi ba'asin abinda ya faru".

Shiru yayi yana tuna ranar, dan kuwa haka ne, be taɓa mance wannan ranar ba tun daga farkon ta har ƙarshen ta, gefe guda ranar ce ranar da yayi farin ciki har ya zubar da ƙwalla, a wani gefen kuma ranar ce da ya ji zuciyarsa tana daf da bugawa sakamakon abinda ya faru.

"Abbah, na je har school ɗin su a ranar, na yi bincike akan dalilin da yasa abin ya faru".

"Abba accident ɗin da ya faru da su, shirya shi aka yi".

"Deeni me kake san ka ce?

"Dagaske nake maka Abbah, shirya shi a akayi, makarantar ta abokin A. Madaki ce, wanda suke kasuwanci tare da shi, daga baya ya siyarwa da A. Madaki ita, batare da kowa ya sani ba sai a tsakanin su da kuma lauyoyi. Nadiya da take aiki a makarantar yarinyar ita ce abokin nasa ce. Shi be san komai ba dangane da A. Madaki da kuma waye shi. Kawai yasan shi ne a matsayin abokin kasuwancin sa.

"Nadiya tana tunanin da cewar Sabir ɗana ne, saboda ada ta so ni sosai bansan me ya faru ba ta janye soyayyar da take min, A. Madaki yayi amfani da ita ne don ya ji labarin abinda ta take yiwa Sabir. Hakan yasa yayi kwangilar ta, ta haɗa duk kan abinda ya faru. Har ta buge shi akai shine dalilin da yasa Sabir ya samu matsalar da yake fuskanta a yanzu".

Kallan sa kawai Major Kabir yake yi babu ko ƙiftawa.

"Kallan fa?

"So na gano ƙarya kake min ko gaskiya,kuma na kasa".

Dariya abin ya bawa Deeni yayi murmushi kawai yana cewa kai Abbah.

"Ehh mana ba gaskiya na faɗa ba?

"Ehh hana ne".

Ya faɗa yana ɗan murmushi, ajiyar zuciya Major Kabir ya sauke.

Yace, "Meye dalilin sa nayin haka?

"Saboda so yake ta kowacce hanya ta kowanne fanni, ya kassaru, kamar yarda ta saba yi a baya. Yana kuma tunani jefa mu a cikin prison".

"Shi ma kuwa zai je tunda junan sa jefa mutane a prison ba?

"A'a shi ba zai je ba, ko court ba zamu je da shi ba, haka zamu bar shi yaga rayuwa ya koyi rayuwa da kuma darasin dake cikin ta. Yadda kowa ya talauce haka shima sai ya talauce Abbah in sha Allah".

"Kana tunanin abu ne mai sauƙi yin haka?

"Ba abu bane mai sauƙi Abbah amma ka jira lokaci in sha Allah zaka san komai".

"Deeeni haka kake daman?

Shiru Deeni yayi bece komai ba, kafin ya ajje abinda ke hannun sa.

Yace, "Ni na tafi".

"Nadiyar ce ta sake zuwa ta sanar dashi zancen da ya rikita masa ƙwaƙwalwar sa, ga dukkan alamu ana sanar da shi information akan komai dake faruwa".

Major Kabir ya faɗa ganin Deeni ya tashi be yi magana ba, juyowa ya kalli Major Kabir ɗin da ya harɗe hannun sa a ƙirji yana kallan Deeni, sun jima suna kallan juna kafin, Deeni yace.

"Ka sani ko asibitin nasa ne?

Daga haka ya wuce ya bar Major Kabir da tunani.

******Zuwa yayi ya gano Sabir daga nan ya wuce gida, babu wanda ya dawo a cikin su sai su Umma kawai, sannu da gida yayi musu ya dawo part ɗin su. Sallah kawai yayi ya fara kallan ɗakin, kafin yayi murmushi ya gyara shi irin yarda tayi ɗin nan. Baƙaramin kyau yayi ba, ada ɗin ka ya masa kyau kawai muzgunawa ce irin ta sa da nuna masa irin isar da yake dashi akan ta. Tas ya gyara ko ina yayi kyau. Sannan ya wuce yayi wanka ya fito ya fice waje wurin kiwon sa.

Ganin motar sa a wurin yasa ta ganin cewar ya dawo kenan, murmushi tayi sannan ta fito a motar ko wurin su Umma bata je ba, ta wuce ɗaki dan wani ɗokin ganin sa taji tana yi. Ganin baya ɗaki kuma bata ji motsi ba a toilet yasa ta fito tana duba shi, baya wajen su Umma, kawai ta nufi wajen kiwon dan ganin wajen a buɗe, harɗe hannun ta tayi a ƙirji tana kallan sa fuskar ta cike da murmushi akan ta.

A hankali ya juyo ya zuba mata idon sa, shima murmushin ya sakar mata, kafin ta fara takowa ta zo inda yake, tana rungume da files da kuma jakar ta da bata ajje ba, bama tayi tunanin da su take wayo ba. Burin ta kawai ta sashi a idan ta.

"Ka dawo?

Ta faɗa a sanyaye tana ƙin haɗa ido dashi.

"Kin dawo?

Shima ya mayar mata da amsar, yana kallon ta, ganin ta kasa haɗa ido da shi, sunkuyar da kan ta sake yi sai de fa dan turo baki kaɗan alamar bansan me zance maka ba. Murmushi yayi.

Yace, "Zo ki buɗe bakin ta na zuba mata wannan madarar".

Ya faɗa yana riƙe ƴar ƙaramar jaririyar tinkiyar, sai kuka take yi.

"Ina Maman ta?

Ta faɗa tana ajje kayan hannun ta.

"Mamanta ta rasu tana haifar ta".

"To ai ba zan iya ba, sai de ka buɗe na zuba mata".

Kallan ta yayi yana murmushi, ya miƙa mata madarar dake cikin fida, tare da ƙoƙarin bude bakin nata.

Yace, "Kin manta lokacin da kike zuwa ki bawa tinkiyata madara ne, haka zaki matse ta ki ringa ɗura mata wai ke a dole kina bata abinci".

"Kai Abokin Yaya. Banda sharri".

Ta faɗa cike da sakalci.

"Ba sharri ba ne ba, har haka kike cewa wai zaki bata naki, a lokacin har da su ƙoƙarin fito da shi, time ɗin ma ko.... Su o'o ba'a fara ba".

Ranƙwashin sa tayi.

Tace, "Allah sharri kake min".

"Ba wani sharri gaskiya ce. Hajiya banda mantuwa fa".

Haɗe rai tayi, tana shan kunu tare da dungurar da fidar.

"Ka samu wani ya taya ka bani ba".

Murmushi yayi mata, yana janyo hannun ta.

"Yi haƙuri toh, na dena".

Dawowa tayi tana zumɓura baki gaba, shi kuma yana murmushi yana kallan ta, tunowa da irin abubuwan haukan da ta ringa yi, daga ƙarshe kuma gashi ya mallaki abin sa.

"Wai murmushin fa?

"Ba komai".

"Faɗi de".

"A'a da gaske babu".

"Uhm".

"Ina faɗa zai zama abin faɗa gwara kar na faɗa ko?

Shiru tayi masa bata ce komai ba, shima shirin yayi ya cigaba da murmushin abin sa. Har suka ga kammala.

"Bani shi na riƙe".

Ba musu ya miƙa mata, ita kuma ta riƙe shi.

"Kuma yanzu wata ba zata iya bata ba?

"Ko mutane ba duka ne suke shayar da ɗan ɗan uwan su bare kuma dabba".

Ya bata amsa yana kallan ta, ɗan hararan sa tayi alamar meye haka? Wani murmushin yayi taje ta ajje shi a ɗan gidan ta, da aka zagaye mata.

"Kasan wani abu?

Girgiza kan sa yayi alamar a'a.

"Goya ni zaka yi nagaji".

Tsayawa kawai yayi yana kallon ta. Ita kuma tayi kalar tausayi looking so innocent. Be kula ta ba yayi gaba bayan ya ƙare mata kallo. Wani iri ta ji a ran ta amma sai tayi murmushi tayi gaba itama bayan ta kwashe kayan ta. Su Hafsah da naci harda gudun ta ta kamoshi suka jera a tare kallan ta kawai yayi be yi magana ba ita kuma ta sakar masa murmushi. Yarda tayi ɗin ne ya bashi dariya sai yayi mata murmushi kaɗan yana yin gaba.

Sai yanzu ta samu ta ƙarewa ɗakin kallo, irin tsarin da ta mayar ne ya mayar, bata sanda ta je inda yake ba kawai ta rungume shi ta baya. Tsabar dadin da taji, ita mutum ce marar ɓoye abinda ke ran ta, idan ka mata a wurin zata maka tas bata da riƙo ko kaɗan, amma idan ka ci zalunta to ba zata taɓa yafe maka ba, kuma tsana ce zata maka mafi girma da muni. Shi yasa har yau take jin zafin A. Madaki akan abinda ya musu sosai take jin haushi da zafin sa.

"Nagode".

Ta faɗa tana sake ƙanƙame shi, ajiyar zuciya ya sauke a hankali tare da juyo da ita gaban sa, ga mamakin sa kuka yaga tana yi. Kasa ɓoye mamakin nasa yayi, ya tallafi fuskarta da duka hannun sa. Ta rufe idan ta hawayen na fitowa, murmushi ya sakar mata tare da yasa hannun sa ya goge hawayen.

Yace, "Me ya faru?

Bata ce masa komai ba sai rungume shi da ta sake yi. Raɗar da ya mata ne yasa ta saurin sakin sa tana ture shi tare da shigewa toilet tana sauke ajiyar zuciya. Sai kuma ta kalli kan ta a madubin.

"Wai me ke damuna?

Ta faɗa tana shafa fuskar ta, sai kuma ta zuba ruwa a fuskar. Ta fara cire kayan ta kenan taga mutum ya shigo, da sauri ta kare da rigar hannun nata.

"Meye haka?

"Naji kamar kin ce abokin Yaya zo ka min wanka".

"Kunnen ka ne, ni ban ce komai ba".

"Kin tabbata bakiyi magana ba?

"Ni ba abinda nace".

"To yanzu zuwan banza zanyi kenan?

Ya faɗa yana shigowa toilet ɗin. Marairace fuska tayi alamar ka fita mana.

"Wai mantawa kika yi sanda kina wanka a tsakar gida ne? Umma da Hajja na maki maganar ki dena wanka a tsakar gida? Kin tuna? Ko na tuno maki?

Juya masa baya tayi, tana gunguni, kawai jin mutum tayi a jikin ta yana zare rigar da ta rufe jikin ta dashi.

"Na shiga uku na".

"Me ya faru? Ba abinda kike so kenan ba?

"Abokin Yaya dan Allah kayi haƙuri. Allah bansakewa".

"Meye ba zaki sake ba".

"Abokin Yaya komai ma ba zan sake ba. Allah da gaske nake maka".

Ganin ƙwalla har ta taru a idan ta yasa shi barin ta, yana mamakin ta a yanzu komai kuka, da kuwa fa ? Ko da yake a yanzu zuciyar ta ta riga da tayi rauni, daman irin su ba su da jurar ɓacin rai baya idan suka rasa ya za suyi da abinda ke samun su. Bare kuma ita kan ta da bata san mene yake faruwa da ita ba.....



******Hauka ce kawai A. Madaki beyi ba, gashi yau a mota yazo ba jirgi ba, banda zulumi da zuciyar sa take yi ba abinda take yi. Idan aka auna shi zaka tabbatar da cewar jinin sa ya jima da hawa, zuciyar sa kuwa zata iya bugawa. A yadda yake jin sa ɗin nan. A Kaduna suka tsaya ya shiga companyn sa dake Kaduna, amma ga ɗumbin mamakin su suka ji wai anzo Z products ya zo ya saka sharen sa 80%. Tsabar takaici da haushi, bece da su komai ba ya juyo mota ya dawo.

Kenan haka yake da uwayen kuɗi? Amma aka masa ƙarya aka ce beda kuɗi? To shi kan sa waye? So yake kawai yayi arba dashi yaga ya san shi ko be san shi ba? Ya taba ganin sa ko be taɓa ganin sa ba.

Shafa kan sa yayi kawai yana rufe idan sa, dole ne zai tattaki domin ya je yaga wannan furnitures ɗin nasa, gashi ya riƙe magazine gam a hannu, duk da be duba ba, amma yasan zai lokacin sa ya duba.

Koda ya je gida su Musaddiq yaga ni ana zuba musu kayan su a boot za su tafi yawon buɗe ido sai yanzu aka yi settling tafiyar ta su. Ko ta kan su be bi ba ya wuce ciki. Yana shiga wurin drawern kuɗi ya buɗe yaga  saura bandir ɗin ƴan dubu ba su fi biyu ba. Tsabar takaici kallan drawern yake daga sama har ƙasa yana riƙe ƙugu, yaushe yaran nan suka kashe masa kuɗi har haka?



Continue Reading

You'll Also Like

301K 21.9K 26
Avantika Aadish Rajawat Aadi, with his fiery nature, adds intensity and excitement to their relationship, igniting a spark in Avni. Avni, like the ca...
31.4K 643 13
when every obstacle possible gets in the way of their love
125 57 17
Dhul-Hijja is one of the sacred months in the Islamic calendar. It has in it the 10 best days of the year.
1.6K 209 10
"Wallahi, I've fallen in love with you," he whispered, his eyes cast downward, his voice laced with vulnerability. "I've always had eyes for you." I...