ZARAHADDEEN

By hijjartAbdoul

1.6K 71 8

read and find out More

1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
16
15
18
19
20
21
22
23
24
25
26.
27
28
29
30
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42.
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52
53
54
55
56
57
58
59
60

31

24 1 0
By hijjartAbdoul

31

******Washegari yace za su tafi saboda zai je Anadyr jibi. Kawu Isubu yace kwana ɗaya gaskiya ta musu kaɗan, yace shi ya tafi ya bar musu su  Ameer, dan yaran akwai shiga rai. Ga shi ba ruwan su, musamman ta wajen abinci komai aka kawo musu ci suke babu tsarabar abinci ba komai, ruwa ma da yasa aka siyo musu pure leda leda, ko ɗaya babu wanda ya sha randa suka ringa buɗewa suna shan abinsu, kwata-kwata ba su nuna ƙyamar su ba. Abin ya yi musu daɗi ba kaɗan ba su kan su matan gidan matan su Kawu Isubu da Kawu Bala sun ji daɗin hakan matuƙa dan sun san sune suka tafka kuskuren da ba zai gyaru ba a lokacin da ba sa garin. Ƙiri suke hana mazanje su zuwa wai ba abinda za su je su ɗauko a ƙauye, sai gashi suma na su ƴaƴan sun tafi sun bar su ba da ziyartar su. Ba kuma wai kuɗi ko abin duniya za su ba su ba, dan suna da arzikin su dai-dai da gwargwadon da ba su nema sun rasa ba. Hasalima har kyautar wa suke, amma ka zo a gan ka ma ai daɗi ne da shi.

Washegari suka  haɗa kayan su, suma wannan kwana ɗaya nan ba ƙaramin daɗi yayi musu ba, sai murna suke yi ganin yarda kowa ke hada-hada da su ake yin nan nan da su, ga wani irin tattali da ake bawa Ameerah ganin tana dauke da juna biyu, aka ringa mai take so, yayin da ita kawai girkin yayar ta take so, amma haka ta daure ta ce musu komai ma, da aka kawo mata Ɗanmalele kuwa ta zage ta ci yayi mata daɗi a baki haka wainar filawa mai manja. Da za su tafi kuwa har ayi mata aka yi aka bata.

Mazan ne suka biya company  dan ƙara dubawa dakyau kafin su tafi, suka ga wani mutum na jiran su, yana ganin su ya ta so, suka gaisa cike da mutuntawa. Yake ce musu shifa wannan abin da aka bashi jiya be ishe shi ba da kuma wanda ya siya sai mutum ɗaya biyu aka yi.

Ameer da baya shiru yace, "Gidan marayu ka kai?

Sosai abin ya bawa mutumin dariya yace, "Wanne marayu kuma? Gidana de gidana".

"Kuma duk aka shanye naga Boot aka cika maka".

"Ina da iyali da yawa ai".

"Duka yaran ka ne? Matan ka hudu?

Dariya Ameer ya bashi yace, "Ehh mata na hudu, yarana hamsin da shida".

Ba Ameer da ake faɗawa ba, har Deeni sai da ya sake kallan sa bare su Taufiq da suka hangame baki suna kallan sa. Ameer kada haƙuri yayi yace.

"Kuma duka ka san su? Yaran naka?

"Nifa na haife su, ba zan san su ba".

"Nufina kowa ka gani kasan ya yake, kasan halin shi, kuma gida daya suke?

"Ya sunan ka nikam?

Cewar mutumin da'alama de babu ruwan sa da wani ne ai ba zai tsaya yana masa bayani ba.

"Zaid. Amma Ameer ake ce min".

"Zaidu zaka ce min, ina da Zaidu, ina da Ameer kuma yarda kake ɗin nan haka suma suke".

"Yauwa, wurin sa suna fa".

"Babu sunan da babu".

"Akwai Ziyada?

"Akwai mana".

"Sunan Ameerah ta ce".

"Zaid da Ziyada zan so itama nagan ta naga haka take?

"Laaa ina ruwan dunkum ni ba ruwana".

Taufiq yace, "Kuma suna aiki?

Kallan Deeni yayi da da'alam wata maganar suke mai muhimmancin da yasa ba su masa magana ba, suna daga gefe abin su, shima mutumin gajiya yayi ya samu kujera ya zauna suma su Taufiq suka nemo suka zauna.

Yace, "Me zan maku ne?

"Labarin gidan ka zaka cigaba da ba mu".

Murmushi yayi musu.

Yace, "Ashe zamu kwana mu yini anan, meya kuke san jin labarina?

Taufiq yace, "Haka kawai ni ina san nake jin labarin mutane. Ka sani ko littafi zan wallafa".

Jinjina kai kawai yayi yana kallon yaran cike da sha'awar su. Sun burge shi kuma sai suka haɗu da mutum mai sauƙin kai da ya biye musu shirmen su.

"Yi min magana da Ogan na ku".

Ya faɗa yana duba agogon hannun sa.

"Ka yi magana da ni kawai kai tsaye nine Chief Executive ɗin ai".

Taufiq yace, "Nine rabu da wannan. Me kake so".

"Assalamualaikum".

Cewar Deeni yana ƙara miƙa hannu suks gai sa. Sannan su Ameer suka wuce suka tafi wurin wani hallau da ya zo.

"Da farko sunana  Umar Babangida, anan Gumel nake, ni ɗan siyasa ne sannan kuma ɗan kasuwa. Ina da shaguna  a cikin wani garin na nan Jigawa. Na zo ne domin na siya kayan ku na gwada s shaguna sabo dana buɗe na drinks".

"Bansani ba ko bakwa sararwa".

Murmushi Deeni yayi yace, "Zamu so mu haɗa kasuwancin mu da kai".

Ya faɗa yana miƙa masa suka gaisa. Shima ya karɓa yana murmushi. Daga nan suka yi exchanging numbers da shi sannan ya haɗa shi da Moddibo yayin da Moddibo yace za'a kai masa duk inda yake so.

Ameer ya kalla shida da Taufiq yace, "Ina gayyatar ku bikin yarana, nan da wata uku zaku zo?

Taufiq yace, "Zamu zo ko Yaya?

Ya faɗa yana kallan Deeni, murmushi kawai Deeni yayi bece masa komai ba.

Ameer yace, "Idan kana so, muna album ɗin biki, muna abubuwa da yawa ga numbern mu".

Ya faɗa yana miƙa masa katin sa da na Taufiq karɓa yayi yana karata abun jikin kafin kawai ya jinjina kai yana ce musu za su yi waya. Sannan ya tafi yana mamaki wannan ahali, shi kam sun yi masa daɗi bisa ɗari tun jiya da ya kalle su, balle kuma da yaran sa suka ringa cewa abin yayi daɗi, idan suka ce yayi to yayi ɗin.

******Kasancewar yau za'a koma hutu yasa ta shiryawa kawai ta tafi abinta tare da tare Napep ta shiga, ko wurin su Umma bata je ta gaida su ba, dan jiya yini suka yi ita da Hajja suna mata zancen Deeni bawan Allah. Yayin da ita suke ɗaura mata laifi, shiyasa suma ta basu space bata koma ba da daddare ita kadai tayi kwanan ta a part ɗin ta. Sai da ta fito tayiwa Umma waya wai ita ta wuce.

Hajja da ita ɗauki wayar tace, "Kin cewa mijin ki yau zaki koma wajen aiki?

Haɗe rai tayi kamar tana ganin ta.

Tace, "Ai hutun daman kwana biyu ne ranar sallah da jiya".

"Kya sanar da shi ai, dan yau za su dawo fa".

"Tunda bansan tafiyar su be kamata nasan dawowar su ba".

Ta faɗa tana kashe wayar ta tare da hawa tsare napep. Idan ran ta yayi dubu to ya ɓaci, haka kawai wani can yake ɓata maka rai. Sanda ta zo babu wanda ya zo sai ita kadai sai a wurin na su, bata damu da cewar ita kaɗai ba ce ba, ta shiga aikin ta. Tana nan taga fitowar Ogan na su ya do so ta yana waya.

"Dan Allah nace ko zaki taimaka ki ɗauko mana hotan wani gida".

"Amma ai ba aiki na bane ba".

Ta faɗa kan ta tsaye cikin halin ko in kula.

"Ba wanda ya zo, kuma tun kafin sallah yake sanar dani. Dan Allah taimaka min, na masa alƙawari".

Sai da ta haɗe rai. Sannan tace, "Nifa ba zaka cuce ni ba, waya sani ma ko kashe ni zaka yi, ko s cutar da ni. Tunda ƙiri-ƙiri kun nuna bakwa so na".

Ta faɗa haɗe fuska tana cigaba da typing ɗin ta kamar ba abinda tace. Yayin kawai ya tsaya yana kallon ta, be taɓa tunanin hakan daga gare ta ba amma a yanzu ya tabbatar da waye ce ita, kasancewar ita kadai ce hope ɗin sa yasa shi cewa.

"Wallahi ba abinda zan maki, wannan aiki ne fa. Ki tafi da ke da drivern company sannan shi kuma drivern sa da ya aiko sai ya shiga gaba".

"Gaskiya ba zan iya ba".

Ajiyar zuciya ya sauke, wai shi da ke bada umarni ana bi ba tare da ance ƙala ba amma yau wannan yarinyar ke roƙa tana bauɗe masa.

"Kiyi haƙuri ba..."

Wayar shi da tayi ƙara ne yasa shi saurin ɗagawa jin kamar ana cewa zai sauya waje yasa ta cewa zata je. Har bakin ƙofa ya rakata.

"Idan na je me zan yi?

"Gidan zaki je ki gano, ki ɗauko komai da zai dace da gidan".

"Kuma duk ni ɗaya ce zan yi wannan?

"Daman duk mutum ɗaya ne ke yi ai. Kiyi haƙuri ke ɗaya ce kawai available kuma daga yau ne".

Zata yi magana kenan sai kuma tayi shiru ta shiga motar companyn na su yayin da drivern dake jiran ta kuma yace masa ya bi bayan ta. Sai de maikon gida wani waje taga sun yi da ita kamar military. Abin ne ya bata mamaki tana kallan drivern da suke bi yayi parking, haka ma drivern su shima ya sami waje yayi parking. Fitowa tayi tana rarraba ido ganin sojoji ta ko ina. Drivern ne ya fito ya mata jagora har hawan ƙarshe hawa na bakwai inda Sir ɗin nasa yake, sai de be shiga ba ya nuna mata ƙofa alamar ta shiga.

"Me zan yi anan?

"Sir yana ciki ya san da zuwan ki".

"To kai meye na tsayawa anan?

"Anan nake tsayawa".

Ganin yarda ya ƙame tayi. A ranta tace 'wahala' kafin a fili.

Tace, "Nace shi Sir ɗin na ka musulmi ne? Naga kai kamar ƙedari".

Dariya ta bashi amma be yi ba ya dake.

Yace, "Ehh, nima kuma musulmi ne".

"Awwto".

Ta faɗa tana ƙara kallan sa, kafin ta sa hannu ta murɗa handle ɗin ƙofar tana yin Bismillah, sai de kuma wasu ƙartan sojojin ta gani sun yi layi a wurin wata ƙofar, yayin da sojan farko ya mata da alamar ta wuce da hannun sa. Ba musu ta bi su da ido kowannen su tana kallan su ita ta dariya suke bata kawai su kafa ƙamewa. Tana zuwa wurin ƙofar, ƙofar ta buɗe ta shiga haɗaɗɗan offer ɗin mai kyau da tsari, baƙaramin yi mata kyau yayi ba office ɗin ba, har bata san ta tsaya tana kallan office ɗin ba, kafin ta zagayo da kallan ta g mutumin dake zaune yana typing a system da duka hannyen sa, yayin da ya duƙufa ga abinda yake yi.

Cak ƙwaƙwalwar ta ta dena motsi yayin da zuciyar ta, ta dena aiki banda kallan mutumin babu abinda take yi. Domin ganin sa take yi tamkar Abban su Deeni da ya rasu, sai de wannan ya fi hasken fata banda wannan bata ga abinda da ya bambanta ta su ba. Ta jima tana kallan mutumin yayin da shi kuma ya ji shirun yayi yawa hakan yasa shi  ɗagowa yana kallan ta..

"Ya ilahi".

Ta faɗa can ƙasan maƙoshin ta ganin irin zallar kwarjinin da yake da shi, da kuma cikar haiba da zati, da ya sakar mata murmushi kuwa sai take ganin kamar su Deeni da Zarah da Sadiq ne suka yi mata murmushin. Sai da ta nemi ta faɗi ta ji ta ɗan jingina da kujera ta dafe ta, tana ƙoƙarin zama.

"Lafiya?

To muryan ce kuma irin ta Abba. Sai ta nutsuwar ta tayi tana ƙaƙalo murmushin da bata shirya masa ba, tare da ɗaga kai kawai. Nuna mata wajen zama yayi.

"Please yi hakuri, ɗan jirani urgent abu nake yi".

Ɗan murmushi tayi masa tana satar kallan sa. Shi kuma ya jinjina kai sannan ya ce. Nagode. Sai da ga gama kallan sa tsaf sannan ta cigaba da kallan haɗaɗɗen office ɗin da ya tsari ta ko ina. Akan table ɗin sa ta tsayar da idan ta tana kallan yarinyar da matar dake jikin hotan da kuma shi. Ƙura mata ido tayi tana san tuno inda tasan matar nan amma ta manta, yayin da ta kalli hotan Ishaq da Yaya Bilk suma a gefe guda da Ahmad a tsakiyar su. Sai ya zamana ta kalli wannan ta juya ta kalli wannan, ta ma rasa wanne zata kalla daga cikin su, dukan su tana so ta tuno inda ta san fuskar su. Bata taɓa jin haushin saurin mata mutane ba irin yau.

"Kin san su ne?

Cewar sa yana rufe system ɗin sa ganin irin dafe kan da tayi tana murza goshi. Ɗagowa tayi tana ɗan murmusawa ganin shima murmushin yake yi.

"Kamar nasan wannan yarinyar".

"A'ina?

Cewar sa yana kallon ta, kafin ya sakar mata wani murmushin.

"Na manta inda na san ta".

Ta faɗa calmly tana saukar da kan ta ƙasa, ta fara wasa da hannun ta. Cike da nutsuwa ya fara sanar da ita yanayin gidan nasa da abinda yake so ayi masa, itama ture duk wani abu tayi ta fuskance shi suka yi zancen aikin su, cike da ƙwarewa take masa bayanin komai. Tace ba zai iyu ba kuma,  sai anje gidan ya angono sun ɗauko komai sannan za su ga wanne irin kaya ya dace da a sawa gidan bayan sun ga tsarin gidan. Cike da gamsuwa ya amsa mata tare da kiran wayar yace za su fita.

Barshi tayi yayi gaba yayin da shi kuma ya tsaya suka jera da ita, suna fitowa taga ana sara masa, kawai a fakaice ta bi su da ido daga shi har sojojin nasa, yarda ya murtuke fuska kai ka ce ba shi ne ya gama mata dariya ba a ciki. Suna zuwa suka ga motocin an fito da su an kawo su bakin building ɗin waje tare da buɗe masa mota, ita kuma tayi ƙiƙam a tsaye tana kallan ikon Allah. Nuna mata yayi alamar ta shiga, yayin da wani soja ya je ya buɗe masa ɗayan ɓarin yana zagayawa da shi. Sai da ya shigo ya zauna sannan ta lura da tag ɗin dake jikin rigar sa ta sunan sa. M.K.M kawai aka sa a jiki sai rigar dake nuna cewar mutum babba ne sosai a harkar soja. Jinjina kai kawai tayi tana ɗauke kan ta daga gare shi dan sosai mutumin ke mata wani irin kwarjini. Ko da bata saba ganin sojoji ba ne ba oho.

Har suka isa gidan su, wai ita ce da tarin sojoji ana tafiya da ita a cikin mota, wani iri take ji baya idan ta kalli gaban su, ta juya ta kalli baya duka motoci ne kuma duka na su ne. Har suka isa da tunanin dake ran ta, nan gidan ma de sojojin ne ta ko ina birjik. Aka yi parking suka fito tana kallan gidan,tsarin sa da yana yin sa sun yi mata kyau, sai de babu filayoyi a gidan. Inda ya dosa itama ta do sa sallama yayi tare da shigowa.

Wata dattijuwar mata ce a zaune a ƙasa tana zaune tana karatun Qur'an yayin da Najwa ke zaune itama kusa da ita da'alama ita ake ƙarawa karatun, sallamar ta sun ce ta katse musu abinda suke yi.

"Yayya sannu da gida".

Ya faɗa yana zame takalmin ƙafar sa, yana zama a kan carpet ɗin shima, ita kuwa daman Hafsah tun a ƙofa ta cire nata ita kuma a kusa da Najma ta zauna.

"Yau sannu da dawowa. Ya aikin?

Ajiyar zuciya ya sauke yana faɗin Alhamdulillah.

"Ina wuni?

Cewar Hafsah tana ɗan kallan matar. Yayin da Najwa ta gaida ta. Tana komawa wurin Baban ta, ta lafe a jikin sa.

"Lafiya Ƙalau ƴar nan. Har wuni ne Ya gida?

"Alhamdulillah".

"Masha Allah".

"Kun gama karatun ne?

Ya faɗa yana kallan ƴar ta sa. Turo baki tayi cike da shagwaɓa tace, "To ba faɗa take min ba".

"Ba dole na yi maki faɗa ba? Duka zan fara miki".

"Kana ji Abba ko?

"To kiyi haƙuri".

Ya faɗa yana ajje ta a gefen shi, shi kuma ya tashi da kan sa ya kawo mata ruwa da abin motsa baki sannan ya wuce wani corridor da'alama hanyar ɗaki ce.

Yayya ta dubi Hafsah tace, "Daga ina?

"Daga company na zo ne zan ga gidan domin muga wanne irin kayan ɗaki ne za su dace da gidan".

"Kuma mata da yin kayan ɗakin?

Murmushi Hafsah tayi, tace, "A'a, mu kawai aikin mu, zuwa muga gidan muje mu kai bayanin abinda gidan yake buƙata daga baya kuma sai azo a sa".

"Ayyto ai na ɗauka mata ne ke yi nace ohh Allah ya kawo zamanin da mata aka fara aikin ƙarfi kuma".

Murmushi kawai Hafsah tayi tana satar kallan matar.

"Allah kuwa ƴar nan, nan fa aka kawo mana mata ƴan sanda....

"Yayya sojoji ne fa ba ƴan sanda ba".

"Ke gidan ku, duka ba sunan su de masu ɗamara ba, bana san iya shege ɗaga min cinya ta, ba zai iyu ba na rene ki na reni uban ki, ɗaga ni".

Tashi tana tura baki ta wuce, ɗakin dake parlour ta bango ƙofar.

"Idan kika ɓata uban ki ne zai yi kisan kuɗi ba ni ba. Yarinya duk abin an sangarta ta da ɓaci da taɓara".

"Ai yarinya ce".

Cewar Hafsah.

"Haka ake kafewa da cewar yarinya ce, amma ta iya fitina iri-iri, uwar ta sai faɗan banza da wofi amma ba za'a bawa yarinya kyakyar kulawa ba, shiyasa fa ni bana san zaman gidan nan gashi an kawo ni an ajje ni ina musu reno".

"Zata dena".

"Nan aka dake ta yarinyar ta zo ta tadawa kowa hankali a gidan nan, uwar ta, ta ringa bala'i an taɓa ƴar gwal. Tace ba zata yarda ba sai ta je makarantar".

"Allah nake faɗa maki sai gashi ta je ta dawo ta haɗu da wacce ta fita masifa da bala'i".

Kallan Yayyar tayi tana tuna abinda ya faru, tabbas anan ta san Maman da kuma Ƴar.

"Suma basa kyautawa".

"Kamar ya ba da kyautawa? Kin taɓa ganin inda aka doki mutum be yi komai ba? Nace kin taɓa ganin inda ake daki mutum be yi komai ba?

Murmushi Hafsah tayi tana gyara zaman ta. Tace, "Ana duka amma ba irin wannan yaran ba, kuma ko dukan za'a musu ba'a irin wannan dukan na rashin hankali ba. Su fa yara jan su ake a jiki a san me suke buƙata, me su ke so? Aga wanne irin method za'a yi amfani da shi wajen koyar da su".

"Haka ne?

Cewar Yayya tana kallan Hafsah, dan murmushi ta sake yi. Tace, "Turawa sun ce, yara shekara 1 zuwa 7 basa yin laifi....

"Inji uban wa?

Ta faɗa tare da saurin zabura harda ɗan matsawa dan ta kalle ta dakyau, dariyar da bata shirya ba ce ta ƙwace mata, tana ɗan rufe bakin ta.

"Kin fara ko?

Cewar sa yana zama kusan da Babar sa.

"Me na fara? Ni ƙarya ce bana so".

Yace, "Me aka ce na ƙarya?

"Gata nan ta faɗa maka, danni ba zan saurari ƙaryar da nasan ƙarya bace ba, wai turawa sun ce wai yara shekara nawa zuwa nawa wai basa laifi. Tsabar ƙarya".

Maman Najma ce da fitowar ta kenan tace, "Laaa Maman Sabir ke ce?

Da mamaki take kallan ta, kafin ta kalle shi sai kawai tayi murmushi tana zama a kusa da ita.

"Ina wuni".

"Lafiya Ya Sabir, Yayya ita wacce nake na baki labari".

"Kullum kike bani labari de, ai ba denawa kika yi ba, ɗazu ma sai da kika bani labarin. Kinga yarinyar nan ba ranar da zata zo ta wuce bata ce Maman Sabir ba".

Murmushi Hafsah tayi. Yayin da Yayya tace, "Ashe kece, ehh dole ki yi ƙoƙarin ɗaurawa Malama laifi mana".

Tana ɗan dariya tace,"Wallahi ba haka ba ne ba,su ba laifi suka yi ba, wai ba sa da saurin ɗaukan karatu kuma suka yi bacci, idan daman ba ta so mugunta ba, taga yara sun yi bacci to ta bar su mana su huta, amma ta dake su".

Maman Najma tace, "Iya duka?  Harda up and down ta sa su ko frog jumb ne bansani ba, amma cinyar ta ta fi sati tana mata ciwo".

"Har da su zuwa asibiti".

Cewar Yayya tana kwaɓe baki.

"Ai shi Sabir ko me za'a masa ba zai faɗa ba, badan Allah yasa na gani ba da shikenan ta daki banza".

Kallan ta kawai Major. K ke yi yana mamakin ta.

"Wallahi fa, haifar su mukayi ba'a ruwa muka sha ba".

Yace, "To meye dan a doki yaron ka, be dace ace kaje ka ci masa mutuncin ba a gaban ɗaliban sa, hakan kamar cin fuska ne da nema rena malami". 

"Be kama ta, amma suma Malaman ya  kamata ace sun ja yaran a jikin su, sun yi motivating ɗin su, sun fahimci su waye yaran, ba wai ake koyar da yara saƙaƙa kawai ba da ka".

"Hala Education kika yi?

Cewar sa yana kallan ta, jinjina masa kai kawai tayi.

"Kuma kika ƙare a company?

"To ya zan yi? Anan nayi service ma".

"Meyasa?

"Haka Baban mu yake so".

"Ai da kin yi abinda kike so ba wai abinda yake so ba".

Murmushi tayi kawai bata ce komai ba. Yayin da Maman Najma.

Tace, "Ina Sabir?

Ta manta da ba sa nan sai kawai tace.

"Yana gida".

"Ki kira ƴar ki yanzu haka ɓarna take min, tayi shiru ita kaɗai".

"Najma zo ki gai sa da Maman Sabir".

Fitowa tayi tana cewa na gashe da ita.

"Baki tambayi Sabir ba".

Cewar Maman nata.

"Ina Sabir".

Ta faɗa tana kwanciya a cinyar Yayya.

"Yana gida. Zaki je ki gan shi ?

Kallan iyayen nata tayi. Tace, "Ai Abbana ba zai bari ba".

"Zai bari, idan muka tafi zuwa yamma sai na dawo dake ko?

Kallan Abban nata tayi.

Maman Najma tace,"Idan zaki tafi sai ki tafi da ita".

Kallan ta Yayya tayi bata ce komai ba, yayin da ita kuma Najma ke murnar zata je gidan su Sabir. Sosai suka ja Hafsah da hira itama ta sake a cikin su sai hira suke abin su, ita kan ta mamakin kan ta ne ya kamata, haka kawai ta ji duk wani damuwa dake ran ta ya wanye, gashi de Soja ne kuma babba ne da shi. Amma ace Najma ce kawai ƴar sa. Ga kuma yarda ya ware suke zance da ita kamar sa can sun san ta. Sai da zata je taga ɗayan part ɗin na su da aka gama shi wanda za'a sa masa kayan.

Yayya tace, "Ƴar nan ya sunan ki?

Murmushi tayi tace, "Hafsah".

"Ahh ki ce ansai ce kenan, na iya kiran ki da Babar Sabirun ko

Najma tace, "Ba Sabiru ake cewa ba Sabir ake cewa".

"Uwar fi'ili".

"Babar Sabiru, kina ji ko? A parlour na da ɗakina ki saka min kayan irin namu na tsoffi".

Tana dariya tace, "To in sha Allah zan sa maki".

"Yauwa akwai ki da sauƙin kai. Ni ban yarda ke kika yi abinda aka zo ake sanar da ni ba".

Major Kabir yace, "Yayya masu faɗa suna da kama ne?

Daga haka haka suka fice daga part ɗin. Suka kai ta, suka nuna mata ko ina da ina na cikin ɗakin, har ɗakin Najma dake cikin ɗakin Yayya aka nuna mata. Sannan tayi wa Yayya sallama suka tafi tare da Najma aka haɗa ta da drivern da zai kai ta. Sannan suka yi exchanging numbers da Maman Najma.

Kallan Major Kabir Maman Najma tayi bayan sun dawo.

Tace, "Baka ga irin kallan da take maka ba kamar ta san ka".

Kallan ta Yayya tayi bata ce komai ba. Yana ɗaukan abinda bata taɓa ba wanda ya kawo mata.

Yace, "Sai kinga yarda tayi ma sanda ta ganni shiyasa na bata lokaci ta gama kallo na sosai".

Yayya tace, "Gaskiya ne, wataƙila tasan Kabiru".

Ta faɗa idan ta yana cikowa da hawaye.

"Yayya waye Kabiru?

"Yayan ka ne".

"Yaya na kuma?

Ya faɗa cike da mamaki tare da saukowa ƙasa inda take ya zauna.

Yace, "Yayya daman ina da Yaya? Daman bani ɗaya kika haifa ba?

Sosai ta ji wani irin kewar ɗan nata na taso mata, kukan da take dannewa n shekara da shekaru shine ya ƙwace mata a yanzu take kwarara abinta tana sharewa da ƙasan zanin ta banda  gyaɗa masa kai babu abinda take yi, tana tuno dukkan abinda ya faru a baya.

*******Ba gida suka wuce ba, sai da suka je company ta bada duk wani abu da ya dace da gidan da kuma tsarin gidan suke so abun na su ya kasance, sannan aka masa message akan nan da sati biyu za'a yi komai. Ta ɗauki lokaci hakan yasa sai da tayi sallahn La'asar sannan taje ta ɗauko Najma da tayi bacci ta kwantar da ita a office a ɗin sa, tukunna suka wuce gida. Tana zuwa tagan su sun dawo, drivern ta kalla tace masa ya da daddare ya maida ita tunda yaga gidan, cike da girmama ya amsa masa, a kafaɗar ta ta saɓeta ta fita daga motar.

Da sallamar ta shiga parlourn, dukan su suna zaune ansaka HDMI a system suna hotunan da Videon wurin bude companyn a TV. Kowa na kalla ga kuma fresh milk da Yoghurt nan kowa na sha, da'alama sun jima da dawowa ganin kaya ko ina an ajje.

Da gudu Sabir ya zo ya tare ta. Yana murnar ganin ta, tana murmushi sosai.

Tace, "Sabir albishrinka".

Dukan su kallan ta suke, ba za su iya cewa basu taɓa ganin ta cikin wannan matsanancin farin cikin ba idan ba yau ba daman idan kaga dariyar ta ita da ɗan ta Sabir ne, hakan yasa dukan su zuba mata ido suna kallan ta, yayin da Deeni kawai kallan yarinyar da ke kafaɗar ta ya yi tare da mata kallo ɗaya, yayi murmushi a ran sa kawai ya tashi daga wajen.

"Anty goro".

Ya faɗa zai leƙa fuskar Najma. Dawo da shi gaba tayi tana dariya.

Tace, "ka tsaya anan, ka rufe idan ka. Fari ko Ja?

"Ja? Fari? Wanne zance?

Ameer yace, "Ka ce fari".

"Fari tas".

"Ai baka rufe idan naka ba".

Kulle idan yayi, tana cewa da Ameer ya matsa zata kwantar da yarinya, ana kwantar da ita tana tashi zaune tare da kallan mutanen da suka zubo mata ido duk suna kallon ta tare da mamaki waye ce wannan ɗin da Anty ba san yara ba take. Har ta ta sauke shi akan Sabir da shima ya buɗe idan sa akan ta, a tare suka sake wa junan su dariya kowa na kallan kowa.

"Yau na zo gidan ku, kai ka zo gidan mu".

Abinda ta fara faɗa kenan, yayin da Sabir dake murna sosai yace zai zo. Daga nan ya fara nuna mata kowa, yayin da kowa kawai kallan sa yake, dan tunda aka shi a makarantar nan sanda Najma ta zo ya ringa damun su da yayi ƙawa ƴar seat ɗin sa, waye waye suka ringa masa jaraba ya dame su da wata Najma, to yau ga Najma ta zo har gida sun ganta. Yayin da ita kuma duk wanda aka nuna mata sai ɗan sunkuya ta gaida shi, har aka wajen Baba suka je ta gaida shi.

"To shi baya magana".

Cewar Najma tana kallan Baba.

"Ya dena magana zo muje".

Ya faɗa yana jan hannunta, yayin da Hafsah kawai ta bishi da ido, itama tana jin daɗi a ran ta. Da murmushin dake kan fuskar ta ta shiga ɗaki tare da zuge hijabin tana sauke ajiyar zuciya, naɗe hajabin tayi tana zama akan sofa sam bata lura da shi ba da tun shigowar ta yake kallan ta. Har zaman ta a kan kujera, shi kuma yana wajen kujerun sa yana shirye shiryen tafiyar sa da zai yi gobe.

Ribbon ɗin dake kan ta cire tana baja gashinta alamar ya dame ta ɗin nan. Sannan ta tashi ta shiga toilet ta fito ta sauya kaya, duk bata lura da shi ba, sai da ta gama.

Yace,"Baki iya sannu da zuwa ba?

Murmushi tayi masa kawai tana ɗauke kan ta.

Tace, "Matar so ce ke wannan ba matar da ba'a so ba".

Ta faɗa tana zura hula a akan sakakkiyar doguwar rigar ta, ta fice ta bar masa ɗakin, abinci taje ta zuba ta buɗe Fridge taga yadda aka cika musu shi da Yoghurt da Fresh milk. Duk san ta dashi, da kuma duk son ta sha Yoghurt haka ta haƙura ta bata sha ba, kawai ta ɗauki lemu ta koma parlour, anan taga shima ya fito, sun gama kallan an koma kallan hotunan da suka ɗauko daga ƙauye. Sai su kawai a parlourn Baba da Umma sai zuwa jimawa za ta fitar da Baba dan shan iska. Ana ta kallan hotunan ana cin dariya. Idan ba'a gane waye ba sai a kawo Deeni yace wane ne wani kuma yace ya manta.

Hafiz ne yace, "Gaskiya Kawu Bala ya haɗa ku da aiki da ya baku wannan hotunan".

Taufiq yace, "Hotunan ne abin dariya, kaga Yaya Sadiq kuwa?

Sadiq yace, "Daman da gangan ya haɗa ku da shi".

Hotan Mama da Ummi aka ɗauko sanda aka haifi Sadiq. Zarah ta ɗauko ta nunawa Deeeni.

Tace,"Yaaa waye ce wannan me kama dani?

Sadiq yace, "Matar Abba ce baki san ta ba".

Ameer yace, "Matan Abba biyu ne daman?

"Ehh biyu ne".

Cewar Sadiq. Hafiz yace, "Irin kana da wayon nan ka san ta ko?

Yace, "Nasan ta mana, ita ce Maman Deeni da ke".

Kallan sa Deeni tayi jikin ta na yin sanyi tace, "Yaa wai?

Lumshe mata ido yayi cike da tabbatarwa kafin yace, "Kiyi haƙuri".

Murmushi tayi tana ɗan kwanciya akan kafaɗar sa.

Tace, "Kawai de addu'a ce bana yi mata amma yanzu zan yi ko?

Jinjina mata kai yayi. Sadiq yace, "Mama ba irin Ummi ba ce ba, Mama akwai san yara tayi ta goya ni ina kamar Sabir ɗin nan lokacin ko?

Ya faɗa yana kallan Deeni murmushi kawai Deeni yayi.

Hafiz yace, "Muma fa Baba ya taɓa yin wani auren sanda muna Kebbi".

"Hajiye zaki tuna?

"Nanni ko?

"Ita de, matar nan tayi gashi ba ruwan ta".

Tace, "Sunan kawai zan iya tunawa Yaya amma na manta ta".

Deeni kallan Hafiz yayi.

Yace, "Kuma tana ina? Rasuwa tayi?

Girgiza kan sa Hafiz yayi.

Yace, "Ba ɗaya kawai rabuwa suka yi ina tunanin dan rana ɗaya kawai tace tafiya zatayi lokacin da Baba baya da kuɗi".

Tace, "Haka zaka ce lokacin da azzalumin mutumim nan ya ƙwace wa Baba kuɗin sa".

Kallan Hafsah Deeni yayi sannan ya kalli Hafiz dake ba su labarin ta.  Zarah dake kan ka faɗar sa ya sauke, sannan ya tashi ya je gaban, Hafsah ya tsugunna ya ajje plate ɗin abincin da take ci, ya rufe duka hannyen ta, tare da sa idan sa a cikin ta. Yayin da suke kallan sa kawai, ita kan ta tsayawa tayi tana kallan sa.

Calmly yace, "Paris: Charles de Gaulle (CDG) Airport. Mun hau jirgi zuwa Anadyr, sanda zaki jewa Baba aiki. Wata mata ta zauna a kusa da ke, kin tuna? Sunan ɗan ta Ahmad kin tuna ta? Yaro mai kuka".

Shiru tayi tana kallan sa, kafin ta gyaɗa masa kai.

"Kun yi exchange ɗin number ko?

Ƙara gyaɗa masa kai tayi.

"Kin yi saving?

Gyaɗa masa kai ta kuma yi.

Yace, "Me kika sa?

"Na manta".

Ta faɗa tana so ta tuno abinda ta sa amma ta manta.

"Ba Maman Ahmad kika saba?

"Dan Allah ki tuna".

Girgiza kan ta ta fara yi, yana cewa ta tuna, ganin ba zata iya tunawa ba.

Yace, "Ina wayar ki?

"Tana ɗaki".

Da mamaki suka bi shi da kallo ganin duk suna kallan ta. Sai gashi da wayar ya dawo ya sami numbern. Danna mata kira yayi yana zama a kusa da ita, ita kuma ta ɗan matsa masa dan kujerar ta mutum ɗaya ce. Tana shiga ya sa a speaker yana cewa kar wanda yayi Magana.

"Assalamualaikum".

Aka amsa daga can, yayin da ta kalli Deeni dake riƙe da wayar, ya nuna mata alamar tayi magana, sai a nan ya ga ba'a Nigeria take ba amma numbern kuma ta Nigeria ce.

"Walaikumussalam".

Ta faɗa, tana sake kallan shi. Shi kuma ya raɗa mata me zata ce. Sai da ta maka masa harara sannan tayi yadda yace ɗin, bayan sun gaisa.

"Hafsah ce, wacce kuka haɗu a jirgi har kika sauka a Belgium kin tuna?

Ji tayi matar na yin dariyar farin ciki.

Tace, "Hafsah?

"Sai yau? Kin san sau nawa ina jiran kiran ki? Waya ta ce na mance da ita a airport a wancan ranar, saboda ke kawai nayi welcoming na layi na".

Kallan shi tayi alamar me zata ce.

"Yanzu kina ina?

"Nigeria, Kano".

"Zan shigo Kano, duk sanda na zo zan kira ki".

"Nagode".

"Hafsah nice da godiya".

Daga haka ya kashe.

Hafiz yace, "Kasan matar ne?

Yace, "A'a, amma ita tana zargin Hafsah da ta san ta, ko kuma a dalilin ta zata haɗu da Baba".

"Kana nufin ita ce Nanni ɗin?

"Ko shakka bana yi Hafiz, ita ce, dan tabbas ta san Hafsah dan har tayi bacci tana juyowa tana kallan ta, harta tawadar dake tafin hannun ta sai da ta buɗe ta kalla, dan ta tabbatar da abinda take zargin gaskiya ne".

"Meyasa take neman Baba".

Umma dake bakin ƙofar ɗakin su, ta ƙaraso tace, "Domin ta ga ƴar ta take neman sa".

"Ƴar ta kuma?

Jinjina kai tayi. Tace, "Tabbas, ta tafi da tsohon ciki a jikin ta, wanda tun kafin ta tafi ta fara labour a tafiye, ita ce haihuwar ta farko, hankali na be kwanta da ita ba, sai na bi bayan ta batare da sanin su Baban ku, sanda na bita naga motar Daddyn ku a wajen ya ja ta jejin dake gefen mu, da shi da matar sa".

"Akan ido na, suka tafi da jakar ta da kuma da jaririyar yarinyar, hakan yasa ta na ƙarasa na taimaka mata. Tace da ni na kula mata da ƴar ta da ta haifa kuma na karɓe ta daga hannunsa domin ya kwashe mata dukkan kadarar ta. Zata dawo duk daren daɗewa domin Baban ta ta fi shi san kuɗin sa".

Kowa shiru yayi yana jin Umma dake bayanin nan.

"Sai gashi muma mun tashi, Baban ku har yau be san cewa Maryam ita ce ƴar sa ba, haka nan nima ban sanar da shi ba, har yau idan nace zan yi masa zancen ta sai yace baya so, gani yake ita ce ta raba shi da kowa nasa".

Kowa shiru suka yi suna jinjinawa wannan rashin mutunci irin na mutumin nan, yayin da Baba idan sa yayi ja ya kasa tuna komai dan danan ya fara ƙoƙarin saukowa ya faɗi ƙarar da suka ji ne yasa su, zuwa wurin sa suna kiran sunan sa.....

Continue Reading

You'll Also Like

246K 2.7K 75
*COMPLETED* Short imagines about Harry Styles! ( Some of these are from tumblr, giving them full credits.) •FLUFF/CUTE IMAGINES •NO SMUT
2.2K 301 16
Afnan is an introvert, shy clumsy girl who see the good in every one, she's not the perfect girl with the perfect body she has too many imperfections...
444K 17.7K 48
Vikram, a senior officer, prioritizes his duty above all else, much like his father, ACP Rajendra. He has three siblings: one is an officer, and the...
15.3K 1.1K 47
Unrequited love. When a patient person reaches his limits what happens? He explodes. The true color of this wicked world and cruel life shows. When t...