ZARAHADDEEN

By hijjartAbdoul

3.2K 81 8

read and find out More

1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
16
15
18
19
20
21
22
23
24
25
26.
27
28
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42.
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52
53
54
55
56
57
58
59
60

29

48 1 0
By hijjartAbdoul

29

********Sun shafe fiye da minti talatin kowa na kai kawo a zuciyar sa, yayin da wasu daga cikin ƙananan ma'aikatan wanda ba su damu da abinda ake yi ba suke darewa ɗaya bayan ɗaya, domin ba su da ta cewa, dalilan kiran meeting ɗin gaggawar ma ba'a yi ba. Suka fara wani abun daban. Yayin da Hafsah take s tsaye har yanzun bata motsa ba, kawai bin su da ido take yi, so suke ta fice ta ba su waje, suyi yarda suka ga dama da Deeni dan sai abinda suka ce masa, amma ta kafa ta tsare bata bada duk wannan damar ba. Shi kuma Deeni babu wani abu da yake tunani sama da labarin da Maman su Mu'azzam ta bayar.

Ganin babu wanda yayi magana yasa Hafsah cewa.

"Idan kun amince da abinda na zo da shi shikenan, idan baku amince ba kuma yau a kuma yanzun nan zamu tattara yana mu yana mu, mu bar maku companyn nan".

"Wanne abu?

Babban Directorn company ya faɗa yana kallan ta.

"Zai zama Director bayan ya je ya dawo. Salaryn sa ya tashi daga 30k zuwa 250k".

Kallan kallo aka fara tsakanin su, suna mamakin wannan yarinyar, yayin da Deeni ya ɗago ya kalle ta da tarin mugun mamakin dake kan fuskar sa, amma sai de babu wanda ya lura da hakan har ita uwar gayyar bata gane meye akan fuskar sa ba, kawai de tasan yana mata wani kalar kallo da idan ta kalle shi zata kasa yin komai. Koma ta fice a wajen.

"Muna da buƙatar yin tunani".

"Duk wani tunani kuyi shi anan, babu wanda zai fita".

"Ke fa ƙaramar ma'aikaciya ce, dan haka ki ja bakin ki, kiyi shiru. Baya ga haka ke baki da kunya ne? Duka nan bamu girme ki ba? Wasu ma sun haife ki".

Murmushi tayi mai kyau, tana komawa wajen projectern ta tsaya tana naɗe hannun ta.

Tace, "Bana jin kun haife ni, domin wanda ya haife ni ba zai yi irin abinda kuke yi ba. Dan haka kar nake ganin ku, marasa mutunci kawai".

Wani Inyamuri ne ya tashi yace, "Bana jin ta faɗi ko tayi ba dai-dai ba, laifi ne, kuma hakan abin yake, a yanzu mu kuke so, dole mune a ƙasa. Idan kuka yi duba da irin abinda Ya samo mana zuwan sa Anadyr nasara ce babbar Nasara muka yi, kuma duba da shi suke da buƙatar gani ba mu ba, dole shi ɗin ne zai je domin nasarar mu".

"Maganar ka gaskiya ce, dan kuwa ko idan Oga Deeni ya tafi bamu da wanda ya fishi har yanzu a companyn nan namu".

Cewar wani shima yana faɗar ra'ayin sa. Ita de taɓe baki tayi.

Tace, "Daga baya kenan".

Ta faɗa tana takowa wajen sa, kallon ta yayi kawai yaga me zatayi, biron dake gaba rigar sa ta cire ta miƙa masa.

"Sa hannu".

Kallan ta yayi alamar me? Ita kuma ta haɗe fuska tamau, tana tsuke baki alamar ko wanne lokaci zata iya fashewa ta gasa masa magana, hakan yasa shi yin signing babu musu, ta je wajen Mu'azzam shima ya saka hannu. Sannan itama ta zo ya saka hannu a nata takardar, ta mayar masa da biron sa inda ta ɗauka, zata koma kenan ta ji ya riƙe hannun ta, cak ta tsaya tana addu'a cikin ran ta Allah yasa ba dizgata zai yi ba, su de jama'a kallo ne na su kawai. Juyowa tayi a hankali tana ƙara tsuke baki, wani ɓoyayyan murmushi yayi yana sunkuyo da ita ya gyara mata hijabin ta da ya zame, ana ganin sumar ta. Dan shima ji yayi ya kasa daurewa kowa na kallan fuskar ta, hakan yasa shi gyarawa dan sai yake ganin yarda yake ganin sumar kan ta haka ma kowa ke gani, haka yarda ya masa kyau sai yaga kamar yayi duk sauran jama'ar kyau.

Sakin hannun ta yayi tana wucewa wajen projectern nan ta maƙala papers ɗin a  cikin board ɗin dake wajen.

"Ko da zaku sauya shawara, muma a shirye muke da mu sauya ta mu shawarar".

"Mu tafi ko?

Ta faɗa tana kallan Deeni, sai da ya gama kallan kowa har su Aisha dake zaune suna kallan ikon Allah, su ga zai tashi ko ba zai tashin ba, ba su gama tunani ba sai gani suka yi ya miƙe ya tattara file ɗin sa yayi gaba.

"Kai kuma fa?

Ta faɗa tana kallan Mu'azzam, shima tashin yayi ya bi bayan Deeni.

"Ya aka yi kika san wannan?

Cewar Kawun Aisha, juyowa tayi ta kalle shi.

Tace, "Bana jin idan mutane biyu suka yi magana suke tunanin babu wanda zai ji, ko ya ji wannan maganar. Bare kuma maganar da aka yi ta ba mutum ɗaya ba, ba mutum biyu ba, ba kuma uku ba. Ita magana wanda ake tunanin be ji ba, shine yaji ta. Kawai ana ji ne ayi kamar ba'a ji ba".

"Me kike nufi?

Murmushin takaici tayi, tana kafe shi da wannan idan ta nata Masha Allah da su.

Tace, "Abinda nake nufi, bango ma yana iya faɗar munafurci".

Tayi masa wani banza kallo ta wuce, baki a sake suke kallan ta, yayin suka sallami sauran da ba su tafi ba kowa ya kama gabansa.

Su Aisha kam da sauran ma'aikatan da ake gulma, waje suka samu suka zauna ake gulmar Hafsah da Deeni, duk a tunanin su bata jin su, ita kuwa sarai tana jin su, ko Mu'azzam dake gefe da ita shima yana iya jiyowa, ya na so ya mata magana amma tsoron ta yake ji, shiyasa ya zaɓi da yayi shiru kawai yayi abinda yake gaban sa.

Zainab ce tace da Aisha, "Kinga ki haƙura da shi, dan wallahi da'alama mijin tace ne. Kada ki kuskura kiyi wannan kuskuren shiga gidansa".

Khadijah tace, "Abinda nake jiye maki kenan, kiga de ranar ta je ta janyo shi kamar wani ɗan ta, shi kuma abin haushin zungui-zungui yana binta baya. Yanzu ma fa kiga sai abinda tace masa yake yi".

Shiru Aisha tayi tace, "Kin san kuma akwai sanda ya zo gidan mu, ba nace muku ya zo ba? To beci komai ba, wai Madam ta hana shi ci".

Ita Hafsah dake jin su sai tayi tunanin Madam Hafsah da yake faɗa, yayin da gefe ɗaya kuma na zuciyar ta na yiwa Aisha dariyar auren sa, dan ta tabbatar abinda yake mata sai ya fi wanda zai yiwa Aisha, ta wani wajen har gwara ita ma akan Aisha ba.

Tana nan zaune har lokacin tashin su yayi yayin da su kuma suke aikin na su na gulma daga wannan suyi wanna girgiza kan ta kawai tayi. Tana ratayaa jakar ta lokacin shima ya fito, tare suka fita su dukan har Mu'azzam da ya tura machine ɗin sa, suna kallan sa suka ya fita.

"Wai dan Allah me ke damun ka?

Shiru yayi mata bece da ita komai ba. Ƙara ƙulewa tayi.

Tace, "Amma kasan abinda kake babu kyau ko? Kasan wannan shirun naka baya da amfani ko? Ba kuma zai amfane ka da komai ba wallahi".

"Ni ban yarda da wannan maganar ba da ake cewa wai mahaƙurci mawada ci. Ta ina ne mai hakuri zai zama mai Wada ta? Ta wanne ɓangaren? Ta kowanne bangare cutar sa kawai ake yi. Sannan da ake cewa wani mai haƙuri kan dafa dutse har ya sha roman sa ta ina?

"Idan ba fadar bahaushe ba, da san mayar da mutum komawa ba, bana ganin zan iya yin wannan haƙurin, bangan ranar da za'a zalunce ni ba ace nayi haƙuri. Wallahi ba zan haƙura ba".

"Muslunci ma haka yace idan an mare ka inda ba za'a ka iya yin haƙuri ba, ka rama ko ?

Ta faɗa tana tambayar sa, duk da tasan hakan ne, tasan kuma ba zai yi mata magana ba, maybe yau baya jin maganar ko sai ta gama zubar ta ya gasa mata magana, amma bata damu ba.

"To ni de ba zan iya ba, ba kuma zan iya gani ana zaluntar wani ba namma nayi shiru. Babu abinda ya min fi".

"Kuma kai ma".

Sai ta kalle shi, sai kuma kawai tayi shiru ta koma ta zauna tana kallan window.

"Naga ranar da zaka zamto kamar kowa".

"Sauya ni kike so kiyi?

Ta ji muryan sa..

"Laifi ne danna sauya mijina?

Murmushi taga ta yayi zai yi magana tayi saurin rufe masa baki idan ta na cikowa da ruwan hawayen abin tausayin. Dan tunda taga yayi wannan shegen murmushi nasa yanzu haka wata maganar zai gaso mata, wacce zata hana ta sakat ta hanata sukuni. Yayin da shi kuma hakan ya zo masa a bazata yana saurin taka burki, Allah ya so su a danja ta tsayar da su, da be san wacce mota za su bugawa ba. Kallan juna kawai suke yi, yana kallan idan ta dake ƙyallin ƙwallar da zata zubo.

"Dan Allah kar ka ce komai".

Ta faɗa tana cire hannun ta daga kan bakin sa, sannan ta koma wajen ta ta zauna, wato ma kan sa ta dawo tayi ɗane-dane duk a rufe masa bakin kar yayi magana, to Allah ya taimake ta ta haɗa shi da Allah. Ta kuma fara sanin halin sa na waye shi. Da ba abinda zai hana shi yi bata manana. Yana kallan ta tana share hawayen ta akai-akai. Ita kaɗai tasan rashin maganar sa illar da yake yiwa zuciyar ta. Bata so taga wani abu ya taɓa shi.

Har suka je gida babu wanda ya sake magana, ita ce ta kwashi kayan da ya siyo musu ta kaiwa su Umma na su, bata shiga ta ƙofar dake ciki ba ta su, sai yaga ta fito ta nufi ta main parlourn su. Duk yana zaune a mota yana kallon ta. Shafa kan sa yayi yana murmushin abinda tayi masa ɗazu kafin ya fito ya nufi cikin.

******Suna isowa suka kira Hafiz da ya san da zuwan su tun sanda suka taho, hakan yasa ya bar duk wani abu da yake ya je ya taho da su. Be kai su gidan su ba sai ya kai su Iffa ɗin su na kasuwa, sai da suka huta sannan Hafiz ya kora musu bayanin abinda suke so ya musu da kuma idan ya karya sharaɗin yarda suka yi. Tsaf suka yi komai a rubuce ya kuma sa sunan Mahaifinsa na next of kin ɗin sa, saboda duk inda aka je aka dawo de Mahaifin sa ne, kuma ko me ya same shi dole yana da iko akai. Haka aka yi komai cikin mutunci da mutuntawa, yayin da Hafiz a gefe guda kawai danne zuciyarsa yake saboda Deeni ne yasa shi yin duk wannan, daga nan suka tashi ya kai su tasha tare da kiran Moddibo ya sanar dashi.

Ya je ya kai su ya dawo yana parking ya ga Ɗalha shi da wani suna faɗa. 

"Lafiya?

"Kuɗi na zai bani, sace mi kuɗi yayi".

Cewar matashin saurayin dukan su uniform ne a jikin su alamar daga makaranta suke suka taho nan waje iyayen su.

Ɗalha yace, "Ban sace masa kuɗi ba, kowa ya san shine ɓarawon ba ni ba".

"Wallahi shi ya sace min kuɗi na, gashi nan kuɗi na a jikin sa, ai kullum ansan Baban ka baya baka kuɗin makaranta idan an baka ma kashewa kake".

"Ƙarya kake yi ne, Baba na yana bani kuɗi tara nake, kai ne kake sata".

Ya faɗa yana ƙara danƙo shi ya fara kilar sa, yayin da Hafiz  ya tsaya kawai yana kallan su, ya kasa rabasu to me zai ce musu? Sai da yaga ana neman a fi ƙarfin Dalha sannan ya raba faɗan yana mai kallan Ɗalha.

Yace, "Ya isa, nawa ne kuɗin?

"Ɗari ce".

Ya faɗa yana turo baki, yanzu akan naira ɗari suke wannan faɗan?

"Ba shi kuɗin sa tunda yace kai ne ka ɗauka".

Kallan Hafiz  yayi.

Yace, "Amma ban ɗauka masa kuɗi ba".

Dafa shi yayi yace, "Nasani, kawai ka bashi".

Ɗaukowa yayi ya bashi yana hararan sa. Yayin da Hafiz shi kuma ya ɗauko ɗari biyar ya bawa Dalha.

"A'a ba zan karɓa ba, Daada zai min faɗa".

"Ka karɓa, kace aiki kayi aka baka".

"Aiki kuma?

"Ehh zo mu je ka yi aikin".

Ba musu ya bi bayan sa, yace da shi ya je ya sauya kayan sa, aka bashi sabbin riga da wando a ledar sa dal. Ya zo yana ganin abinda Ameer yake yi.

"Meye wannan kake yi?

"Me kaga ina yi"?

Ameer ya tambaya kamar hasale yake, Ɗalha ya taɓe baki.

Yace, "Allah ya baka hakuri daga tambaya".

Hafiz ne ya kira shi ya zo, yace ya haɗa masa kujerar zama idan zai iya irin ta matan nan, da sauran katakon da suke zubarwa.

Yace, "Wannan abin me kuke da shi?

Ya faɗa yana nuna tulin garin katakon.

"Zubarwa".

"Zubarwa kuma? Na ɗauka?

"Me zaka yi da shi?

"Siyarwa, idan an kai wani waje da suke karɓa, naji ance paper ake haɗawa da shi. Amma fa ba sa siya da daraja".

Shiru Hafiz yayi yana tunani, daga shi har Deeni babu wanda ya kawo wannan abun, musamman Deeni ya san wasu abubuwan game da irin wannan abun na haɗe-haɗe.
Jinjina kai kawai Hafiz yayi bece ba.  Yayin da ya ke aikin sa shima Dalha yana aikin sa, na haɗa kujera kafin ya yace yana zuwa zai je nan kusa wurin Baban sa kar ya ji shiru be dawo ba. Yana zuwa kuwa ya dawo ya cigaba da aikin da yake tare da bashi tabbacin cewar Baban nasa yace zai zo yaga inda yake aikin ɗaga masa kai kawai Ɗalha yayi.

Tun Ameer na basar da shi har ya saki jiki da shi suka ringa zuba, Ameer ɗin na kowa masa wani abun shi kuma yana yi, sai gashi ya haɗa kujeru huɗu daga zuwan sa. Kafin ya tafi ya siyar da su, a tunanin sa kuɗin su ne sai ji yaji Hafiz yace kuɗin sa tunda shi ya haɗa, wani irin dadi yaji jin irin karamcin da suka masa, ne tashi ba sai da ya haɗawa Maman sa kujera guda ɗaya sannan ya musu sallama ya wuce, da kallo kawai Hafiz ya bishi. Be san shi ba, be taɓa ganin sa ba, amma yaron ya shiga ran sa da yawa. Yayin da Sadiq yace.

"Kasan yaron nan da wa yake min Yaya Hafiz?

"Sai ka faɗa".

"Da wani wanda Ameer yayiwa libry".

"Zai iya iyuwa idan ya dawo sai ka tambaye shi".

Jinjina kai kawai Sadiq yayi, ya wuce ciki wajen Ameer shima ya kwanta yana hutawa. Sanda suka dawo suka ga Deeni yana rufe mota, kallan Ameer kawai yake yi da shi da yayar sa basu da maraba a wajen ragwanta ace sam ba su da juriyar azumi.

"Ameer lafiya?

Sadiq yace, "Yaya kai ma kasan dalili ai".

"Ba Yaya Hafiz ba ne yace ba zai ɗauko ni a mota ba".

Girgiza kan sa Deeni yayi kawai, yayin da Hafiz ya yi parking motar sa yana tarar da Deeni.

"Yau kun dawo da wuri".

"Wannan uban gaggawar ne ya dawo damu".

Cewar Sadiq yana nuna Ameer, suka wuce part ɗin su batare da sun shiga wajen su Baba. Yayin da Hafiz take daman Allah Allah su haɗu yayi masa zancen da ya zo masa kan sa.

"Ina da shawara?

"Ta?

Cewar Deeni suna nufar kujerar da suka gani a parking space ɗin.

"Me zai hana mu buɗe wurin yin paper da stickers, da wannan pulp wood ɗin da muke zubarwa a banza, ko a ƙone?

Shiru Deeni ya masa yace, "Tun da baka kawo wannan ba?

Hafiz yace, "Ta ina zan kawo bayan ba field ɗin na karanta ba".

"Nima ka manta ba shi na karanta ba?

"Koma de meye yanzu taya zamu ɓullowa lamarin nan".

"Fa'iz ne zai yi mana amfani mana".

"Dan Allah ka dena sako Fa'iz a sabgar mu, me ka sani dangane da Fa'iz wai?

"Fa'iz nasan shi sanda zamu je Anadyr, kujerarsa ce a kusa dani, shi kuma a lokacin sunje America yin project ne ko wani practical bansani ba. Amma de anan nasan me ya karanta, me kuma ya je yi, ina kallan sa duk wani abu da yake yi,  kafin ya tashi ya koma bayan kujerar da nake wurin ɗan mate ɗin sa. Anan nasan waye Fa'iz".

"Kawai nagan shi, ban za ci zan sake ganin sa ba, sai da naje Gumel kawai nagan shi, abin ba baƙaramin mamaki ya bani ba dana gan shi a wannan halin. Da kuma na ji labarin su shine na fahimaci komai".

"Nayi tunanin daman za su je gidan A. Madaki shiyasa muka yi magana da Sakeenah ta ajje su a gidan su sanda tace maka ta tsince su".

Kallan sa kawai Hafiz yake yi, wato Deeni irin mutanen ne da ba su da yawa a cikin al'umma. Baiwa ce da su ta sanin inda suka zauna suna lura da komai dake faruwa a kewaye da su. Kuma zai yi kamar baya ji ko gane komai nan kawai yana sane da duk wani motsin wani abu.

"Hafiz duk wani labari da ake bayarwa idan ka tsaya ka ji labarin dakyau akwai wani abu da labarin ke  so ya isar maka da shi. Kamar mai kyau ko marar kyau, hallau na raya ko bana yara ba. Duk inda ka tsinci kan ki a cikin mutane ka ji suna wata maganar su, to akwai abinda suke so su isarwa da junan su, ida ba sirri ba ne maybe ya amfane ka".

"Kaga wannan maganar ta ka, ba gane ta ba nake. Ka fito fili ka min bayani".

Ɗan murmushi yayi masa.

Yace, "Hashim ba ɗan A. Madaki ba ne ba".

Wani irin mamaki ne ya kama Hafiz a zaunen da yake, yayin da Deeni kuma yake jinjina masa, kafin ya kwashe komai ya sanar dashi. Banda salati babu abinda Hafiz ke yi, sai da ya nutsu shima ke sanar da shi ya sami wani yaro ya ɗauke shi aiki. Jinjina kai kawai Deeni yayi bece komai ba, yana tunani yarda za su ɓullowa lamarin nan. Sai da suka ga an kusa magriba sannan suka shiga ciki wanka kawai yayi ya fito ya same su anyi jiran asha ruwa. Ko kallan inda yake yau Hajiyar sa batayi ba tana ɗaure fuska. Ita kuma tana haɗe rai ne dan kada ya faɗa mata wata maganar, hakan da take yi shi abin dariya yake bashi.

*******"Yau de na samu aikin yi, na dena zuwa Islamiyya gaskiya, ku ga fa yau kuɗin da nayi. Wallahi mutanen suna da kirki".

Cewar Ɗalha yana sake irga kuɗin sa sau ba adadi. Halima har ta gaji da magana tayi shiru yayin da Maryam ke sawa kuɗin albarka duk sanda yayi  maganar. To yanzu kuna Ɗalhat ake so a sanarwa da saƙo.

Ɗalhat yace, "A'ina ka samu aikin?

"A kusa daku, wanda yake baya da inda kike siyar da kayan ka?

"Ina kenan?

"Masu kujerun nan, fa naga ma aiki ake musu a gefen wajen, kamar wurin cin abinci za'a buɗe".

"Eh nagane wajen, anan naje na siyo kayan ɗakin nan ai".

"Ai sun iya kaya ba laifi".

Cewar Daada. Yace, "Naji ana ta faɗar su kam, yanzu su suke abin su da man su sai kuma yara haka masu taimaka musu,  dan naji an sun kori yaran shagon".

Ɗalhat yace, "Wallahi Daada ko ina akwai maha'inta, kaga a companyna sai fa duk sati ina bi ina duba ingredients, ina shiga da kai wajen abinda ake manufacturing,  baka ga ba yadda ake abinda aka ga dama".

"Ai mutane ba amana".

Ɗalha yace, "Allah Daada baka gan su ba, wani ne de ya yi banza dani kamar Sadiq naji shi Ogan na su ya kira".

Ɗalhat yace, "A'a Ɗalha, indai Sadiq ɗin da kake faɗa ne wanda nasani gaskiya ba ruwan sa".

"Mai kama da Daada fa".

Murmushi Ɗalhat yayi yana cewa shine kuwa.

Halima tace, "Masu kuɗi, sai ka bamu kuɗin kitso da lalle da ƙunshi".

"Idan kin isa nashiga Makka. Ke da ko albarka baki samin ba".

Ya faɗa yana ƙara wara kuɗin.

"To biya ni kuɗin iloka ta da ka ringa sha min".

"Ehh?

Ya faɗa yana ɓoye kuɗin a bayan sa. Fatan shirya kawai Daada yayi musu yana sake tunanin to waye mai kama da shi kuma aka samu? Zai je shi kuwa domin yagan shi. Indai ya je kasuwar ta su.

******"Nace ba?

Banza tayi da shi ta kwanta luf kamar wacce tayi bacci.

"Hajiya fa".

"Hajiya ".

"Dake nake magana fa".

Ta kowa  ya yi yana zuwa da bubbaga ta, yi tayi kamar bacci ya kwashe ta,  ɗin nan aka tashe ta.

"Abincin waye zai zuba min?

Wayar ta kalla taga tara da wani abun. Miƙewa tayi tana hamma irin baccin nan.

"Ƙarya de bakyau, kuma mai ƙarya ɗan wuta ne".

"Ƙarya kuma? Kai ka san me kake faɗa. Muje na zuba maka".

Hanya ya nuna mata alamar ta yi gaba.

"Ashe ba zaka ci ba".

Ta faɗa tana komawa da kwantawa.

"Amma kin san ba wurin kwanan ki ba ne ko? Kuma ki gaggauta tashin a gado tunda ba gado".

Ta shi tayi ta wuce ta bar masa ɗakin, shi kuma ya bita a baya, parlourn kawai ta tsaya kalla, ba ƙaramin rena mata hankali yaran nan suka yi ba, ta dafa ta kawo musu, su zauna su ci su tafi, su bar mata parlour kaca-kaca.

Riƙe ƙugu tayi ta fara kiran su ɗaya bayan ɗaya suna fitowa har Sadiq babu wanda ta bari, har su Ummu da yau aka ritsa da su suna ɗakin Zarah ko ace Ameerah dan ta dawo an kacokam.

"Anty gamu".

Cewar Taufiq yana zama a kujera. Yayin da su Ameer suka tsaya suna jiran su ji dalilin kiran. Ta juya ta kalli Deeni dake bayan ta, a zuciyar sa kuma cewa yake yau akan ku za'a sauke kenan. Dan har da haushin sa take ji bakaɗan ba akan abinda ya faru a office.

"Dan kut****ku ni kuka mayar baiwar ku? Na dafa muku, na kawo muku ɗauke kwanon ma ni zan yi muku?

"Kai Anty gajiya muka yi fa".

Cewar Ameer.

"Gajiya kuka yi ko? Sannun ku Allah ya taimaka, Allah ya huci gajiya".

Ta faɗa tana jinjina kan ta.

"Zaku iya tafiya toh".

Tayi hanyar kitchen sai gata da tsintsiya da parker. Har rige-rigen karɓar  tsintsiyar suke dan sun san halin kayan su. Zama tayi yayin da shi kuma yake tsaye ya jingina yana kallan su kawai.

Sabir ne ya shigo ya yi wajen ta da littafi a hannun sa, shatin da taga a wuyan sa ne yasa ya yin wani irin zagi tana cire masa rigar dake jikin sa.

"Wa maka wannan dukan?

Shiru yayi yana kallan ta.

"Dan uwar ka ba manana nake maka ba?

Ummu tace, "Anty, Antyn ajin su ce ta yi musu sanda muka je zamu ɗauko shi ma kneel down suke yi ba shi ɗaya aka daka ba".

"Ni be dame ni ba kawai yaro na na sani, kuma na ci Kut***ta".

Sadiq yace, "Yanzu ai dare kiyi haƙuri sai gobe, kuma baki da numbern ta bare ki kirata".

Daƙyar ta haƙura ta bari zuwa gobe ta koma ta kwanta, yau be ƙara mata magana ba kar abun yayi mata sai ya kwanta a gefen ta.

"A'a ba zan hau gado ɗaya da kai ba gaskiya".

"Ohh haka ne?

"Tambaya kake?

"Gani nayi ɗazu harda su hawa kai na, shiyasa nayi tunanin ko wani abu kike biɗa".

'wanne irin mutum shi'

Ta faɗa tana ɗaukan pillow Simi simi ta wuce tayi shimfiɗa.....

Continue Reading

You'll Also Like

2.1K 58 9
I don't own Ninjago, LEGO does! Also, this wasn't my original idea it was @Lordexploionmurder idea. Even though I'm planning for this story for the p...
40.1K 8.8K 58
"Sarauniya!" I said almost loudly but not enough for my friend Bilal to hear, "who is she?" "Aaliyah. She's the late Alhaji Mujib's daughter. " Bila...
58.6K 1.4K 31
~ Featured 2× on @StoriesUndiscovered's Reading List Tales Of The Heart. ~ Featured on @WattpadEmpowered's Reading List Monthly Spotlight. ~ Winner...
72.6K 7.5K 55
A life of a strict father who is a soldier raising his 2 kids along with his duties.