ZARAHADDEEN

By hijjartAbdoul

1.6K 71 8

read and find out More

1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
12
13
14
16
15
18
19
20
21
22
23
24
25
26.
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42.
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52
53
54
55
56
57
58
59
60

11

26 2 0
By hijjartAbdoul

✨ *ZAHARADDEEN* ✨

          
                   By

       *Hijjartabdoul*

 
                     11.

*****Ya jima akan ta yana kallan ta, ya rasa takamaimai mene yake ji a game da yarinyar nan, duk iskanci sa da mace iya riƙe riƙen hannu ne kawai amma ko kiss baya haɗa su da kowa, ba kuma wai ba zai yi ba kawai harkar ce baya so shide barshi a dating yarinya idan yaga tana neman wuce gona da iri kuma su rabu, ba lalle ba dole....

Ajiyar zuciya ya sauke yana zama a kusa da ita, kafin ya shafi fuskar ta, cike da tausayin ta, ganin yarda fuskar ta, ta wani irin tashi ta kumbura tayi jaa da ita, jin ana shafa mata fuska yasa ta buɗe idan ta a hankali tana kallan sa. Bata ce masa komai ba ya janyo wayar ta da tunda yau ta waye bata kalle ta ba,tama manta da wata waya ita kam. Ganin har ƙarfe biyar tayi yasa ta dirowa daga gadan cike da sauri saide rashin ƙwari jiki yasa ta kusan faɗuwa sai da ya tarota tana cewa tayi a hankali. Bata tanka masa ba ta wuce bayi, sai da ta sake gasa jikin ta da ruwa mai zafi taji dama-dama sannan ta fito, sanin cewa yana ɗakin yasa ta rufa towel biyu. Yana kwance akan gadan ya faɗa duniyar tunani, kwata-kwata ya ma rasa mene ya dace da yayi. Zancen Maryam zai ɗauka ko kuwa zancen da ƙasan zuciyar sa yake cewa kar ya ɗauka.

Har ta zo ta shirya be san tayi ba, sai da yaji ƙamshi ba turaruka sannan ya buɗe idan sa ya zuba mata su, tana kallan ta, ta shirya ta zo ta fara sallah, iya sallahr na ta ma kawai abin burgewa ga wata nutsuwa da yaga ta ƙara yi. Shide yasan ba haka yake sallahn sa ba, kawai fakawa yake yi daga ya tada zai kai, daga ya kai ruko kuwa zai ɗago. Amma ji ita yarda take yi, wani irin burge shi tayi sai ya bata dukkanin wani hankalin sa har ta idar, yanzun kam ta tayi azkhar sai ta haɗa da na yamma duka tayi. Naɗe abin sallahn tayi kawai ta  fice daga ɗakin. Shima bin bayan ta yayi ganin tana ƙoƙarin fita yasa kiran sunan ta.

"Zaki je ?

"Abinci zan ci".

Ta faɗa tana ƙara yin gaba.

"Dawo ki zauna, bari na ɗauko maki".

Ba musu ta dawo ta zauna, dan bata san ina ne Kitchen ɗin ba a gidan.

Yau anyi sa'a dukan su suna zaune, babu wanda ya fita har Hajiyar, kai tsaye dining ya wuce, ganin babu abinci ya sa shi yin hanyar Kitchen babu wanda ya lura da shi, Saboda kowa abinda ya shafe shi yake yi, a kitchen ɗin ma ba abinci dan sai sun ce suna so ake yin na dare, na rana kuma anyi har sun ci. Kiran wayar dake Kitchen yayi maid ɗin ta zo ya faɗa mata abinda zata girka sannan ya fita ya sami waje a parlour ya zauna.

"Lafiyar ka kuwa?

Cewar Hajiya, girgiza kan sa kawai yayi yana gyara zaman sa ya lumshe idan sa.

Safiyya tace, "Ita abar taka bata faɗa maka irin rama marin da nayi ba?

Daman yayi tunanin hakan, tunda yaga fuskar ta tashi. Ko buɗe idan sa be yi ba bare ta sa ran tanka mata.

Hashim yace, "Mari kuma Sofi?

"Eh mana, Bro bata da hankali just imagine ni zata haɗa jiki da ita? Wata kuca ka da ita".

"A'a sis, abinda kika be dace ba, ki dena wulaƙata mutane mana, mutane fa suna da daraja".

"Ai kaima naga kana yi".

Yace, "Duk abu na Sofi,bana taɓa marin mutum, ba kuma na wulaƙata shi, ki bar ne da rashin mutunci na shima sai na ga dama. Amma ke bansan wacce iri ba ce. Kumar matar yayan ki".

"Kuma wallahi ko kallo na ta kuma yi sai na rama".

"Zaki iya".

Daga nan be kuma cewa komai ba ya cigaba da danna wayar sa. Shi de Ɗalhat na jin su be ce da su komai ba haka Hajiya.

Musaddiq yace, "Ni bamma ganta ba, tana da kyau?

"Abinda ya dame ka kenan?

"Ehh mana, idan tana da kyau to ni duk abu da kike faɗa be dame ni ba".

Babu wanda ya tanka masa, har maid ɗin ta kawo abinda ta haɗa a ciki try, ta ajje a gaban shi, dukan su kallo suka bishi dan a iya zaman da suka yi da shi baya san cin abinci a gida shide barshi a wayon restaurant amma shine yau?  Ko kallan su be yi ba ya tashi ya wuce part ɗin su, suka bishi da ido. Hajiya na jinjina kai. Hashim kuwa besan ya akayi ba sai abin yayi masa daɗi.

Waya ya same ta tana yi da ƙawayen ta tana musu bangajiya da godiya, tashi tayi zaune ganin ya shigo, ƙasa ta sauko hakan yasa shi ajje mata a ƙasan ya zuba mata komai sannan shima ya zuba, sosai ta ci abincin batare da ji komai ba dan na ɗazun a takure ta ci shi. Kuma abincin yayi mata daɗi. Babu wanda ya tanka har suka gama ya kashe kayan ya kai Kitchen ɗin su dake parlourn ya dawo ya zauna a kusa da ita.

"Kana so na?

Ya ji tambayar a sama, hakan yasa shi zuba mata ido itama shi take kallo.

"Meyasa wannan tambayar?

Ya tambaye ta. Kawar da kan ta tayi hawaye na zubar mata a ido.

Tace, "Bansani ba ko saboda zakuyi amfani da ni shiyasa kuka aure ni".

Goge ƙwallar tayi, tana wani murmushin takaici.

Tace, "Ka faɗa masa, koma meye ya sani zan yi ba zan musu masa ba. Amma dan Allah kada ya cutar da kowa nawa".

Tana kaiwa nan ta haɗe kai da gwiwa ta fara rera kuka. Ajiyar zuciya ya sauke cike da tausayin ta, yanzu kam ko ba ya san ta zai kwantar mata da hankali dan tabbas an cuce su an kuma yaudare su, a hankali ya ƙarawa matsawa kusa da ita kamar mai tsoron ya taɓa, ɗago ta yayi ya haɗe goshin su.

Yace, "Ina san ki".

Ɗagowa tayi ta kalle shi, sai ta girgiza kan ta, tana cigaba da hawayen kafin ta sa hannu ta cire hannun sa.

Tace, "Kana san wani abu de, amma bani ba".

Daga haka ta wuce ɗaki ta barshi a nan, jikin sa ne yayi wani irin sanyi kawai ya tashi ya bita. Ya same ta akan gado tana waya da ƴan gidan su ba ƙaramin dauriya tayi ba wurin nuna musu babu komai.

Hafsah ce daga can tace, "Ke dan uwar ki ban yarda da ke ba, ya na ji muryan ki haka? Wani ne ya taɓa ki? Faɗa min waye shi na ci uwar sa".

Sai da Ɗalhat ya sami kan sa da murmushi, jin abinda tace, daman ita ce aka auro, matar da ta dubi Yayan sa ta mara to waye ba zata mara ba kuwa?

"Anty fa bakomai fa. Ni waye zai taɓa ni ma. Ina Zarah ba sa su zo ba?

Zarah tace, "Zamu zo mana kafin mu tafi gobe".

"Dan Allah ku zo da wuri to".

"Zamu duba mu gani".

Cewar Ummu.

"Kada Allah yasa ku duba ɗin kar ma ku zo".

Ta faɗa tana kashe wayar ta, sai kawaita rushe da kuka tana kwanciya akan gado, beyi aune ba yaga ya bita kan gadon, daga lallashi zancen ya sauya....

******Bayan sun gama waya kowa na faɗar abinda ke ran sa gami da Ameerah har ga ita de bata yarda da ita ba, duk a tunanin ta ba zata samu ba dan Ameerah tayi aure amma duk yarda taje ga rashin damuwa ta damu ɗin. Sam hankalin ba'a kwace yake ba, ina ma ana iya bari da ta koma gidan Ameerah da zama. Amma tasan hakan ba me iyuwa ba ne ba. Tana wannan tunanin taga su Deeni sun dawo, ido ta zuba masa lokacin da yake parking dake dukan su suna tsakar gidan.

"Iyayi kawai".

Ta faɗa a zuciyar ta. Tana kau da kai.

Ameer ne ya matso kusa da ita. Yace, "Anty saurayi naki kike kallo haka?

Yana faɗa ya tashi zai gudu, mikewa tayi tana cewa, "Ameer sai na ci Kut****ka, naga reni ya fara shiga tsakani na da kai".

Ta faɗa damƙoshi.

"Dan Allah kiyi haƙuri, Yaya ka zo ka taimake ni".

Hafiz yace, "Sake shi mana, me ya maki".

"Wallahi Yaya...".

Ki sake shi nace, sai da ta kwade shi sannan ta sake shi. Yana dariya dariya.

Yace, "Wai da girmana Anty kike duka na, ki ga fa na fiki tsayi sau ɗari tsakani da Allah. Kika sani ko nine zan yi maki waliyyi na bada auren ki...."

Wayar ta ta jefa masa, ya cafe ba ƙarasa ba, yaba bayan Hafiz zata kamo shi, shi kuma Hafiz na tsakiya.

"Allah Yaya ka bari na ci uwar yaron nan".

"Kiyi haƙuri dan Allah".

Ameer ɗin ya faɗa dan yasan ko anjima ne sai dake shi tunda ta furta. Ƙwafa tayi tana komawa ta zauna, Deeni na kallan su yana girgiza kan sa ko sai yaushe zata yi hankali?

"Sai ka aure ta".

Wata zuciyar ta bashi amsa, sai yayi murmumushi yana shafa kan sa, tare tahowa wajen su.  Sabir da gudu ya yi wajen sa, ya daga cimak yana juyi da shi da a sama, har daga shi sama yayi ya cafe.

"Nide aka yarda min ba yafewa zan yi ba".

Bece mata uffan ba, ya rungume shi suna sauke ajiyar zuciya, sannan suka zauna.

"Yaaa".

Zarah ta faɗa tana matsowa kusa da Deeni.

"Uhm?

Ya Faɗa yana kallan ta.

"Gobe idan Allah ya kaimu zamu je gidan Ameerah ko?

"Ku je kuyi me?

"Yaa dan Allah sallama zamu je mu mata".

Ameer ma yace, "Dan Allah Yaya Deeni".

"Kunsan de da wuri zamu tafi ko?

"Kai Yaaaa dan Allah Allah fa".

"To Allah ya kaimu goben".

Rungume shi tayi, tana gode masa.

"Ina Sadiq?

"Sun fita da Taufiq".

Jinjina kan sa kawai yayi, yana kallan mutuniyar ta sa dake danna wata ƙunkuni, yau kam ba zancen ana kallan mutane dan Hijabi ne meduimya jikin ta.

"Yau da daddare zamu fita shan ice cream Yaya da Hafiz zaku je?

Ummu ta faɗa tana kallan su.

"Kuma ba za ku je ba".

Cewar Hafiz.

"Wallahi Baba ne ya ce mu je saboda Zarah da Yaya Sadiq ko Ameer?

Ameer yace, "Ehh ba". 

Sabir yace, "Anty ce kuma zata kai mu".

Deeni shiru yayi, dan be san ko ta iya mota ba, ko bata iya ba.

"Nide ba zanje ba, kuma Deeni ma ba zai je ba".

Da daddare suka shirya bayan sun ci abinci, dukan su kaya iri ɗaya suka sa, suna so su kam sa abu iri ɗaya, Zarah kayan Ameerah ne da bata ɗauka ba ta sa, rolling suka yi dukan su da Hijabi zata sa Zarah tace dan Allah tasa veil ɗin kayan, haka ta roller shi amma bata san ɗan kwali ba ana ganin shatin ƙananan kitson da aka mata. Sun yi kyau sosai abin su. Suma mazan iri daya suka sa, kala ce kawai ta banbanta.

Umma tace, "Hajiye dan Allah kar ku je ku zauna".

Hafiz yace, "Ai ba sai kin faɗa ba Umma indai Hajiya ce, yanzu zaki ga sun dawo".

Baba yace, "Shiyasa na ce su tafi ai. Kar ayi dare".

"In sha Allah Baba".

Ta faɗa tana duba wayar ta.

"Sabir ina waya ta?

"Nima bangan ta ba".

Taya ta suka fara yi ana duba wayar, a parlourn, wayar kuma na gefen Deeni sai da ya zauna ya gan ta, da suna nema kuwa be ce da su uffan ba, ga wayar a silent take.

"Ke ma sai ki ke sa waya a silent gashi irin ta nan ai".

Hafiz ya faɗa.

"To damuna ake yi".

"To gashin nan ai".

Haka ta haƙura bata tafi da wayar banda bata rai ba abinda take yi.

******Suna zaune an kawo musu ice cream ɗin ita kuma tace ba zata sha ba, hakan sa banda ita, sun yi hotunan sun yi cinye cinye abin su, anyi videos kala kala, kowa ka duba yana dariya ita kuma be fi hoto ɗaya ta ɗauka ba haka ma Ameer guda ɗaya aka musu da Zarah wai ita ce ƴar gidan su yanzu.

Ameer ne ya zo ya sami Hafsah dake zaune bata je inda suka yi hotan ba.

Yace, "Anty waccen ba ita ba ce wacce kika mara  jiyan nan?

Ya faɗa yana nuna inda Safiyya take wurin wasu mata da maza.

"Kamar ita ko?

"Anty ita ce mana, ji yarda take  wani abu da maza".

"Allah ya kyauta".

"Yanzu gidan muka kai Ameerah kenan Anty?

"To Ameer ya zamuyi. Kawai ni a tunanina Baba ne be san abinda yake ba. Ya rasa nutsuwar sa gaskiya".

"Kai Anty Baban?

"Ameer kenan, ba ku san komai ba Shiyasa".

"Meye bamu sani ba".

Shiru tayi ta rabu da shi dan bata san me zata ce masa ba. Daga nan suka wuce suka je siyayya sannan suka koma gida. Suna zuwa gida kowa ya wuce ya je ya kwanta mana a'a sai suka baje anan aka fara maida zance daga nan Ameer yace suyi shigar India mana su yi rawa aikuwa suka yi, aka fara shirme da hankali irin abin kabhi kushi kabhie gham, Taufiq ne Sharukhan Zarah ce uwar shi kuma Ameer shine Baban.

"Daman Zarah bata da lafiya itama?

Hafiz ya faɗa yana kallan su, sai abin ya bawa Deeni dariya ya kai duban su kan su.

Sadiq yace, "Da kai kallan mai hankali kake mata?

"Wallahi nutsuwar ta nake gani, gani ta fi su hankali".

"Yanzu ka tabbatar da kan ka ba wani ya faɗa maka ba ai".

"Nagani kam".

Deeni ne ya kalli sama ganin fitowar Hafsah yanzu haka tayi bacci yayi kai uku, kawai leƙa su tayi ta saman ta girgiza kan tana ɗaukan ruwa ta koma abin ta batare ta sauko ba, sai ya kalli wayar ta da bata ɗauka ba kawai ya girgiza kan sa shima. Tare da tashi ya shige ɗaki yana wani tunani akan auren Ameerah. Hafiz shima tashin yayi ya wuce ya bar su ba su ne suka kwanta ba sai wajen uku saura shima badan sun gaji ba sai dan Baba da yayi musu magana sannan suka kashe kiɗan suka turawa Ameerah da mai hankalin da marar hankalin duka suka hankaɗa mata.

Taufiq yace, "Mu tashe ta dan Allah kunji".

Ummu tace, "Haka za'a yi, kira mana ita a wayar ki Yaya Zarah".

Ba musu Zarah ta kira ta suka sa ta a speaker kamar de ɗazu.

Ameer yace, "Kar mu tsorata ta fa".

"To ai haka zamu ce mata ta duba wayar ta sai mu kashe".

*******Suna cikin bacci suka taji ringing ɗin wayar ta, salati tayi tana tashi zaune dasauri tana ɗaukan wayar tare da ficewa daga ɗakin duk a tunanin ta, wani abu ne mummuna ya same su, sai da ta kunna hasken parlourn sannan ta ɗaga cike da fargaba.

"Da sanin Allah wallahi".

Ta faɗa bayan ta ɗaga jin su suna mata dariya.

Ameer yace, "Daman mana Allah ya fi mu sani".

"Da wannan tsohon daren zaku ka fa kira na".

Zarah tace, "Ki duba wayar ki".

"Meye ne?

"Kede ki duba mana".

"To naji zan duba".

"Sai da safe".

"Goben fa zamu zo".

"To Allah ya kaimu, ku kuma Allah ya saukar muku da shiriya".

"Ke ɗin shiryuwa kika yi?

"Ko ban shiryu ba amma kun san yanzu na fiku hankali kuma na fita daga jerin sahun ku dan haka ku dena sani a shirmen ku".

Ta faɗa tana kashe wayar ta bar su da baki sake suna kallan juna ehh lalle Ameerah ita ce ke faɗa musu wannan maganar.

Ameer yace, "Daɗin abin ma muma zamu je inda kika je".

Taufiq yace, "I hope baka ƙufila ba".

"Uban ƙufila nayi ba ƙufila zata san tayi da mu".

Zarah tace, "Bashi ta ɗauka".

Ameerah kuwa murmushi tayi tana kashe wayar tasan ta shaƙa musu iya shaƙawa ma kuwa. Sanna ta kunna datar ta da tunda aka fara bikin nan bata buɗe ba, hotuna ne da videos tun daga na bikin ta har wanda suka turo mata yanzu, bata na kan na bikin ma sai ta buɗe na yanzu tana gani, sosai tayi dariya kafin kuma ta ajje ruwan hawaye na wanke mata fuska, jin motsin sa zai fito yasa ta saurin share hawayen nata, tana ɗaukan wayar ta cigaba da kalla.

"Me kike yi?

"Bakomai".

Ta faɗa tana kallan sa, dan har ga Allah yanzu bata san wata magana take haɗa ta da shi. Zuwa yayi ya zauna a kusa da ita yana karɓar wayar. Shima yana gani sai da wani abun ya bashi dariya, kawai kallan sa tayi tare da tashi ta bar masa wayar tasa, hotunan bikin ya buɗe yana kallan ɗaya bayan ɗaya, kafin ya dauko wayar sa duk wani hotan ta wanda aka yiwa ita kaɗai sai da ya tura kafin ya sami mai kyau ya ɗaura a wallpapern  shi both home and lock. Sannan shima ya je ya kwanta.

    Washegari ƙarfe tara Abban su ya kira ta, kamar ko yaushe tana hakimce akan kujerar sa ya zuba mata shayi ya miƙa mata. Hannu tasa ta amsa tana godiya.

"Nasan baki ci komai ba nasa a na tashe ki. Ki sha".

Ya faɗa yana kai nasa bakin sa. Ƙin sha tayi.

"Idan baki sha ba laifi ne, sannan idan kika sha baki shanye ba shima laifi ne, sannan kuma ki ajje idan kina sha laifi ne. Dan haka bana san ki sake maimaita abinda kika yi jiya UHM?

'wai shi wannan wanne irin mutum ne?

Ta tambayi zuciyar ta tana mai kai wa bakin ta, kamar ya shiga zuciyar ta yasan me tace.

Yace, "Ni mutum ne kamar kowa Yusrah".

Ita fa ba sunan ta Yusrah fa ya bi ya wani laƙaba bata Yusrah, sai ta ɗago ta kalle shi ta maida kan ta ga shayin da take sha.

"Naji saƙon da kika bayar a bani, kuna ya iso gare ni".

Sai ya dube ta dakyau, yana mai ansar cup ɗin hannun ta tare da ƙara mata wani shayin ganin ta kusa shanyewa.

"Tashi ki dawo nan".

Ya faɗa yana nuna mata kusa da shi, ba musu ta tashi ta dawo kusa da shi. Sai ga Hashim ya shigo bayan yayi knocking an bashi iznin shigowa. Zama yayi a ƙasa yana gaida mahaifin nasa tare da bashi tabbacin irin abinda suke nema fa sa'a ta fara zuwa, sai yayi murmushin jin daɗi yana maƙi masa nasa shayin. Yayin da ya mika masa takardun hannun sa. Shima sai ya miƙawa Ameerah.

Yace, "Buɗe min Daughter".

'wai Daughter'.

Ta faɗa a ran ta, sai ta buɗe masa kamar yarda ya umarta, takardu ne a ƙalla za suyi goma. Sai kuma blue biro kala da kala, ɗagowa tayi ta kalle shi.

Yace, "Ajje mana".

Ta ajje akan table ɗin yace, "Irin wannan signature ɗin zaki min".

Ya faɗa yana nuna mata exactly signing ɗin Baba, ta kalle shi ya kalle ta, tana mai haɗe wani abu dake zuwar mata wuya. Ƙwalla na cika mata ido.

"Ko ba zaki yi ba?

Girgiza masa kai tayi alamar a'a kafin ta duba biron da ya dace ta fara exactly irin signaturen Baba babu banbanci ko matsala kamar de Baba ne yayi shi, haka ta gama tas, ya bata tayi na Hafiz shima ta gama sannan ya karɓa yana misklin murmushi.

"Kafin na nemawa ɗana auren ki sai da na tabbatar da wanne irin amfani zaki min".

Sai yayi murmushi yana cewa ta tashi ta tafi, tana yin gaba hawayen da take maƙalewa suka zubo tasa hannu ta share.

"Amm... Yusrah".

Sai ta juyo tana kallan shi.

"Kada ki yi kuka ɗaya cikin deal ɗin mu".

Sai yayi mata shegen murmushi yana kallan kofin da ta sha yau ma de bata shanye ba. Kawai tafiya tayi bata ce masa komai ba. Tana fita Hashim ya biyo bayan ta.

"Ina kwana".

Ta gaida Hajiya bata amsa ba, hakan yasa ta wucewa ta shige part ɗin su kawai ta zube a  parlour ta hau kuka tayi mai isar ta sannan ta wuce ɗaki. Yana kwance yana bacci, idan tace rashin sallahr sa baya damun ta to tayi ƙarya, dan sosai abin ke damun ta wai shine mijin da take aure, ta gama kallan sa sannan ta wuce ta shiga wanka sai da ta fito ta zauna ta kalli kan ta kafin ta tsara kwalliyar da ta san zata rufe mata wannan shatin marukan da ta sha a wajen ƙauwar sa. Tana gamawa kuwa suna kiran ta hakan yasa ta cewa gata nan zuwa wai suna main parlour.

"Inyee ka ga Amarya".

Cewar Zarah ganin ta fito, murmushi kawai tayi musu tana cewa su fito, suna shiga Hashim na fitowa daga ɓangaren Abban su, dan haka be ga Zarah ba.

"Ita wannan bata amsa gaisuwa?

Ummu ta faɗa tana kallan Ameerah.

"To Ummu gaki ga ta ai ni ba ruwana".

Zarah tace, "Aikuwa de, me kika dafa mana".

Zarah ta faɗa tana nufar dinig ɗin.

Tace, "Nima bansani ba, muje mu ci".

"Kinga yarda kika yi kyau kuwa inyee".

Tsaki taja tana hararan su.

"Ina su Ameer?

"Laa suna waje, harda Yaya Sadiq fa".

Ummu ta faɗa tana tashi dan taje ta kira su. Musaddiq da saukowar shi kenan yaga Ummu.

Yace, "Wacce da ta fita kuma wacece?

Hashim yace, "Ina ruwan ka?

"Ni ganin mutane ne bana san yi any how".

"Wurin ƴar uwar su suka zo toh".

Be rufe bakin sa ba sai ga Ameer da Taufiq da Sadiq, bama su lura da su ba kawai suka shige ɓarin Ameerah.

Hajiya tace, "Ni kwa Hashim na tambaye ka mana?

Beyi magana ba sai kicin kicin da yayi da fuska.

"Meye haɗin ka da mutanen nan?

"Babu".

Ya faɗa ba ya bo ba fallasa.

Shiru kawai tayi masa bata ce komai ba dan ta fara lura da irin sauyin da ya fara yi shida Ɗalhat.  Amma zata ɗau mataki da wuri kafin Ɗalhat ya fara san waccen shegiyar yarinyar.

Sadiq ne ya dube su yace, "Ku tashi mu tafi to".

"Kai Dan Allah Yaya Sadiq".

Ameerah ta faɗa tana marairacewa, be je ga magana ba sai Ɗalhat nan ya fito har zuwa share su sai kuma ya zo suka gaisa sannan ya fita. Har bakin mota ta raka su suna raha da dariya abin su gwanin ban burgewa sai tsokanar juna suke.

"Bari ayi hoto".

Cewar Taufiq yana fidda da camera.

Sadiq yace, "Taufiq kai komai sai anyi hoto?

"Saboda tarihi mana".

Ya faɗa yana daura cameran akan mota tare da saita timer suka sa a Ameerah a tsakiya kowa ya dara. Sannan suka shiga mota suka tafi tana ganin za su tafi kuma sai hawaye.

"Idan kuka kike ba zamu ƙara zuwa ba".

"A'a na dena".

Cewar Sadiq yana ɗaga mata hannu, sai itama ta ɗaga masa tana goge ƙwallar ta tana kuka. Sai da suka tafi sannan ta kalli zoben da Zarah ta bata da ƙarfi da yaji ta kwace shi. Duk abinda suke Abban su na daga zaune yana kallon su. Murmushi kawai yake yi. Suna cewa Hashim na fitowa suka yi saɓani da su. Gaida shi kawai tayi tana mai wucewa ta bar shi a tsaye yana danna waya.

"Ke zo nan".

Cewar Safiyya tana ƙoƙarin zama a dining. Ba musu ta wuce ta je inda ta kira ta.

"Zuba min".

Zuba mata tayi kamar yarda ta umarce ta sai de kuma bata san me zata duba mata ɗin ba, dan haka abu ɗaya kawai ta zuba mata.

"Sai ke kuma?

Bata rufe baki ta ji kau. Ta mare ta, haɗiye kukan da ya zo mata tayi tana mai shanye shi.

Tace, "Ki yi hakuri".

Dan bata san me tayi ba kuma, ita tashin hankali ba san shi take ba kwata kwata.

"Ki zo komai dake wurin nan".

Ba musu ta zuba mata ta juya zata tafi, tace ta tsaya ta ta gama ta haɗa mata ruwan wanka. Haka ta jira ta a tsaye ta gama yangar ta, Hajiya na jin su bata ce komai ba. Ɗalhat ne ya shigo yaga yarda take share ƙwalla ya kalli Safiyya ya kalle ta. Bece komai ba ya rike hannun Ameerah ya damƙo hannun Safiyya ya fara jan su.

"Bro D ina zaka je da mu?

Banza yayi mata har suka zo suka wuce su Hajiya ganin haka yasa Hajiya tashi ta bi su shima Musaddiq bin su yayi. Yana zuwa ya buɗe balconyn Abba da ya san a irin wannan lokacin yana can tunda weekend ne baya fita. Yana zuwa ya watsa su a gaban sa daga ita har Safiyyah nema suka yi sh faɗi dan yadda ya wurga su sai kace kayan wanki. Safiyya kam sai da taje ƙasa ta faɗi warwar dake jiki ba kwari ba, yayin da Ameerah kuma ta ja ta toke bata je ƙasa ba. Kallan sa kawai Abban na su yake yi babu ko ƙiftawa........

Continue Reading

You'll Also Like

16.1K 1.8K 22
In the remote village of Dumurkul, Rayhan had life pretty hard. She's simply a 15 years old Fulani girl that knew pain in all shades, and all she wan...
388K 13.2K 53
Anhay Sharma:- Cold business tycoon who is only sweet for his family. He is handsome as hell but loves to stay away from love life. His female employ...
303 52 15
Can't you understand it's over between us Khalil for 8years you have done nothing to me but torture you are a beast and I am done with this marriage...
12.8K 1.2K 21
Hanan love Sadeeq dearly. She loved him since she was young. Hanan never got the chance to tell Sadeeq and he fall in love someone else. She was com...