biyayya.... 65-66

820 40 10
                                    

💎💎💎💎
   💎💎💎💎
     💎💎💎
        💎💎

*BIYAYYA*

*Story...writing*
   By
   *Maryam Abdul*

*Typing.....*⌨

   💫 *DA BAZARMU WRITERS ASS*💫

We are here to make you happy.... Smile and educated to realized that we are the best among all..... *DABAZAMU MUKE TUN'KAHO*💃💃

Masoyana ina matuqar alfahari daku....masu comment, vote, like and share duk inatare daku...wad'anda banasamun damar mayar musu da amsa kuyi haquri kunji...amma kuna raina sosai.

Wannan shafin nakine, gaba d'aya littafin sadaukarwane gareki *Nana Khadija* ina alfahri dake sosai.

Kuyi haquri readers nayi mantuwar page ana baya zansa *page 63-64* sai nasa *62-63* amin afuwa duk d'an adam tara yake bai cika gomaba....nagode.

*page....65-66*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

-------------Koda ta miqo mata abincin girgiza mata kaita alamar bata ci, duk yacce Fiddausee taso Dije taci abincin hakan baisamuba.

Duk da yau tafara zuwa makarantar amma hakan baihanata jin dad'in makarantar ba dan sosai makarantar ta burgeta matuqa.

Koda akatashi tana kallon kowa ana zuwa d'aukanshi suna tafiya itakam sai samun wajetai tazauna.duk dadai dad baicemata za'a zo d'aukantaba amma ita inatason hanyar gidanma balle tace zata koma dakanta.

Tana cikin wannan tunanin ne taji andafata, d'ago  da kanta tai takalli wanda yadafatan, Fiddausee ce tsaye tana kallonta cikin tuhumar zaman me takeyi anan ita kad'ai?

Dije ta d'an gyara zamanta kafin tace" ba'azo d'aukata bane"

Fiddausee tai murmushi kana tace" kizo muje sai drivern ya saukeki wace unguwa kike?"

Dije tai murmushi tace" ah bakomi nagode nasan suna hanyama"

Tana qarasawa taji muryar auta na fad'in" auntynmu"

Waigawatai cike da fara'a ta kalli autan tace" ah auta harkun taso?"

Auta ta gyad'a kai kawai, sai alokacin ta lura da Fiddausee dake tsaye, hannu ta miqamata tare da murmusawa.

Ganin hakan yasa Fiddausee n miqamata nata hannun itama fuskarta cike da qyataccen murmushi.

Cikin qanqanin lokaci suka bud'e babin hira tsakanin Fiddausee da auta, sai Dije tamusu magana ganin abin nasu ba qaraubane.nan sukai sallama tare da musayar lamba.

Ko amota Dijece tai tayiwa auta fad'a" wai akanme daga had'uwa da mutum rana d'aya lokaci d'aya zata sakewa mutum fuska"

Auta tai murmushi tace" aunty ancefa mutane rahmane shiyasa, kuma wllh kallo d'aya namata naji kawai ta kwantamin"

Dije ta ta'be baki kafin tace" uhmm kiyi dai ahankali" daga haka bata sakya cewa wani abuba ahaka har suka qarasa gida.

Koda suka qarasa gida agajiye Dije ta koma kaitsaye d'akinta ta wuce auta da mom nata tsokanarta wai" ahaka za'adinga zuwa school d'in ana dawowa" ita dai batace kanzil ba inbanda haurawa sama datai.

Tanashiga ta fad'a kan gadonta tare da mimmiqewa, tana nan kwance har auta tashigo ta taddata.

Kallonta tai tace" kaddai aunty kice tund'azo kina zaune ahaka ko uniform d'in ma baki cireba?"

Dije taja tsaki kafin tace" hmm kedai bari Allah duk jinaki jikina namin wani iri kamar ana sassarawa"

Auta ta qyalqyale da dariya tare da nuna Dije tace" kai aunty daga farawa"

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now