Biyayyah....!

814 39 3
                                    

💎💎💎💎💎
💎💎💎💎
     💎💎💎
        💎💎

*BIYYYAH*

   *Story...writing*
By

   *Maryam Abdul*

Wattpad:@maryamad856

*Typing.....*⌨

💫 *DA BAZARMU WRITERS ASS*💫

We are here to make you happy.... Smile and educated to realized that we are the best among all..... *DABAZAMU MIKE TUN'KAHO*💃💃

Da bazarmu writers ass. Fatan alkhairi ga kowa da kowa.... Ku kasance cikin farin ciki da annushuwa na har abada.
 

Wannan shafin naku ne:

*Auntyn Mubasshir*
*Aunty Maimunah O.G*
*Aunty Mardiyya*
*Mama queen*
*Mrs.Abubakar*
*Salmah M.D*
*Queen Ameena*
  E.T.C wad'anda ban ambata ba kumin uzuri.

*page.... 51-52*

Bismillahir rahmanir raheem.

---------Ranshi ya matu'kar 'baci sosai, lallai ma shi zasu yiwa haka.tashi yai ya fice daga falon ganin hakan yasa Imran shima binshi a baya.

Tsaye ya tadda shi dafashi yai kafin yace" sorry fa aboki kasan kai d'in ne sai da haka, na lura akwai abinda yake faruwa atsakanin ku Sam ba wata jituwa sosai"

Ture hannun nasa yai tare da Jan tsaki kafin yace" amma ka rasa ta inda zaka 'bullo Dan jin meke faruwa sai ta sharri? to yanzu ai kaji dad'i tunda anmin abinda kakeso ko?"

Imran yai murmushi yace" nifa ba Dan ama fad'a nai hakan ba, a tunanina mom zata yi bincikena ne sabida jin kayi hakan ni banso ma ta tsaya a Iya fad'an ba"

"To dad ai kai zaka Iya ko" ya fad'a a 'kufule.

" Sorry ba wannan maganar ai, nidai yanzu muje na ci abinci na wuce" Imran ya fad'a.

Ashraf yaja tsaki yace" abinda ka sani kenan, banza acici mala'ikun tauna, to wllh sai dai in kar kaci abinci indai sai na rakaka"

Imran ya juya yana fad'in " bakomi dad'in abinma nasan hanya ai"

" kai kasani, banza munafuki" Ashraf ya fad'a da Dan d'aga sauti yadda Imran d'in zai jiyo.

Ai kam ya jiyo shin, sai dai kawai murmushi da yai ya wuce ciki.




........Dije kam mom sai da Tasha faman rarrashinta sannan tai shiru, Dan daga kukan 'karya kuma aka koma na gaske.

'D'aki ta koma ta janza kaya, sannan ta sakko 'kasa wai zata tayi girki, ba yadda mom batai ba ta hakura amma ta'ki, Dan ita wai sai tayiwa ya Imran d'in ta girki, tunda yace" nata zai ce" .(nikam nace"oh su Dije za dai ai karanbani dai ko, Imran zakaci jagwalgwalo kenan")


Ba ita ta fito daga kitchen d'in ba sai wajen awa d'aya da rabi a hakanma duk tayi du'ku-du'ku da ita yadda kasan ba d'azu tasa kayan ba.Dan koya ta 'bata hannun ta a jikinta take gogewa, a hakanma mom na kula tana hanata.

Girkin kam sai da ya babbake wai shima a haka mom na duba mata, Dan da mom tace" ta sauke shi haka sai data barshi ya Kara mintuna kusan goma, Allah ya sotama jalof d'in taliya ta masu da taso ta mai d'an malelen da tace, mom tace" basu da tsaki" hakan yasa ta dole ta ha'kura.


Dukkan su zaune a dinning yayin da Imran keta yiwa mom rigima " wai shiga yinwa yakeji har yanzu ba'a gamaba"

Mom tai dariya tace" wllh Imran ka rage ci, gashinan kana son d'orawa kanka wata jarabar ta in baka ciba baka jin dad'i "

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now