biyayy....70

816 34 33
                                    

*BIYAYYA*

Writing by
*Maryam Abduul*

Wattpad@Maryamad856

*Page...70*

BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

---------Duk wad'an nan kwanakin dasu hajiya kaka suka qarasa shi sunyi shine bisa kitchen ita da dije, kuma masha Allah duk wani abu da takeso taga dijen ta iya ta iyashin kuma tana fahimtar sa sosai, daya kema takanyi jotting din wani gudun mantuwa.

Sukam su mom da auta hatta da Hanne nasu aikin kallone, kuma koya akai abincin sai an lashesa.

Alhmdulillah awannam fannin kuma dije ta fara samun lambar yabo, wanda hakan ya qara jamata tsana wajen ashfa, dan tasan badan komi hajiya kaka ke koya mata ba sai dan Ashraf, itakam sanda tanema catai bazat koyamata ba, kenan itance battaso tare da Ashraf d'in kenan?"

Kwanan da suka diba zasuyi ya qare haka suka tarkata yanasu-yanasu suka koma garinsu.

Koda zasu tafi hajiya kaka dabdije kamar kar su rabu, dan sunyi matuqar shaquwa tare a iya wannan d'an zaman dasukai.

Sai da tasa dad yamata alqawarin zuwan da zasuyi har da ita za'azo sannan driver yajasu zuwa airport.

Dije ma jitake inama basu tafiba, dan sosai tsuhowar tashiga jikinta, gata tsohowa wayayyeya dan sau tari duk hirar da zasuyi da ita tofa akan abin qaruwane, hakan yasa kullun take maqale da ita, wannan zama nasu yasa takoyi abubuwa da dama, dan yanzu dije sai tai wanka sau uku ko biyi a rana ba kuma wai dan batta jin dad'in jikintaba, ko intayi aiki tagaji a'a haka kawai, wannama ta koyi hakanne wajem hajiya kaka, su humra kam da kwalakca sai ambaliyarsu takeyi kusan koda yaushe, harta da turare wannan koda baida qamshi sosai batta barinsa haka banza.

Wannan duk aikin hajiya kakane, domin ita tasabar mata da wannan d'abi'a akan ta dinga zama koda yaushe cikin qamshi hakan nasa miji yaji kullun yana sha'awar ra'bar matarsa, bawai da ya dosheta yaji tana tashi ba.


Bayan tafiyarsu hajiya kaka da kwana biyu su dije suka koma school, sosai taji dad'in komawar tata, duk da fiddausee na fushi da ita akan batazo gidansuba.

Sai da dije tace mata itama ai batazoba me ya hanata zuwa?"

Jin hakan yasa fiddausee yin dariya dan tasan su take ta rama, wato kar dai tazama itace kad'ai mai laifin.

Itakam fiddausee anata 'bangaren taso zuwa kodan yayanta daya matsamata da san samo mata lambar wayarta, duk da tasan dije bata da waya a hannu, amma koda ta gayamai catai bai yaddaba, sauqinta daya ma da tasamu shine tafiyar dasukai, taje abuja ita da mamanta, hakan yarage kaso 80% daga matsin da yake mata akan dijen.

Bayan anagama duk abinda zasuyine dayake ranar da aka koma ba'a karatu za'ayi bitar aikin da akaine abaya ataqaice, hakan yasa ranar basa komawa gida da wuri.

Driver da yadad'i da zuwa yana zaman jiranta, yayinda Hisam ke zamn jiran fiddausee wanda azahiri harda maaoyiyar tasa, dan yarigada yagama yadda sonta kawai yake, kuma bazai bari ta kubce maiba insha Allah.

Yayima kansa alqawarin bin duk wata hanya dazata sadashi da ita, wacca kuma zata sa tafahimci irin son dayake mata.

Yana nan zaune cikin mota ya hango tahowarsu hakan yabashi damar bud'e murfin motar ya fito tare da jingina da jikin motar game da hard'a hannayensa asaman qirjinsa.

Suna qarasowa fiddausee tace" lah yaya yau da kanka kuma, kodai akwai gagarumin abinda yafito dakai?"

Maka mata harara yai kan yace" in gulma kikesin yi sai nakoma?"

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now