BIYAYYAH....

1.1K 55 4
                                    

🔥🔥🔥🔥🔥
     🔥🔥🔥🔥
          🔥🔥🔥
               🔥🔥

*BIYAYYAH....*

By

*Maryam Abdul*



💫 *DA BAZARMU WRITERS ASS.*💫

We are here to make you happy, smile...educated and realized that we are the best among all *DA BAZARMU MUKE TUN'KAHO....*💃💃💃

  

   *Dedicated to you my Fans, Allah yaɓar ƙauna*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*


*page 15-17*

 
-------------- Koda ya fito ko kallonsa baiba, wadrop d'insa ya nufa, ya fito da kayan da zai sanya, sai da yagama abinda zaiyi sannan yai shirin kwanciya dan hutawa, domin a yanzu ba abinda yafi bu'kata illa hutu.

     Imran dake kan sofa ya kalleshi tare da yin wani 'kaya taccen murmushi yace " ba dai kwanciya zakai ba?"

      Ko kallonsa baiba bare ya saran zai bashi amsa. Imran ya girgiza kai yace " ni bari na wuce, ma had'u gobe, in kunyi waya da 'kawas ka gaida min da ita"

     Wani wawan tsaki yaja tare da jan blanket d'insa ya rufa. Imran kwa  dariya yai yace kaji dashi, banza anaso ana kaiwa kasuwa, yana gama fad'ar haka ya fice daga d'akin.

    Koda Imran ya fita, mi'kewa yai zaune ya kalle agogo yaga 2:48, kana ya juya ya kalle  kansa a madubi, " lallai ba shakka dad yana san kassara rayuwarsa, haba dubeshifa amma kamarsa ace za ai wa auren dole, ina sam abinda ba zai yiwubane, to taya ma zai samawa kansa mafita.alhalin wad'anda yake sa ran zasu temaka masa duk sun 'ki. ga wannan banzan yana so ya samasa ciwon ka" wannan tunanin ne ya fara addabarsa ganin bashi da mafita illa yai alwala yai salllah ya mi'ka lamuransa ga Allah, hakan kwa akai domin ya dad'e yana gayawa Allah bu'katunsa da kuma neman za'bi a gareshi, kafin ya kwanta.




  
*******       ********

    Ɓangaren su Dije kuwa suna shiga cikin gidan ta faɗa ɗakin iya, kan cinyarta ta aza kanta tare da faɗin " wash! Iya wllh du na gaji"

    Iya ta shafa kanta tace " to 'yar gidan iya me kikayi, baƙin naku sun tafine?"

    Miƙewa tai zaune tace " ehh, Iya alqur'an suna da mutunci, kinga yadda suka dinga nan-nan dani, kamar wata ƙanwarsu da suke ciki ɗaya."

   Iya ta washe baki tace " ah kice sun miki, to shi wanda yazo ganin naki, yayi bashida matsala?"

 
    " haba Iya, ana maganar suna da kirki wace tambaya za ai akai, ai nida nasan haka 'yan birni keda mutunci da daraja 'yan Adam da ban ƙisuba tun fari da kawu ya kawon zancan, ni dama abinda nake gudu shine kar naje nai yoyan fitsari ko su wulaƙan tani"

   Iya tai mutmushi tace " ai ku 'yan zamani ne, amma mu sadda akamana auren muna nawa, kuma ba abinda ya samemu, kinga ki kwantar da hankalinki kinji jikalleta"

   " shikkenan Iya, nasan inda ke ba mai cutata ko?"

     " eh man waya isa ya taɓamin ke, ina raye"

    Jummai dake zaune kusa dasu tana kallon ikon Allah, lallai Dije shu'umace, kamar ba yanzu tagama tafka mai rashin mutunciba, amma tazo gaban iya tana ta yabansa, kamar ba abinda ya faru, gyaran murya tai tace " uhhm! Iya kinsan wani abu kuw...."

    Cikin sauri Dije ta tareta da faɗin " au na manta kince kinajin yinwa, muje muce"

   Iya ta kalli Jummai tace " amma ki dai Allah ya shirya, to nan ɓaƙin kine da bakisan hanyar madafarba, ni wuce ko bani guri"

     "ehh man, kamarfa ba 'yar gida ba, nima haka nace mata iya" Dije ta faɗa cike da murmushi, tura Jummai tai tace "muje ko."
   
 
   koda suka shiga ɗakin Dije, kallonta tai tace " wllh ki fita idona Jummai, bawai mun gama magana dakeba"

    Jummai ta kalleta tace " to ni wai wani abu kikaji nace, nifa maganata da zanyi ba'akan ki bane"
   
   
      Dijr tace " to akan uwar mene, narantse sai na rage wani abu acikin wanda zan baki, yarinya dani kike zancan"
   
   
    " Kai kefa kin fiya rigima alqur'an ba'akai zanyiba, ai baki tsaya kinji me zanceba"
   
   
   
    " au nice nafiye rigima, an sake rage wanima, rayinya ki ta magana ina ragewa"
   
   
    Cikin sauri Jummai ta durƙusa tare da riƙo hannunta tace " haba ƙawalliya kinsan bama haka dake dai, dan Allah kimin rai kinji"
   
   
    Cikin haɗe rai da hura hanci Dije ta kalleta tare da faɗin " naji, tashi, in kika kuma kuma wllh saina rage raɓi ma"
   
   
    " ah! wace ni a gaban yaya babba, ai bama za asomaba"
   
   
    " muje ni muce abincin, banza kura kawai" Dije ta faɗa.
   
   
   
    Jummai tace " naji, kuma meyi dai, muje kuma kuɗine sai nace" ta ƙarasa a hankali yadda Dije bazata jiyutaba"
   
   
    " me kikace yarinya" Dije ta tambaya.
   
   
     " wa! ni, ba abinda nace, nina isa"
   
Nana dai suka wuce madafa dan ɗebo abinci.







  ........Ashraf kwa be farkaba sai ƙarfe huɗu na yamma, koda yatashi bayan yai addu'a tsaki yaja, dan beso yakai i yanzuba yana baccinnan,. cikin sauri ya faɗa banɗaki ya soma yin brush, sannan ya antayawa kansa shower dan wanka.yayi kusan 30mnt aciki kafin ya fito, nikam nace "kamar mai canja halitta". Koda ya fito gaɓan dressing mirror ya nufa, ya daɗe nanma yana ƙaƙale-ƙaƙalenshi tukunna ya nufi gabon wadrop ɗinshi, kaya masu kyau ya ɗauka yasa kana ya feshe jikinsa da turaruka masu daɗin ƙamshi.saida ya gama duk abinda zaiyi sannan ya sakko ƙasa dan bawa ciki haƙƙinsa, inkuma dad na nan shima zaiso sutattauna duk da yasan ba wai lallai ya yadda da maganar da zai zomai da itaba.


Bakowa a falon direct dinnind area ya nufa sai dai ƙwalam ba komi akan table ɗin, wani wawan tsaki yaja tare da haurawa saman mom ɗinshi, sai da yai sallama sannan ya nemi izinin shiga ( wannan ƙa'idar gidance, indai ɗaya zai shiga ɗakin ɗaya sai yayi sallama tare da neman izini, musamman akan iyayen nasu). Izini ta bashi kana ya tura ƙofar yashiga, tana zaune kan gefan gado, ya ƙarasa ya zaune ƙasa nan kusa da ita, saida ya fara gaidata tare da faɗin " barka da yamma mom, fatan nasameki lafiya?"

" lafiya lau my son, fatan kaima haka?"

  " nima haka, amma akwai matsala mom fa gaskiya" ya ƙarasa cike da shagwaɓa.

  " to meya faru da ɗan nawa?"

 
  " mom cikina, sai kukan yinwa yake, kuma na duba dinning ba komi"

"Ayya sorry, yau ba mutuminka akai ba, munyi alele ne kuma kai kasan baka ci, barin inzo in maka koda indomie ce"

Cikin zunɓoro baki yace haba mom, yanzu fisabilillahi haka ake, ni kenan saina zama bare a gidanmu, jiyama fa haka kukai da safe kuka dafa abinda banaci, yanzu shine kuma aka maimaita da rana."

Kallon shi kawai take kafin tace " to yallaɓai an daina, shiyasa nace ai gwara amaka auren ko ka samu mai dafama, adai namana ƙorafi dai ko"

Jin ta anbace aure yasashi haɗa rai tare da faɗin " dad yana cikine, ko ya fita?"

  " a'a, yana ciki, amma dai naji yana cewa zai yi wanka ya fita, saikai sauri Allah yasa bai shiryaba, lafiya dai ko?"

  "Ah!  bakomi mom, kinsan ance tsakanin uba da ɗa sai Allah, ki dafan kawai indomie ɗun da ruwan shayi bari in sakko" yana ƙarasa faɗa ya haura part ɗin dad.

     Yawan comment naku, shine ƙwarin gwiwata.

Comment, and
  Sare.



   *Miss Gentle taku ce...*✍✍✍

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now