BIYAYYAH...

990 43 0
                                    

🔥🔥🔥🔥🔥
🔥🔥🔥🔥
  🔥🔥🔥
  🔥🔥

*BIYAYYAH*

By
  
  *Maryam Abdul.*


💫 *DA BAZARMU WRITERS ASS*💫

We are here to make you happy, smile..and educated to realized that we the best among all.... *DA BAZARMU MUKE TUN'KAHO*💃💃💃


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

*page... 21-24*


.........Imran ya kalleshi yace " oh naji, yanzu dai ina zamu  kakemin wannan Kiran gaggawar haka?"


" bako ina , amma  ina son karakani wani wajene ba dad'ewa zamu yiba"

  " amma yana da kyau nasan ko inane hakanko?" Imran ya fad'a.

" dallah ba nisa Karka dameni da surutu"

Imran yakalleshi yace " bafa zaiyiwu ka d'akkoni har gidan muba sannan kadinga juyani, ina Sam bazaiyiwuba"

" naji, zanje nai siyayyane kayana sun 'kare, kuma ni banason nace da dad yaban kud'i, yanzu sai yafara fad'anshi da nai aure bazan dinga tambaye-tambayeba, inada aikina nakaina, kuma na mallaki abubuwa da dama, shiyasa muje na cira anaka asusun zan biyaka daga baya"

Imran yai dariya yace " to duk baga irintaba, aini wllh dad ya matu'kar burgeni da ya kafa maka wannan dokar tacewa" sai kayi auren zai sallameka, amma yanzu kana 'kar'kashinsa", komi saida izininsa, kaga kayi zuciya kayi auren ai ko"

" kaga malam Niba surutu  nace kaminba, aure ra'ayinane nayi yanzu ko ba yanzu ba, zaka bada ATM aciro kud'i ko kowa a'a?"

" muje yana iya"  imran ya fad'a cike da kunshe dariyarsa.




.......koda mom tasami dad da zancan ba'karamin fad'a tasha ba, danme zata dinga d'aurewa yaro baya haka, cike da fushi yace " na fahimta bazai tab'a fahimtar al'amuraba , Dan haka na yake shawarar tsai da ranar aure  nan da wata d'aya, kuma ki gayamai ba fashi, da zarar wata d'aya yacika to aure yazo, Dan haka yashiraya, in  baya bu'katar shirin to Abu yayi dai-dai, muzamu shiryashi"

" amma abban yara, ya kamata ayi abubuwan nan anutse, kosu dangin yarinyar na tabbata basu shiryaba, Kaduba lamarin fa, kar ai Abu cikin gaggawa"

Murmushi tai yace " nafiki sanin koya ahlinta suke, sannan  bazamuyi Abu muzo muna da nasaniba"

" amma dai duk...."

" ya isa ! Kiyi abinda kawai nace, bayan haka aje afara shiri daga yanzu, na kuma d'ora miki alhakin kula da duk wasu kaya da dangin miji keyiwa amarya" yana gama fad'a haka ya fice daga d'akin" tabbas sai yayiwa tufkar hanci".


Itakam mom ba abinda take anbata sai fatan alkhairi garesu, yasa kuma  son ya yarda da 'kaddararsa yadda tazo Masa nan haka".

  



------- Shikam dad na fita wayarsa yaciro daga aljihu yashiga Kiran wata number, bayan sunyi sallama da gaishe-gaishensu na manya naji dad na fad'in " inafata kana gida ?"

Bansan mai akace daga d'aya bangaren ba saidai naji dad na 'kara cewa " OK to ganin tahowa, sai Nazo, to madallah" nan ya kashe wayar. Motarsa ya fad'a tare da umartar driver da yajashi zuwa *Rimin gado*. "To fa ah lallai abin azumin be."

Da yake gudu yake sosai basu wani dad'e akan hanyaba suka 'karasa. Sosai yasamu tar'ba daga wajen kawun, nan suka 'kara gaisawa. Dad ne yayi gyaran murya tare da fad'in " ina fata abinda nazo muku dashi bazai kawo wata matsalaba?"

Kawu yai murmushi yace " haba Alhaji karma asoma 'Yar haka, muna jinka me ke tafe dakai haka?"

Dad ya 'kara gyara zama yace " bawata magana bace illah akan auren 'ya'yan nan, nayi wani tunani ne nace me zai hana asa nan da wata d'aya?"

Murmushi kawu yai  yace " ah alhamdulillah wannan ai kyakkyawan labarine, ni dama Dan kace abarsu su fahimce juna be, amma Allah na tuba muda akamana auren fahimtar junan mukai, basai da muka tareba muka San juna, kuma gashi har muka kai I yanzu ba wata matsalaba, hakan yayi dai-dai, Allah ya kaimu lokacin da rai da lafiya"

" ameen thumma ameen" dad ya fad'a kana yaci gaba da fad'in " to  in hakane badamuwa na taho da kud'in nagane inaso, sannan kuma sai asa ranar ko?"

" ah to masha Allah, bari nasanar da jama'a ko, koda mutum Biyar be sai a shaida hakan" kawu ya fad'a fuskarsa cike da d'unbin far'in ciki.

Cikin abinda baifi minti biyar ba jama' a suka taro kusan mutane goma, cikwa harda baban babbar 'kawar amarya wato Dije, Wanda dama duk abinda kawu zaiyi to da shawararsa yakeyi, domin sud'in had'in Allah ne , tare suka taso har da baban Dije. Nan dad ya bada dubu hamsin kud'in zance, sai dai kawu take ya had'a rai  shi Sam bazai karbi dubu hamsim ba, sunyi yawa, da 'kyar dad ya shawo kansa  sannan ya amsa, sai da aka kammala  komi cikwa harda sa ranar aure wata guda sannan dad yayi sallama da su.

Cike da farin ciki kawu yashiga cikin gidan , Iya ce zaune ita da Dije tana ta fama da ita akan tsifar kai, murmushi yai yace " ah yanzu ke tsifarma sai anyi fama dake haka, Allah ya kyauta"

Iya ce  ta kalleshi tace " ah to kaima dai ka fad'a, sai kace wata yarinyar 'karama"

Dije kam zun'buro baki tai tace " kai iya to da mece, ai ni har yanzu Ban girmaba"

" kyaji dashi dai" iya ta fad'a ta dungure mata kan.

" ash! wayyo kaimna" Dije ta fad'a cike da tsantsar shagwa'ba.

Kawu ne ya kallesu tare da dariya yace " kud'in dai sai Ku, bame Shiga tsakaninku, yanzu dai akwai magana Dana keson muyi"

"To Auwalu wace magana ce haka?" Iya ta tambayeshi.

Sai da ya zauna kana yace " bakomi bane illa d'azo Alhaji, baban yaron da zai aure Dije yazo yasameni da maganar ya naso ASA ranar auren, ya kuma bada kud'in Nagani ina so, sai dai batare da nazo na gayamiki ba na yanke hukunce , domin kowa na amshi kud'in, kuma ansa rana wata d'aya."

Cikin fad'in ciki Iya tace " ai bakomi d'annan , Allah yakimu lokacin yasa kuma muna da rai da lafiyar da  za ayi damu"

Shima cikin farin ciki yace " ameen Iya"

'Kululu cikin Dije ya kad'a" kanbu, kar dai ace da wannan mugu za amata auren, dagaskene wai dama maganar, cikin sauri ta mi'ke tare da sakin kuka " lallai sai nayi wani abun yana zun nan"ta fad'a

Cikin murya ta kuka Dije tace " Nidai alqur'an bana sonshi, kawu, Iya Ku maida musu da kud'insu wllh banason shi"

A tare suka jiyo, Iya tace me like cewa haka Dijato na, kinsman kowa hakan ba dai-dai bane"

" Ni dai wllh Iya banason auren nan, Ku mai da musu da kud'in su kawai"


*Miss Gentle taku ce....*✍✍✍

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now