BIYAYYAH.....

801 34 0
                                    

Biyayy
💎💎💎💎💎
💎💎💎💎
     💎💎💎
        💎💎

*BIYYYAH*

 

*Story...writing*

By

   *Maryam Abdul*

*Typing.....*⌨

💫 *DA BAZARMU WRITERS ASS*💫

We are here to make you happy.... Smile and educated to realized that we are the best among all..... *DABAZAMU MIKE TUN'KAHO*💃💃

*page....31-32*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

-----------Alllah ya kuwa ba su sa'a suka samu ticket d'in, amma ba su suka tashi ba sai 'karfe 11:30am.
   cikin IKON Allah suka sauka lafiya, gidan su suka fara wuce wa dan hanzarta wa wajen kai ammi d'in gidan gaskiya, sai da suka dawo sannan shida baban Hindatu suka zarce asibitin da aka kwantar da Abi d'in shi. ha'ki'ka duk wani mai tausayai da imani a zuciyar shi yaga halin da Abu yake ciki sai ya zubar masa da hawaye sosai, Dan ba kyan gani Ko ina na jikinsa asalu'be yake fuskarsa ce kawai ta tsira. Ba 'karamin kuka malam Adam ya dinga yi ba, sai da baban Hindatu ya tsayar da nasa hawayen ya shiga rarrashin shi. wajen Dr. da ya kar'bi shi yake kula da shi suka nufa , nan malam Adam ke tambayar " ko za a iya fidda shi ko da India ne  ko wata 'kasar da za'a iya samun cigaba anan?"

Nunfasawa ya yi ya ce " I to, za'a iya hakan, akwai wani Dr. da ya sani a India zai yi masa magana sai ya had'asu da shi" nan suka shiga yi masa godiya.

Bayan sati d'aya suka kammala duk wani shirye-shiryen su na tafiya India, jirgin 'karfe hud'u na yamma suka bi, ya samu kulawa sosai a wajen likitocin, kuma ma sha Allah an sami nasara, Dan cikin abin da baifi wata biyu ba jikinsa ya fara normal.Wanda suma Kansu sunyi matu'kar farin ciki da hakan.

Watan shi hud'u cif ya koma normal, sai dai duk jikinsa ya zama mai ta'bo, ranar da suka shirya zasu dawo gida Nigeria aranar wani baban tashin hankali ya afkar musu, domin kwa  jikin Abu Ne ya dinga wani irin kakkarwa, nan da nan  aka nufe da shi emergency, nunfashinsa Ne ya soma barazanar d'aukewa, nan fa hankalinsu malam Adam ya matu'kar tashi.Allahu Akbar cikin abin da baifi minti goma ba Allah ya d'auki kayansa, wannan mutuwa ta Abu ba 'karamin girgiza su malam Adam ta yi ba, *"Allah sarki Ashe sau'kin na tafiya ne Abu "* nan da nan aka shirya gawarsa suka 'd'akko hanyar dawowa gida.ko da suka sauka mutane sunyi matu'kar jimamin rashin da akai, Dan kwa Abu mutum Ne shi mai karamci sosai da sosai, ga San jama'a, kowa yana yabawa da halayensa.cikin mintoci ashirin akai kai Abu gidansu na gaskiya." Allah ka ji'kan musulmai...muna in tamu tazo kasa mu cika da kyau da imani...ameen"

Saida akayi arba'in d'in su Abu sannan suka juyo gida garin Abuja, nan ma jama:'a suka dinga taya malam Adam jajaan rashin iyayensa.

------------Bayan shekara guda komi yazama normal a wajensu, Dan sosai ng Hindatu ke 'ko'karin kawar mai da duk wata damuwa, kuma masha Allah yana samun nasara.cikin IKON Allah hk kuma ta'ba rainaon 'ya'yanta Wanda a yanzu hakama duk sunyi wayo.

Yanzu malam Adam linkafa ta fara ci gaba Dan ayanzu haka ya zuba hannun jari sosai da 'yan kasuwa, kuma alhmdulillah suna samun riba mai yawwa, kuma wacca ba riba a cikin ta.

*Bayan wasu shekaru*

---------shire take sosai na tar'bar mijin NATA, Dan yayi tafiya zuwa jumaita, kuma yau take saran dawowarshi, kayan abinci kala-kala ta shiryamai na musamman.Ibrahim Ne yashiga da hud'u ya na fad'in " mama yai daddy zai dawo ko, yace zai suyo mana alawoyi da yawwa ko?"

Murmushi tai tace " ehh 'yana gidan daddy, saida kuma in ya dawo Ku mata dani"

Dariya yai irin tasu ta yara yace " ai ba zamu manta dake ba mama"

Shafa Kansas tai tace " yawwa 'yana albarka, to maza ake ai wasa, amma banada 'bata kaya fa, kinji"

" to mama" ya fad'a yana mai barin wajen.Dariya tai tace " ohh ni 'yasu, wannan yara da San shan kayan Zaki"

Yana nan zaune har wajen biyar na yamma wayar tace tai 'kara sunan sa tagani akan screen d'in wayar, a hankali ta d'aya tare da karawa akunne, sallama tai, daga d'aya 'bangaren akace " kece matar mai wayar nan?"

" ehh nice, lafiya dai ko, ina mijin nawa ?". ta tambayar arud'e.

"lafiyar sa lau, amma in bazaki damuba muna San ganinki a office d'in no 1998"

" to kawai tace ta kashe wayar" cikin sauri yasa driver ya jata  zuwa gidansu , nan Taiwan mamanta bayani, alokacin kwana babanta na nan, nan yace " ta zauna shi bari yake yaji " fafur ta'ki, Dan tace " bazata zauna ba" haka sukavrankaya shi da ita.koda suka isa office d'in nan suka neme jin ba'asin Kiran nasu.

Wanda yai magana da itane ya fara yimusu bayani dallah-dallah kamar haka:" da farko dai muna tuhumar mijinki da safarar kayan mage, wannan dalilin Ne yasamu zaunar dashi a office d'inmu, kuma nan da sati biyu dazarar mungama bin cike zamu turashi koto, Abu na biyu shine kun kuna da halin samo lauya to zaki iya, amma ba shakka muna kamashi dumu-dumu da hodar iblis a kayansa, wannan shine gaskiya maganar"

Cikin kid'ima da rud'ewa Hindatu ta kalleshi tare da fad'in " ina Sam wllh wannan maganar 'karyace , mijina bazai ta'ba aikata wannan d'anyan aikinba, Dan Allah Ku salam n mijina"

Offican ya kalleta yace " Hajiya abinda na gaya miki dai d'azun to shine , kuma mu bama kama mutum batare da hujjaba, Dan haka kalle wannan kayan kiga" ya 'karasa yana me muna mata kayan da suka kae'ba daga wajensa.

" wllh 'karyane, sharri kawai akeso a Nasa , Dan Allah Ku sakarmin mijina, na ro'keku"

Murmushi yai yace " Abu d'aya zaki yi shine: indai har bada gasken bane to kiyi 'ko'karin samu lauya da kuma manyan hujjoji"

Har zata sakya magana babanta ya katseta ta hangar fad'in " ba damuwa, zamu 'ko'karta, amma zamu iya ganinsa?" Ya tambaya.
" ah ba matsalaba, zaki iya" nan yabada umarnin akaisu d'aki na 25.ke da sukaje yana zaune ya had'a kai da gwiwa, cikin sauri da sar'kewa tace " baban yara, me yafaru haka dakai, badai dukanka sukaiba"?"

Jin n muryar matar sane yasa ya d'ago Kansa, tashi tsaya yai tare da matsowa kusa dasu ya kama hannunta yace " Hindatu ya akai kika zo nan, ba abinda sukamin, kwantar da hankalinki"

" nasani, sharri kawai akema, nasan bazaka ta'ba aiakata laifin da ake tuhumarka dashi, duk rintsi kada ka ta'ba amincewa da hakan , ka gaya musu cewa baki bane Dan Allah, ko sara'bu dakai"

Sharema ta hawayen d sauka zu'bo kan kumatun ta yai kana yace " nasani, sharri akamin Hindatu, ki kwantar da hankalinki nsha Allahu zan fito da yardarsa, baba ka d'auketa ko kuma gida, Dan Allah karki wahalar da kanji, kimin alqawari"

Gyad'a mai kai kawai tayi, amma ita kanta tasan bazata ta'ba iya cire wannan damuwar ba, nan sukai sallama dashi akan jibi zasu dawo.koda suka koma gida fafutukar Neman lawyer suka shiga yi, Allah ya basu sa'a sun sano.

Ranar da suka ce zasu koma, tare dashi sukaje, nan ya dinga yiwa malam Adam tambayoyi, amma abinda basu gane ba shine " shi yace jakar wace, kuma da ita yataho, har yahau jirgi ta'ba hanunsa, kuma bakomi acikin, sai kud'ad'ensa da takaddu, to ya akai aka sauya jakar, Dan wannan ya tabbatar da cewa sauya ta akai, Dan ala'kab'mai Sharron nan" nan dai sukai sallama dashi, lawyan kuma yai musu alqawarin yin binciki acikin wannan al'amarin.

Koda ake koto, basu samu nasara Dan duk wani bin ce ki da sukai ba susami wata kyakkayawar hujja da zata tabbatar ba shi ya aikataba, sunaji suna gani aka yakemai zaman gidan yari na tsawon shekara bakwai tare da horo mai tsanani.kuka kan sunsha shi ba yadda suka iya, haka suka Bari kuton.

*Miss Gentle ta kuce......*

BIYAYYAHOnde as histórias ganham vida. Descobre agora