BIYAYYAH....

798 35 0
                                    


💎💎💎💎💎
💎💎💎💎
     💎💎💎
        💎💎

*BIYYYAH*

 

*Story...writing*

By

   *Maryam Abdul*

*Typing.....*⌨

💫 *DA BAZARMU WRITERS ASS*💫

We are here to make you happy.... Smile and educated to realized that we are the best among all..... *DABAZAMU MIKE TUN'KAHO*💃💃

      *Dedicated to you my Fans*
   
*page....35-36*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

----------Rayuwa nata tafiya, haka shekaru nata 'karuwa awajen mutane, ayanzu haka shekarun Ibrahim 22 yayinda Auwal keda shekara 20. kuma alhamdulillah suna samun nasara akomi da komi nasu, Dan yanzu Hindatu tana d'an ta'ba sana'arta na saida koko da safe, hakan yasa jama'a ke kiranta da *IYA* wannan girmama wace agareta, yayinda yazamo asalin komawarta Iya har bazakace ga sunan ta na gaskiya a gane taba.

Akwana atashi ba wuya wajen Allah, kamar yauma Abdallah da malam Tsallah suka fita kasuwa, daman akwai kayan daza suje cikin garin Kano su saro, Dan haka Abdallah Ne da wani yaron malam Tsallahan suka tafi.

Sabon gari, nan suka yiwa tsinke shagon wani alhj.Dan mutumin yana da kirki sosai da sosai, nan suka gama duk wani Abu da zasuyi, suka Baro cikin garin.kowa Nata hada-hada,yayinda sukuma aka shiga sauke musu kayansu.

"Malam ka yarda jakarka" yaji wani sauti ya fito daga bayansa, juyawa yai yana kallon 'bangaren da maganar ta fito, saidai tuni ya zarce da kallon kyakkyawar halittar da yai arba da ita, "gashi" ta 'karasa fad'a tare da mi'komai lalitar yasa.

Kar'ba yai yace "nagode"

  "Bakomi, tun a can kayar inata magana Ne ma bakajiba" tana gama fad'a ta juya da nufin komawa wajen da take.

"king a" ya ambata.

Juyowa tai ta kalleshi yace " ganaki ladan tsintuwa"

Murmushi tai tace " bana kar'bar ladan Abu, godiyar dakaima ta wadatar"


"shikkenan to na gode, zan iya Sanin sunan malamar, inba damuwa?"

Murmushi tai tace " Aisha, amma ana cemin indo, kaifa?"

"suna mai dad'i, amma Aisha ai yafi ko, ni kuma Ibrahim" nan dai hira tashiga tsakaninsu, har saida ya rakata wajen da take, nan take sanar dashi "ai sud'in fulanin rigar gabansuce, yanzuma ta fito saidawa Ne kafin la'asar zata koma"

Yai murmushi yace " yana da kyau hakan, amma gashi kin iya Hausa sosai, kamar kekika 'kir'kiro tama"

" ai Dan muna zaune cikin hausawa Ne, sabida muna huld'a dasu sosai, shiyasa"

"Lallai kam, to ni zan wuce, sai na dawo shan fura da nono ko?" Gyad'a mishi kai kawai tayi, shima ganin hakan yasa shi komawa wajen aikinsu.zuciyarsa ce ke da farin ciki, lallai ba shakka yasamu abinda ya dad'i yana kema, wato matar aure, ada baya da ra'ayin auren a wannan shekarun Nasa, amma ayanzu kam taji yana sha'awar yinsa.da wannan tunanin ya 'karasa wajen basu.

To haka dai abubuwa suke ta tafiya, yayin da soyayya mai 'karfe yashiga tsakanin Ibrahim da Aisha info, har takai a yanzu iyaye sun shiga cikin lamarin, Wanda kowa yayi farin ciki da hakan, duk da dai su dangin indo basu su hakan ba sun so ace ta aure d'an kuwa ba abte ba, amma ganin yadda takes on sa yasa suka aminta da hakan, dan suna matu'kar son ta, Nasa fatan wuce sun rasa, akan wani banzan dalili.


BIYAYYAHWhere stories live. Discover now