biyayyah.......!

819 42 1
                                    

💎💎💎💎💎
💎💎💎💎
     💎💎💎
        💎💎

*BIYYYAH*

 

*Story...writing*

By

   *Maryam Abdul*

*Typing.....*⌨

💫 *DA BAZARMU WRITERS ASS*💫

We are here to make you happy.... Smile and educated to realized that we are the best among all..... *DABAZAMU MIKE TUN'KAHO*💃💃

*page.... 41-42*

*Wannan shafin na kune masoya....ina godiya...Allah ya bar zumunci.*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*



--------A kwana a tashi ba wuya awajen Allah....komi akasa masa rana sai yazo, yau ce rananr da su dad suka dad'e suna jira kuma gashi tazo.domin kwa yau 20-03-2016 , Wanda Yakama ranar litinin dubban mutani suka shauda d'aurin auren *MUHAMMAD ASHRAF JABIR DA KUMA KHADIJA IBRAHIM ADAM* akan sadaki 'kalilan, lakadan ba ajalan ba. Bakin dad ya'ki rufuwa, Dan yana jin ya sauke wani babban nauyi dake wuyansa, sai yanzune yaji hankalinsa ya kwanta.

Yayin da 'bangaren ango da amarya abin ba haka yakeba, domin kwa Ashraf jiyake inama Allah ya d'au nunfashinsa, da dai ya zauna da wannan 'kallagagiyar yarinyar" yayin da Dije ke tunanin irin zaman da zasuyi dashi, lallai ne za ai zaman doya da manja, domin kwa dai tasan zataje gidan Wanda ba Santa yake ba, duk da cewa batasan meye asalin soba, tadai ji Ana fad'a, amma ita akaran kanta bata ta'ba jiba, amma taya zata zauna da Wanda yace " baya sonta" da wannan tunanin tayine, Dan ko abinci ta'ki ci, tanajin inama ba'a d'aura auren nanba, yanzu ya zatai, bata da wata mafita. Ko walimar dasu Jummai da inna suka had'a mata bata halacci wajen ba, domin yini tai da wani mugun ciwon kai da zazza'bi.


.......Bayan sallar isha'i aka fara 'ko'karin d'aukar amarya.

Dije na hango zaune gabansu kawu, Iya, inna da kuma malam Tsalha, kanta rufe da abaya wacca ta suturcevduk ilahirin jikinta, sai raskar kuka take.

Kawu ne ya soma da fad'in
" nasani 'yata rabuwa da iyaye akwai zafi, amma ki tuna cewa yanzu zakije kiyi cikakkiyar ibadane, wannan zaman da zaki agidanki mudidin kika yishi yadda Allah ya umarta da ayi, to tabbas zakiga gaske arayuwarki, kiyi 'ko'kari ki sani lada mai yawa ta hanyar yiwa *Mijinki* biyayya, na tabba ta kikai hakan zakice riba sosai, sannan ki ri'ke ibadarki domin itace duk wani jigo nake na rayuwa, ki zama mai gaskiya da ri'kon amana, wannan zaisa mutane su soki sosai. Sannan ki kasance me girmama iyayensa domin suma iyayenki ne, kinji ko"

Bata ce komi ba illa kukanta da takeyi.

Iya ce ta d'ora da fad'in
" duk abinda zance miki, kawunki ya riga da ya fad'a, amma inaso ki nutsu kiyiwa Mijinki biyayya, ki zama mai boye sirrinsa da na gidansa, kizama mai yawan tattali ga kayansa da dukiyarsa, sannan ki zama mai tsafta kama daga jiki, muhalli zuwa abinda yai saura. Ki kasance cijin 'kamshi koda yaushe, kada ki bari Mijinki yaji warinki ko sa'banin hakan, sannan ki ri'ke gaskiya"

" hakane Khadija, kada ki zauna cijin duhu duk abinda baki Iya ba ko baki saniba ki tambayi Wanda ki kaga yasani, nasani Iya gwargwado mun baku ilimin addini keda 'yar uwarki, Dan Allah ki ri'ke adduninki Dije". Malam Tsalha ki wannan maganar.

Sosai sukai mata nasiha mai shiga jiki, Dan daka ganta kasan maganganunsu sun shigeta. Inna ce ta kamata ta kaita d'aki tare 'Kara yimata wasu 'yan nasihohin, wani Abu naga ta bata tace " ta shanye tas" ba musu kwa ta shanye shi.


Awa biyu da faruwar hakan motar Imran ta zo, Dan dama yayi aqawarin shi zaizo d'aukarta, gidan baya ta shiga ita da Jummai, yayinda akai-akai inna ta bisu

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now