biyayya.....74

813 46 23
                                    

*BIYAYYA*


Writing by
*Maryam Abduul*

Wattpad@Maryamad856.

💫 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*💫

*page....74*

BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

-------------Ashraf bai shigoba sai da yai salla shima koda yashigo batta qasan, itakam ta bashi dama akan yasamu yaci dan tasan tabbas yaga tayi zai zauna yacin.

Shima deban yai ya hayewarsa sama, batare da yatsaya wani bata lokaciba.

Cikin wannan weekend din ba laifi sukanyi magana jefe-jefe, kuma ko gaisheshi tai zai amsa amma fa duk wad'annan ayyukan bai janye mata ko d'aya daga cikiba, haka zalika bai bafasa cin abincintaba.



........Yanzu sunyi jarrabawar zangon karatu na qarshe yayinda in sun koma aji biyi zasu ahiga wato ss2.

Wannan hutun da suka samu ta sami mom akan ta tambayar matashi tanason taje taga gida kuma jummai ba lafiya ita hankalinta yahaza kwanciya.

Mom kwa sanin tasan halinsa yasa tace mata" to" aikam ta tambayar mata kuma yabarta saidai wani barin na zuciyarsa na cemasa" yayi missing fa na abinci" amma ba yadda zaiyi.

Dije kam shiri take sosai sanda zata tafi roqon yaya Imran tai akan yakaita, bai musa mataba yakaita.sanda suka je koda tasanar da jummai tare suke dashi sosai ta miqe kamar ba mara lafiya ba.hakan yasa dije fahimtar wani abu saidai tunda taqi gayamata to itama zata 'boye abun aranta amma tabbas zata temakawa qawartata wajen samun cimma burinta.

Kwanata biyar ta juyo a wad'annan kwanakin sosai Ashraf kejinsa wani iri yanaji kamar yarasa wani abu nasa, mai yasama yafara cin abincin nata maiyasa yasabarwa dakansa cinsa gashi yanzu yamazar masa jidali yanajin ko wanne abinci wani iri.

Ba abinda yake ci sai biskit da lemo ko cake da lemo, har dije ta dawo.randa ta dawo kam kamar yai mai dan murna.sai dai ga mamakinsa sai yadinga ganin wayam gashi yau kwananta hud'u da dawowa.

Gashi kuma baida ikon yin magana tunda yace" kada ta rinqa girkawa dashi" yanzu yazaiyi gaahi baison cin ko wanne abinci inba nataba.

Kullum yana zuba ido da hanci amma ba sauyi sai daima uban qamshin turaruka dasuke cikamai hanci, hakan yasa ya rage zaman gidan sai ya koma zaman office sai ya yini yakai dare.

Sanda yaiwa Imran magana cayai" qanwar tasa takoma garinsu" shi kuma baison nuna masa cewa" yagane abinda suka shirya masa" amma sam baijin dad'in kwanakin gaba d'aya.

Imran kwa na lura da duk yadda yake, dan ya lura baison cin abinci daga biskit sai lemo, kuma hakan baisa ya tambayeshiba saima banza da yamasa.

A zahirin gaskiya kuwa Imran d'in ne yace" ta daina har zuwa wani lokaci" shiyasa dije ta daina girki saidai taci kayan qwala damashe ko kuma in yafita ta girka kad'an iya cikinta kan yadawo ta gyara ko ina.



.........Yanzu dije anshiga aji biyu karatu suke sosai ba kama hannun yara, yayinda gefe guda tana cigaba da zuwa wajen Hafsy ga kuma malamin leaaon d'in ta da yake zuwa shima.

Duk randa taje gida kuwa mom da Hanne basa barinta haka.za'a tulu mata kayan anfani nasha da gogawa ko mittsikawa ajiki.

Hanne kam takan qara mata da wasu sirrikan na iya zama da miji.hakan yanamata dadi kuwa sosai.

Zaman dasu kai da hanne nema take gayamata halin data ke ciki wanda shima din saida Hannen ta matsamata sabida taga tayi rama.shine take gayamata halin datake ciki, wanda kullum takeyi kuma ba fashi ga kuma makaranta ga wajen koyan girki shiyasa abubuwa suka mata yawa.

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now