Biyayyah....!

822 41 8
                                    

💎💎💎💎💎
  💎💎💎💎
     💎💎💎
        💎💎
*BIYYYAH*

   *Story...writing*
By
   *Maryam Abdul*

Wattpad:@maryamad856

*Typing.....*⌨

💫 *DA BAZARMU WRITERS ASS*💫

We are here to make you happy.... Smile and educated to realized that we are the best among all..... *DABAZAMU MUKE TUN'KAHO*💃💃

     Da bazarmu writers ass. Fatan alkhairi ga kowa da kowa.... Ku kasance cikin farin ciki da annushuwa na har abada.

      Masu comment and Vote ina matu'kar godiya gareku...Allah ya bar zumunci...ameen.

*page...55-56*

Bismillahir Rahmanir Raheem

--------Koda mom ta shiga d'akin nata kwance ta taddata cukwikwiyi da bargo, yaye bargon nata tai tare da 'd'ora hannunta saman goshinta jitai da zafi.

Dije kam jin an janye bargon data rufa yasata bud'e idanuwanta tas ta sauke su kan mom dake zaune kusa da ita.

Mom ce tace" sannu d'iyata Ashe ba lafiya taso muje kiyi wanka ki karya son zai kaike asibiti"

Dije ta kalli mom tace" mom Waya ce miki ban da lafiya?"

Mom tace" son ne ya fad'a mana yanzu nida dad d'in ku, Dan yace" jiya da dare ma sai da ya baki magani sannan ki ka Iya bacci, zazza'bi da ciwon kai ko? sannu kinji"

Dije taja ajjiyar zuciya kana tace" yawwa mom na gode da kulawarku gareni"

Mom tai murmushi tace" haba kefa 'yata ce dole na kula dake maza tashe kije ki wankan ki sauri yana jiranki kar Kuyi late"

Mi'kewa tai tashiga bayin azuciyarta na ayyana mata abubuwanba da yawa" lallai ma mutumin nan haka daman ya Iya shirga uwar 'karya?, mutumin da ya jibga mata wanke ya kuma tasata a gaba dole sai tayi shine yake ce musu wai ta kwana da zazzza'bi harda bani magani, lallai ma Allah ya sakan" ta 'karasa tana goge 'kwallarta da ta zubu mata Dan ji take kan nata uwa zai cire.da haka tayi wankan ta fito.

Nan ta tadda mom zaune inda ta barta, sauri- sauri tasa ta ta shirya Dan tasan son nacan ya hau sama.

'Kasa suka sakko nan ta gaida dad, mom kwa ta shiga had'a mata break fast d'in.

Dad ya kalleta yace" sannu d'iyata ya jikin fatan yayi sau'kin?"

Dije ta langwa'bar dakai gefe tace" da sau'ki na warkema ai"

Dad yai murmushi yace" ah a'a d'iya ta kudai je asibitin ko test ne sai ayi aga ko maleria ce , zama da ciwo ba dad'i kinji"

Kai kawai ta gyad'a mai, nan tashiga shan ruwan Lipton d'in Dan tace" batason da madara"

Koda ta 'karasa hijab mom ta mi'ka mata tace" ta sanya" ba musu kam ta karba tasa, nan sukai musu sallama.


Parking space suka nufa nan ya bud'e mota ya shiga Dije kam ganin haka yasata tsayawa ba tare da tayi yin'kurin komiba.

Kusan minti uku tana tsaye ganin tasan 'batamai lokaci yasa shi fad'in" dalla ki shigo kintsaya kin wani ja dunga sai kace mai shirin zuwa ya'ki"

Dije ta turo baki tace" to ka bud'an mana ni na Iya ne"

Tsaki yaja kana yace" tsiyar d'an 'kauye kenan komi sai anmasa" ya 'karasa yana mai bud'e mata morfin motar.

Dije tace" dad'in abinma kowa nan ne tushensa 'kauyen ba"

BIYAYYAHHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin