biyayyah....!

767 41 1
                                    

💎💎💎💎💎
💎💎💎💎
     💎💎💎
        💎💎

*BIYYYAH*

   *Story...writing*
By
   *Maryam Abdul*

       Wattpad.
#miss #gentle

*Typing.....*⌨

💫 *DA BAZARMU WRITERS ASS*💫

We are here to make you happy.... Smile and educated to realized that we are the best among all..... *DABAZAMU MUKE TUN'KAHO*💃💃

Da bazarmu writers ass. Fatan alkhairi ga kowa da kowa.... Ku kasance cikin farin ciki da annushuwa na har abada.
 

   Ina matu'kar godiya ga addu'arku gareni my *Fans*....Allah ya bar zumunci....ya barmu a tare...ameen.

*page.... 49-50*

Bismillahir rahmanir raheem.

--------Falon d'akin ta fara gyarawa daga nan ta wuce band'aki sai da ta gama duk abinda zatai tsaf sannan ta shige bayi ta watsa ruwa.kan gadon ta ta zauna tare da fad'in" wash, wannan aiki ko masifa?"

Tana nan zaune taji turowar 'kofar dakin nata, d'aga kai tai ta kalli 'kofar dan a tunanin ta auta ce, sai dai sa'banin hakan da ta gani.

Yana sanye cikin kayan shan iska kayan sun yimishi kyau sosai..." Ki fito falo" ya fad'a yana me juyawa.

Cunu baki tai tace" kai wannan jaraba ba za'abar mutum ya huta ba, daga wannan sai wannan"


Kamar yadda yace mata" ta sameshi a falo" hakan kwa akai yana zaune yana shan coffee d'in da ya amso awajen mom kallon ta yai yace" yawwa inaso ki bud'e kunnuwanki da kyau kijini, Imran zaizo Dan haka be careful, idan kuma kika kuskura kikai abinda ban lamunta da shiba to kiyi kuka tun kan na kamaki, kin san Allah......"

Bai 'karasaba ta katseshi da fad'in" nikam na sanshi....tunda dai ina bauta mai" ta fad'a tana murgud'a baki.

Sakin baki yai yana kallon ta kafin ya matso kusa da ita yace" oh kinyi girman da kafin a gama magana kin 'karasa da taki ko?", to wllh ki kiyayeni "

Turo baki tai tace" nifa duk abinda kacema ban fahimci ko d'aya ba sabida hankalina sam bai wajen"

Da mamaki ya kalleta ta kafin yace" kina nufin na sakya mai-maitawa kenan?"

Gyad'a mai kai tai tace" ehh man sabida ba abinda na gane aciki"

Matsowa ya kuma yi daf da ita tare da Jan kunnanta d'aya kafin yace" bazan mai-maita ba, abinda kikaji nace kiyi aiki dashi Wanda bakijiba hukunci yasa ki fahimta...sannan idan har wannan tasisin bakin naki bazai sami ladaf d'in shiru ba to zan sai tashi nan bada dad'ewa ba, Dan haka in kinaso tsira da shi to kisa ya nutsu"

Turo bakin ta 'karayi kafin tace" amma ai kowa da irin bakin da aka tsagamai ko?, kuma ai ba a hana mutum da magana...Allah ya gani ni daman can haka nake ko Iya ta shaida ce ma"

Bakin ya falla da d'an yatsunsa biyu kafin yace" yanzu ai ya fara mutuwa ko, wannan ma kad'an kika gani"

Cikin sauri ta Sosa wajen tare da fad'in " alqur"'an da saura sai randa na bar duniya wannan kyakkyawan bakin zai mutu"

Tana ''karasawa ta mi'ke a 360 tai d'akin ta, fad'i take" wai Allah ya soni nasha ai yau dana shiga uku...car ubancan wai namiji da suna hajara"



Shikam da kallon mamaki ya bita dashi lallai wannan yarinyar wato taga makwancinsa kenan....lallai ba shakka  sai ya gyara mata zama"

Ya 'kara Jan tsaki tare da yin murmushi kafin yace" sai rashin kunya ga kuma shegen tsoro, zamu gaurayane"


BIYAYYAHWhere stories live. Discover now