Appology/Biyayya....12-14

679 26 5
                                    

💎💎💎💎💎
   💎💎💎💎
      💎💎💎
          💎💎

BIYAYAH

By 
  *Maryam Abdul*

💫 *DA AZARMU WRITTERS ASS*💫

We are hera to make you happy, smile..educated and realized that we are the best among all DA *BAZARMU MUKE TUN'KAHO....*💃💃💃

*page....12-14*

BISIMILLAHIR RAHMANIRRAHIM.

-------Dije ta kalle shi tace " kamar ya nice zan iya dashi, ban ganeba."

Imran ya gyara zamansa yace " kinga ne, yanzu bamu da lokacin yin magana, kinga yanzuma yana waje yana jirana. amma kimin alqawari cewa zaki yarda ki aure d'an uwana ASHRAF, kinji 'kanwas"

"shikkenan, naji nayima, kuma ni daman ai mungama magana da kawuna"

Cikin murna yace "nagode 'kanwas, kin biyani komi. ni zan wuce 'kanwas, amma zan dawo kinji "

Turo baki tai tace " kai muna hirar mu mai dad'i, karka tafi kaji"

"ai nace zan dawo, muje nai sallama da Iya"

Nan suka fice daga d'akin, Iya na zaune ita da Jamila suna hirar su,dan tunda taga Dije an bud'e baki ana hira ta fita ta barsu.nan ya musu sallama. Shima saida ya ajjiyewa Iya goma ta arzi'ki sanan ya fice, yayin da Dije da Jamila suka mara masa baya dan rakiya.

Yana jingine jikin motar sai faman duba agogo yake yana jan tsaki.shi ba abin yace zai koma ya fito dashiba, wani wawan tsaki yaja, ganinsu dayai tare suna ta hira har da dariya.har suka 'karaso wajen motar be motsa daga tsayan da yakeba.

Imran ne ya kalleshi yace " yadai, muje ko, na fito"

Tsaki yaja tare da fad'in " meye ala'kata da fitowarka"

Cikin sauri Dije ta tari nunfashi Imran tare da fad'in " ya Imran kai maza ka d'akko tsintsiyoyi naga tsaka da yawa a kusa, ko kai baka kashe tsaka ne, kasan Ance in aka kashe akwai lada mai yawa, alqur'aran kar ka bari...."

"Ke wawiya, ki tsaya a inda matsayinki yake, in bahaka ba sai nayi 'kasa-'kasa dake, maza 'bacemin daga gani"

Dije kwa ko motsi batai ba, sai ma gyara tsayuwa datai tace " alqur'an baba da inna basu haifi wawuya ba, sai dai in agidanku, kuma ba inda zani, yo in banda shisshige dakai nake zancena, kaga ni bana san sa ido a cikin al'murana, nan kuma ai 'kofar gidan mune, in ana da zuciya kare be ciba kaima ka tafi naku 'kofar gidan aha" ta'karasa cike da tsiwa.

Ba Ashraf ba hatta Imran saida ya tsaya yana kallonta, lallai duk yadda yake tunaninta ta wuce nan.chab lallai akwai chakwakiya a zaman su, domin yasan dai shi Ashraf bai d'aukan raini, to ita kuma DIJE bata barin ta kwana.

Ashraf ne ya kalleta fuska ba annuri yace " duk yacce akai wannn rashin kunyar gada kikai, sa'banin ni da nasan darajar na gaba dani, kuma in baki bar wajennan ba wllh sai na tattakaki, stupid kawai"

Murgud'a baki tai tace " kamar yadda nagaji rashin kunya haka kaima ka gaji rashin sanin darajar d'an Adam, kuma ba inda zani mai siffar aljanu.."

Cike da zafin nama yayo kanta, da nufin ya 'ba'b'ballata, amma ina Dije ta tsere mai, daman ita bananba wajen gudu.'kwafa yai kawai ya zagaya 'bangaren driver sit ya 'bud'e ya shiga, ko kallon Imran beba bare yace mishi ya shigo.shikam ganin yana 'ko'karintada mota yasa ya fad'a 'bangaren me zaman banza.cikin zafin rai ya fizgi motar.

Ita kam Dije na shiga gida ta tsaya a soro tana sauke nunfashi "wai, chab, daya kamani ai da nashiga uku, hmm mutum kamar 'bak'in kumurci."

Koda Jummai tashigo ko kallon inda take batai ba tai hanyar shiga cikin gidan, cikin zafin nama Dije tasha gabanta tare da fad'in " tsaya kije, alqur'an kika gayawa Iya wllh bazan baki kud'in da ya Imran ya bada b"

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: May 07, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now