BIYAYYAH

4.2K 114 3
                                    


  
   *BIYAYYAH*

      
By

    *Maryam Abdul*
   

💫  *DA BAZARMU WRITTERS ASS*💫

  
  We are here to make you happy....smile, educated and to realized that you are the best among all.... *DA BAZARMU MUKE TUNK'AHO*💃💃

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

INA RO'KON ALLAH DAYA BANI IKON ISAR DA SA'KON DANA KESON ISARWA...ALLAH YASA NAFARA A SA'A...YA KUMA BANI IKON KAMMALAWA KAMAR YADDA NAFARA...AMEEN.

*page....1-8*

   

   
...............Gudu yake sosai kamar zai tashi sama, can k'asan zuciyarsa kuma wani irin tuk'uk'in bak'in ciki ne ke tashi "Me ya sa? Dan me Daddynsa zai yi masa haka? Ta yaya ma zai had'ashi da kucakar yarinya wacca sam ba ta da aji?" Wad'annan tambayoyin ya dinga yi wa kansa. Wayar shi ce ta hau ruri, sai da ya yi kusan sakan biyar sannan ya duba kan gilashin wayar dan ganin waye ke kiransa a cikin wannan mood d'in da yake ciki? Wani wawan tsaki yaja ganin sunan IMRAN ya bayyana akai ɓaro-ɓaro. (Abokin shi ne kuma tare  suka taso, duk abin da ke damun d'aya to zai gayawa d'ayan dan su haɗu su samar wa da kansu mafita). Ya yi kusan sakan shida sanann ya ɗaga tare da karawa a kan fatar kunnensa. Ko da ya d'aga d'in bawai ya yi magana ba ne a'a ya yi masa shiru ne, ganin shirun ya yi yawa kuma ga kud'i na tafiya a aikin banza ya sanya wanda ya yi kiran yin magana, dan yasan ko kwana za su yi a haka in bai ga damar yin magana ba ba zai yi ba.
  
  "Ya yi kyau abin da kake yi ASHRAF, kai kana ganin hakan shi ne daidai?" Imran ya fad'a cikin zafin rai.

Iska ya furzar mai huce kafin ya ce, "So meye ruwanka a ciki? Ni dai na riga da na rantse, wallhi duk wacce ta yi gigin aurena sai ta gane kurenta, me ya sa baku gane wa ne?"

Imran ya girgiza kai tamar yana gabansa kafin ya ce, "Wai kai me ya sa kake da taurin kaine Ashraf? Haba ya kamata ka yi biyayya ga Daddy ko bakomai mahaifin kane ai"

"Tun yaushe a ke yin biyayyar, me ya sa ni ma baza a bar ni na zab'i zab'ina ba? Haba zamani fa ya canja IMRAN" ya fad'a ransa a matuƙar ƙolukowar b'aci.

Imran da shi ma ransa ya soma b'ace sosai ya ce, "Wai kai wani irin mutumne ASHRAF? Me ya sa kake san canja wasu halaye naka? Na tabbata yanzun a ka ce ka fito da wacce kakeso d'in cewa za ka yi babu, to yaya kakeso a yi maka?"

"A bar ni har zuwa lokacin da za'a haifa mini matar da zan aura, ni fa na gayama har yanzu ba a haife ta ba, balle ma kusa ran aurar da ni, so plz kabar ni na huta"
     Yana gama fad'in haka ya datse kiran, domin a yanzu kansa wani irin sarawa yake yi masa, shin ta yaya zai b'ullo wa wannan al'amari, sam Daddy yak'i ya fahimce shi. Da wannan tunanin ya k'arasa wani katafaren gida, wanda ni kaina sai da na tsorata da ganin shi, daman akwai irin gidajen nan anan garin KANO, cab wai, ai bazan iya fasalta muku gidan ba domin sai yajuyarmin da hankali, amma gaskiya ya had'u yaji naira sosai.

Horn biyu ya yi mai gadi ya wangale mai tangameman gate d'in, cab ai anan na dad'a tsurewa, lallai wannan gida ya gaji da had'uwa, wajen parking space yayi nan naga motoci kala-kala, wasuma ban tab'a ganin irinsuba anan kasarba, yana gamawa naga yanufe wata k'ofa wacce zata sada shi da ainihin gidan, hoo hoo kunsan me nagani readers hmm lifter ce wacce se ka hau zata kaika ainihin gidan, kai alqur'an gidannan ba a KANO yakeba, cab lallai.

Cikin isa da tak'ama ya shiga falon, wata kyakkyawar mata nagani zaune a falon tana cin kayan marmari, a k'alla zata kai shekara 45, sedai zaka iya rantsewa shekarunta basufi 32, domin tanacin me kyau da kuma samun waje me kyau, cikin farin ciki da walwala tace "ah my son har ka dawo?"

Zunb'oro baki ya yi yace "wllh mom duk kun gajiyar dani, nifa aikin nan yana wahalar dani, kawai a bari na k'ara samun k'arfin k'ashi"

Dariya ta yi tace "lallai my son yanzu har a wannan k'warin k'ashin kake buk'atar dad'in wani k'warin" ta k'arasa tana me kama dan tsansa.

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now