biyayyah.....!

799 41 3
                                    

💎💎💎💎💎
  💎💎💎💎
     💎💎💎
        💎💎
*BIYYYAH*

   *Story...writing*
By
   *Maryam Abdul*
Wattpad:@maryamad856

*Typing.....*⌨

💫 *DA BAZARMU WRITERS ASS*💫

We are here to make you happy.... Smile and educated to realized that we are the best among all..... *DABAZAMU MUKE TUN'KAHO*💃💃

   Wannan shafin naki ne *abar alfahrina (Mahaifiyarta)*

      Masu comment, Vote and Like ina matu'kar godiya gareku...Allah ya bar zumunci...ameen.

*page...57-58*

Bismillahir Rahmanir Raheem

---------Kallon ta yai yadda ta wani babbake akan kujerar, tsaki yaja tare da fad'in" ai saiki yimasa bayani ko?"

Ta kalleshi tare da fad'in"name fa?"

Harararta yai kana yace" bansani ba dalla ni kiyi ki fadi abinda ke damunki dan ina da abubuwan yi agabana"

Dije ta turo baki can ciki-ciki tace" ni kuma babu ko?"

Kallon Dr.Salim tai tace"daman zazza'bi ke damuna sai ciwon kai tun jiya"

Dr.Salim yai murmushi kafin yace" bayan wannan bakomi? "

Kai ta gyad'a mai alamar babu.

Dr.Salim ya 'kwalawa wata nurse kira da take aikin yamma yace" suje a d'au fitsarinta agani"

Cikin sauri Ashraf ya taresa da fad'in" mai kuma za'ai da wani fitsarinta? kaga malam nifa sauri nakeyi"

Dr.Salim yai murmushi kana yace" atunaninka mai ake dashi, zan gwadane naga ko Allah zaisa muna da rabo ne"

Tsaki yaja kafin yace" to babu, malam ba komi ka rubuta mata magunguna kawai Tasha"

Dr.Salim yai murmushi yace" calm down my man, dole in mata gwaji inga ko tana da maleria" ya juya ya kalli nurse d'in yace" aje a mata gwaji maleria da typhod" ya gamawa fad'ar haka suka fice ita da Dije.

Ashraf ya ja tsaki yace" banza kawai da kasan ga abinda ya kamata kayi kake 'batawa mutane lokaci?"

Dr.Salim yace" bansani ba wllh Ashraf ka janza hali, tun wuri kuma yarinyar da kake rainawa wllh kar kai mamakin irin halin daza ta jefaka nan gaba nidai na gayama"

Ko kallonshi bai sakya yiba ya zaro wayarshi ya shiga latse-latsen sa.tsawon mintuna biyar kafin Dije ta dawo, nan akaga ba wani maleria ko typhod kawai dai zazza'bi ne, nan yabata wasu 'yan shawar-wari kana ya rubuta mata magunguna.

Ganin sun kammala komine yasa Ashraf mi'kewa hannu ya mi'ka mai yace" sai munyi Waya" daga haka ya fice.

Ganin hakan yasa itama Dije bin bayansa.Dr.Salim ne ya takye musu baya sai da ya rakasu har parking space cike da zolaya yace da Dije" to amaryar mu sai munzo kwasar girki ko?"

D'aga mishi kai kawai tai tare davsakin wani 'kayataccen murmushi a zuciyarta kam catai" kadai ci jagwal-gwalo"

Nan ta fad'a motar shikam Ashraf ya figeta a guje sai gida.



.......Imran zaune gaban mami d'insa kallon ta yai yace" wllh mami *(sunan ta ya koma haka daga mom zuwa mami Dan da mom nasu Ashraf)* narasa gane kan Ashraf kwata-kwata"

Mami ta kalleshi tace" to me yafaru kuma son? "

Imran ya gyara zamansa yace" sabida Allah mami dan anma auren had'i sai ka'ki kulawa da matarka?"

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now