BIYAYYAH......

1.1K 46 0
                                    

           *BIYAYYAH*


   Story ....Writing by

  *Maryam abdul'aziz*
       (Maryam Abdoul)

Wattpad @Maryamad856




*page....25-26*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*


---------Cikin zafin rai kawu yace " kinji ai irin abinda nake gudu ko Iya, sabida tsabar shashanci da iskanci irin na yarinyar nan mutake gayawa haka, na tabbata da babanta yana da rai ko shi kika shinfid'awa kara bai isa ya tsallakeba, amma gashi  tana Neman ta bamu kunya. Kisani wannan kunyar dazaki bamu, bamu kad'ai bane aciki harda *mahaifinki* da baya da rai, ko kinaso ace ahlinku basu da cika alqawari, kisani mahaifinki da yana Raye sai yafi kowa murna da farin ciki domin harda da hannunsa acikin lamrin nan"

Iya ta kalleta tace " haba 'Yar albarka kada ki bamu kunya mana kinji"

Dije ta kalleta cike da sanyin jiki, duk abinda za asa da babanta to tabbas tana ganin girmansa kuma zatai hakanne Dan *MAHAIFINTA* amma ba Dan komi ba, kuma zata kare Martabar gidansu  da ahlinta. Kallonsu tai tace " kawu, Iya kuyi ha'kuri da abinda na muku a yanzu, nayarda na amince zan aure za'bin da kukayimin. nayarda zanyi *BIYAYYAH* agareku."
Cikin farin ciki Kawu yace " mun gode d'iyar albarka, Allah yayi miki albarka, yanzu ga kud'inki nan na Nagani inaso"

Ta kalle kud'in ta dube kawun Nata tace " kawu ni ba abinda zanyi dash, duk wani Abu da za'aban to mallakin June, kiyi duk abinda yake dai-dai agareni"

"Allah ya miki albarka, tashi kike" Kawu ya fad'a. Nan suka cigaba da tattaunawa kan lamuran. daga bisani yaiwa Iya sallama tare da ajjiyemata kud'in.

Dije kam koda tashiga d'akinta zama tai akan katifarta tare da shimfid'a kyakkyawan tagumi akan kumatunta.tunani kawai take yadda zata tafi tabar 'kauyensu, tabar Iyanta ita kad'ai, wannan shine gatan da ake mata a rabata da kowa Nata, akaita ahlin da bata san suba.

Iyace tashigo d'akin amma Sam Dije bata ki shigowarta ba domin ta fad'a duniyar tunani.  dafata tai tace "ya akayi d'iyar arzi'ki"

Firgigit ta farka tare da kallon Iyan tace " Iya banason na tafi na barki, banason na tafi nabar 'kauyenmu"

   Iya ta tallafota kan kafad'arta tace " kiyi ha'kuri kinji haka rayuwar aure take, kuma nasan duk indai zaki zakiji fad'in zama dash sosai, suna matu'kar sanki jikalleta".

Gyad'a mata kai kawai tai, tare da zamewa ta kwanta kan cinyarta.




---------- Imran ne zaune yana game a wayarsa, sallamar da Ashraf yaine yasa shi kallonsa tare da amsa masa sallamar.waje yasamu yazauna batare da ya cemasa kanzil ba, shima ganin hakan yasa yai banza dashi, Dan yasan ko maganar duniya zai mai indai bai ga Damar mai da martaniba to bazai kulashiba.tsawon minti goma suna zaune a haka cike da mazewa Ashraf yace " kai baka San mutane sun shigo bane, Dan iskanci kana wata shegiyar game"

Kallonshi Imran yai yace " naga ikon Allah yau, nakeji bakai kazo ka tadda niba a zaune, kuma har gidanmu?"

Ashraf yai 'kwafa yace " lallai yaron nan ka raina ni da yawa, to yimin gori Nidai bamu da gidan, sannan ko banza ai na girmeka, taya wa zai fara yiwa 'kani magana salon ya rainashi" ya 'karashe yana wani kun'bure-kun'bure.

Imran yai dariya yace " ah lallai naga Alama, aikam saidai ai tazama a haka, gidan kan waya sani ko babu, ni shiyasa ma wllh na matsu dad ya aurar dakai ko kadaina biye-biyen gidajen mutane" ya 'karashe cike da dariyar tsokana.

Ashraf ya kalleshi tare da cillamai wata uwar harara yace " mai zai hana kai ka wassheshi.Mits" ya 'karashe da tsaki.

Har Imran ya bud'e baki zai magana ya katse shi da fad'in " kaga malam d'an le'ka ka kar'bo mana abinci yinwa na keji, kuma ban San komawa gida yanzu"

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now